< Irmiya 42 >

1 Sa’an nan dukan shugabannin sojoji, haɗe da Yohanan ɗan Kareya da Yezaniya ɗan Hoshahiya, da dukan mutane daga ƙarami zuwa babba, suka zo wurin
ויגשו כל שרי החילים ויוחנן בן קרח ויזניה בן הושעיה--וכל העם מקטן ועד גדול
2 Irmiya annabi suka ce masa, “Muna roƙonka ka ji kukanmu ka kuma yi addu’a ga Ubangiji Allahnka saboda dukan wannan raguwar mutane. Gama kamar yadda kake gani yanzu, ko da yake dā muna da yawa, yanzu ɗan kaɗan muka rage.
ויאמרו אל ירמיהו הנביא תפל נא תחנתנו לפניך והתפלל בעדנו אל יהוה אלהיך בעד כל השארית הזאת כי נשארנו מעט מהרבה כאשר עיניך ראות אתנו
3 Ka yi addu’a cewa Ubangiji Allahnka zai faɗa mana inda za mu tafi da kuma abin da za mu yi.”
ויגד לנו יהוה אלהיך את הדרך אשר נלך בה ואת הדבר אשר נעשה
4 Sai Irmiya ya amsa ya ce, “Na ji ku, tabbatacce zan yi addu’a ga Ubangiji Allahnku yadda kuka roƙa; zan faɗa muku duk abin da Ubangiji ya faɗa ba kuwa zan ɓoye muku kome ba.”
ויאמר אליהם ירמיהו הנביא שמעתי--הנני מתפלל אל יהוה אלהיכם כדבריכם והיה כל הדבר אשר יענה יהוה אתכם אגיד לכם--לא אמנע מכם דבר
5 Sa’an nan suka ce wa Irmiya, “Ubangiji ya zama shaida na gaskiya da kuma aminci a kanmu in ba mu yi bisa da duk abin da Ubangiji Allahnka ya aike ka ka faɗa mana ba.
והמה אמרו אל ירמיהו יהי יהוה בנו לעד אמת ונאמן אם לא ככל הדבר אשר ישלחך יהוה אלהיך אלינו--כן נעשה
6 Ko ya gamshe mu ko bai gamshe mu ba, za mu yi biyayya da Ubangiji Allahnmu, ga wanda muke aikan ka, saboda ya zama mana da amfani, gama za mu yi biyayya da Ubangiji Allahnmu.”
אם טוב ואם רע--בקול יהוה אלהינו אשר אנו (אנחנו) שלחים אתך אליו נשמע למען אשר ייטב לנו כי נשמע בקול יהוה אלהינו
7 Bayan kwana goma sai maganar Ubangiji ta zo wa Irmiya.
ויהי מקץ עשרת ימים ויהי דבר יהוה אל ירמיהו
8 Saboda haka ya kira Yohanan ɗan Kareya da dukan shugabannin sojoji waɗanda suke tare da shi da dukan jama’a daga ƙarami zuwa babba.
ויקרא אל יוחנן בן קרח ואל כל שרי החילים אשר אתו ולכל העם--למקטן ועד גדול
9 Ya ce musu, “Ga abin da Ubangiji, Allah na Isra’ila, wanda kuka aike ni gare shi don in gabatar da kukanku, yana cewa,
ויאמר אליהם כה אמר יהוה אלהי ישראל אשר שלחתם אתי אליו להפיל תחנתכם לפניו
10 ‘In kuka zauna a wannan ƙasa, zan gina ku ba zan kuwa rushe ku ba; zan dasa ku ba kuwa zan tumɓuke ku ba, gama ina baƙin ciki a kan masifar da na aukar a kanku.
אם שוב תשבו בארץ הזאת--ובניתי אתכם ולא אהרס ונטעתי אתכם ולא אתוש כי נחמתי אל הרעה אשר עשיתי לכם
11 Kada ku ji tsoron sarkin Babilon, wanda kuke tsoro a yanzu. Kada ku ji tsoronsa, in ji Ubangiji, gama ina tare da ku zan kuma cece ku daga hannuwansa.
