< Irmiya 4 >

1 “In za ka komo, ya Isra’ila, ka komo gare ni,” in ji Ubangiji. “In ka kau da gumakanka masu banƙyama daga gabana ba ka ƙara karkace ba,
Si tu reviens à moi, Israël, dit l'Éternel, tu reviendras ici; et si tu ôtes tes abominations de devant moi, tu ne seras plus errant;
2 kuma in cikin gaskiya da adalci ka rantse, ‘Muddin Ubangiji yana raye,’ to al’ummai za su sami albarka ta wurinsa kuma a cikinsa za su ɗaukaka.”
et si tu jures par « la vie de l'Éternel, » selon la vérité, la droiture et la justice, les nations se serviront de son nom pour bénir, et se glorifieront de lui.
3 Ga abin da Ubangiji yana ce wa mutanen Yahuda da kuma na Urushalima. “Ku nome ƙasarku kuma kada ku yi shuka cikin ƙayayyuwa.
Car ainsi parle l'Éternel aux hommes de Juda et de Jérusalem:
4 Ku yi wa kanku kaciya ga Ubangiji ku yi wa zukatanku kaciya, ku mutanen Yahuda da mutanen Urushalima, in ba haka ba hasalata za tă sauko ta ci kamar wuta saboda muguntar da kuka aikata za tă ci ba wanda zai kashe ta.
Faites-vous des novales et ne semez point parmi les épines! Circoncisez-vous pour l'Éternel, et enlevez le prépuce de vos cœurs, hommes de Juda, et habitants de Jérusalem, de peur que ma colère n'éclate comme un feu, et ne consume sans que personne éteigne, à cause de la méchanceté de vos actions.
5 “Ku yi shela a Yahuda ku kuma furta a Urushalima ku ce, ‘Ku busa ƙaho a ko’ina a ƙasar!’ Ku tā da murya da ƙarfi ku ce, ‘Ku tattaru! Bari mu gudu zuwa birane masu katanga!’
Annoncez en Juda, et publiez à Jérusalem, et parlez, et sonnez de la trompette dans le pays, criez à pleine voix et dites: Rassemblez-vous, et allons dans les villes fortes!
6 Ku tā da tuta don zuwa Sihiyona! Ku gudu ku nemi mafaka ba tare da jinkiri ba! Gama ina kawowa masifa daga arewa, mummunan hallaka kuwa.”
Tournez l'étendard vers Sion, fuyez, ne vous arrêtez pas! Car du nord J'amène la calamité et un grand désastre.
7 Zaki ya fito daga ruƙuƙinsa; mai hallakarwar al’ummai ya kama hanya. Ya bar wurinsa don yă lalace ƙasarku. Garuruwanku za su zama kufai babu mazauna.
Le lion sort de son fourré, et le destructeur des peuples part, il sort de son lieu, pour faire de ton pays un désert; tes villes seront détruites, dépeuplées.
8 Saboda haka ku yafa tufafin makoki, ku yi makoki da kuka, gama fushin Ubangiji bai juye daga gare mu ba.
Aussi, ceignez le cilice, gémissez, et lamentez-vous, car l'ardente colère de l'Éternel ne s'éloigne pas de vous.
9 “A wannan rana,” in ji Ubangiji, “sarki da shugabanni za su fid da zuciya, firistoci za su razana, annabawa kuma za su yi mamaki.”
Et dans ce jour-là, dit l'Éternel, le cœur manquera au roi et aux princes, et les sacrificateurs seront atterrés, et les prophètes seront stupéfaits.
10 Sai na ce, “Kash, Ubangiji Mai Iko Duka, yaya ka ruɗi mutanen nan da kuma Urushalima gaba ɗaya haka ta wurin cewa, ‘Za ku zauna lafiya,’ sa’ad da takobi yana a maƙogwaronmu.”
Alors je dis: Ah! Seigneur, Éternel, en vérité tu as trompé ce peuple et Jérusalem en disant: Vous serez sains et saufs! et cependant l'épée pénètre jusqu'à son cœur.
11 A lokacin za a faɗa wa mutanen nan da kuma Urushalima cewa, “Iska mai zafi daga tuddan hamada za tă hura zuwa wajen mutanena, amma ba don ta sheƙe ko ta rairaye; ba;
Dans ce temps-là, il sera dit à ce peuple et à Jérusalem: Un vent brûlant vient des collines du désert dans la direction de la fille de mon peuple, non point pour nettoyer, ni pour émonder,
12 iska mafificin ƙarfi da ta fito daga gare ni. Yanzu na zartar da hukuncina a kansu.”
un vent plus fort que pour cela viendra de par moi; et alors à mon tour je prononcerai ma sentence contre eux.
13 Duba! Yana zuwa kamar gizagizai, kekunan yaƙinsa suna zuwa kamar guguwa, dawakansa sun fi gaggafa sauri. Kaiton mu! Mun shiga uku!
Voici, Il s'avance comme les nuées, et ses chars sont comme l'ouragan, et ses chevaux plus légers que les aigles. « Malheur à nous, car nous sommes dévastés! »
14 Ya Urushalima, ki wanke mugunta daga zuciyarki ki sami ceto. Har yaushe za ki zauna riƙe da mugayen tunani?
Purge de méchanceté ton cœur, Jérusalem, afin que tu sois sauvée! Jusques à quand séjourneront dans ton cœur tes pensées désastreuses?
15 Murya ta shela daga Dan, tana furtawa masifa daga tuddan Efraim.
Car une voix publie depuis Dan, et annonce un désastre depuis la montagne d'Éphraïm.
16 “A faɗa wa al’ummai wannan, a furta wannan game Urushalima. ‘Sojoji masu ƙawanya suna zuwa daga ƙasa mai nisa, suna tā da kirarin yaƙi a kan biranen Yahuda.
Annoncez-le aux nations! Voici, publiez-le dans Jérusalem: des assiégeants arrivent d'une terre lointaine, et ils poussent leur voix contre les villes de Juda.
17 Sun kewaye ta kamar masu gadin fili, domin ta yi mini tawaye,’” in ji Ubangiji.
Comme les gardes d'un champ ils te cerneront; car elle s'est révoltée contre moi, dit l'Éternel.
18 “Halinki da ayyukanki sun kawo wannan a kanki. Hukuncinki ke nan. Yana da ɗaci! Ya soke ki har zuciyarki!”
Ta conduite et tes œuvres ont attiré ces choses sur toi; c'est l'effet de ta méchanceté; oui, cela est amer, oui, cela pénètre jusqu'à ton cœur.
19 Azabana, azabana! Ina birgima cikin zafi. Azabana, azabar zuciyata! Zuciyata yana bugu a cikina, Ba zan yi shiru ba. Gama na ji karan ƙaho; na ji kirarin yaƙi.
« Mes entrailles! mes entrailles! je souffre dans les cellules de mon cœur; mon cœur bouillonne, je ne puis me taire; car tu entends, mon âme, le son de la trompette, le cri de guerre.
20 Masifa kan masifa; dukan ƙasar ta zama kufai. Cikin ɗan lokaci aka rurrushe tentuna nawa, mafakata ba zato.
Ruine sur ruine est annoncée, car tout le pays est désolé; tout à coup mes tentes sont détruites, en un instant mes pavillons.
21 Har yaushe zan dubi tutar yaƙi in kuma ji karar ƙaho?
Jusques à quand verrai-je l'étendard, ouïrai-je le son de la trompette? »
22 “Mutanena wawaye ne; ba su san ni ba. Su’ya’ya ne marasa azanci; ba su da fahimi. Suna da dabarar aikata mugunta; ba su san yadda za su aikata alheri ba.”
– « C'est que Mon peuple est en délire, il ne Me connaît pas; ce sont des fils insensés, destitués d'intelligence; ce sont des sages pour faire le mal; mais pour faire le bien, ce sont des ignorants. »
23 Na dubi duniya, na ga cewa marar siffa ce babu kome; sammai kuma, haskensu ya tafi.
Je regarde la terre, et voici, elle est déserte et vide; et les Cieux, ils n'ont plus leur lumière.
24 Na dubi duwatsu, sai na ga suna makyarkyata; dukan tuddai kuwa suna lilo.
Je regarde les montagnes, et voici, elles tremblent, et toutes les collines s'ébranlent.
25 Na duba, sai na ga ba kowa; kowane tsuntsu a sarari da ya tsere.
Je regarde, et voici, il n'y a point d'homme, et tous les oiseaux des Cieux ont fui.
26 Na duba, sai na ga ƙasa mai amfani ta zama hamada; dukan garuruwanta sun zama kufai a gaban Ubangiji, a gaban zafin fushinsa.
Je regarde, et voici, le Carmel est un désert, et toutes ses villes sont détruites par l'Éternel et par le feu de sa colère.
27 Ga abin da Ubangiji yana cewa, “Dukan ƙasar za tă zama kufai, ko da yake ba zan hallaka ta gaba ɗaya ba.
Car ainsi parle l'Éternel: La dévastation couvrira le pays; mais je ne la ferai pas totale.
28 Saboda haka duniya za tă yi kuka sammai a bisa kuma za su yi duhu, domin na yi magana kuma ba zan fasa ba, na yanke shawara ba kuwa zan janye ba.”
Pour cela le pays est en deuil, et le ciel s'obscurcit, parce que je l'ai dit, je l'ai arrêté, et je ne m'en repens point, et n'en reviendrai point.
29 Da jin motsin mahayan dawakai da maharba kowane gari ya ruga da gudu. Waɗansu suka shiga kurmi; waɗansu suka hau cikin duwatsu. Dukan garuruwan sun fashe tas; babu wani da yake zama a ciki.
Au bruit des cavaliers et des archers toute ville est en fuite; on gagne les forêts, et on gravit les rochers; toute ville est abandonnée, il n'y reste personne.
30 Me kike yi, ya wadda aka ragargaza? Me ya sa kika sanya mulufi kika sa kayan adon zinariya? Me ya sa kika sa wa idanunki tozali? Kin yi kwalliyarki a banza. Masoyanki sun bar ki; suna neman ranki.
Et toi, ville désolée, que feras-tu? Quand même tu t'habilles de pourpre, que tu te pares d'une parure d'or, que tu bordes de fard tes yeux, en vain t'embellis-tu, les amants te dédaignent, ils en veulent à ta vie.
31 Na ji kuka kamar na mace mai naƙuda, nishi kamar na wadda take haihuwa ɗanta na fari, kukan Diyar Sihiyona tana haki, da ƙyar take numfashi, tana miƙa hannuwanta tana cewa, “Wayyo ni kaina! Na suma; an ba da raina ga masu kisana.”
Car j'entends comme la voix d'une femme en travail, un cri d'angoisse comme au premier enfantement: c'est la voix de la fille de Sion; elle soupire, étend les bras: « C'en est fait de moi! mon âme succombe sous les meurtriers! »

< Irmiya 4 >