אל תיראו מפני מלך בבל אשר אתם יראים מפניו אל תיראו ממנו נאם יהוה--כי אתכם אני להושיע אתכם ולהציל אתכם מידו
12 Zan nuna muku jinƙai don yă nuna muku jinƙai ya kuma maido da ku ƙasarku.’
ואתן לכם רחמים ורחם אתכם והשיב אתכם אל אדמתכם
13 “Amma fa, in kuka ce, ‘Ba za mu zauna a wannan ƙasa ba,’ ta haka kuka kuma nuna rashin biyayya ga Ubangiji Allahnku,
ואם אמרים אתם לא נשב בארץ הזאת לבלתי שמע בקול יהוה אלהיכם
14 in kuma kuka ce, ‘A’a, za mu tafi mu zauna a Masar, inda ba za mu ga yaƙi ko mu ji ƙarar ƙaho ko mu ji yunwa ba,’
לאמר לא כי ארץ מצרים נבוא אשר לא נראה מלחמה וקול שופר לא נשמע וללחם לא נרעב ושם נשב
15 to, ku ji maganar Ubangiji, ya raguwar Yahuda. Ga abin da Ubangiji Maɗaukaki, Allah na Isra’ila, yana cewa, ‘In kun ƙudura ku tafi Masar kuka kuma tafi kun zauna a can,
ועתה--לכן שמעו דבר יהוה שארית יהודה כה אמר יהוה צבאות אלהי ישראל אם אתם שום תשמון פניכם לבא מצרים ובאתם לגור שם
16 takobin da kuke tsoro zai same ku a can, kuma yunwar da kuke tsoro za tă bi ku zuwa Masar, a can kuwa za ku mutu.
והיתה החרב אשר אתם יראים ממנה שם תשיג אתכם בארץ מצרים והרעב אשר אתם דאגים ממנו שם ידבק אחריכם מצרים--ושם תמתו
17 Tabbatacce, duk waɗanda suka ƙudura suka tafi Masar su zauna a can za su mutu ta wurin takobi, yunwa da annoba; ba ko ɗayansu zai tsira ko ya kuɓuta wa masifar da zan aukar a kansu.’
ויהיו כל האנשים אשר שמו את פניהם לבוא מצרים לגור שם--ימותו בחרב ברעב ובדבר ולא יהיה להם שריד ופליט מפני הרעה אשר אני מביא עליהם
18 Ga abin da Ubangiji Maɗaukaki, Allah na Isra’ila, yana cewa, ‘Kamar yadda na kwararo fushina da hasalata a kan mazaunan Urushalima, haka kuma zan kwararo fushina a kanku sa’ad da kuka tafi Masar. Za ku zama abin la’ana da abin tsoro, abin ƙyama da abin ba’a; ba za ku ƙara ganin wannan wuri ba.’
כי כה אמר יהוה צבאות אלהי ישראל כאשר נתך אפי וחמתי על ישבי ירושלם כן תתך חמתי עליכם בבאכם מצרים והייתם לאלה ולשמה ולקללה ולחרפה ולא תראו עוד את המקום הזה
19 “Ya ku raguwar Yahuda, Ubangiji ya ce muku, ‘Kada ku je Masar.’ Ku tabbatar da wannan. Na gargaɗe ku yau
דבר יהוה עליכם שארית יהודה אל תבאו מצרים ידע תדעו כי העידתי בכם היום
20 cewa in kun yi kuskure sa’ad da kuka aike ni wurin Ubangiji Allahnku kuka kuma ce, ‘Yi mana addu’a ga Ubangiji Allahnmu; ka faɗa mana duk abin da ya faɗa za mu kuwa aikata.’
כי התעתים (התעיתם) בנפשותיכם--כי אתם שלחתם אתי אל יהוה אלהיכם לאמר התפלל בעדנו אל יהוה אלהינו וככל אשר יאמר יהוה אלהינו כן הגד לנו--ועשינו
21 Na faɗa muku yau, amma har yanzu ba ku yi biyayya ga Ubangiji Allahnku cikin dukan abin da ya aiko ni in faɗa muku ba.
ואגד לכם היום ולא שמעתם בקול יהוה אלהיכם ולכל אשר שלחני אליכם
22 Saboda haka yanzu, ku tabbatar da wannan. Za ku mutu ta wurin takobi, yunwa da annoba a wurin da kuke so ku tafi ku zauna.”
ועתה ידע תדעו כי בחרב ברעב ובדבר תמותו--במקום אשר חפצתם לבוא לגור שם

< Irmiya 42 >