< Irmiya 38 >
1 Shefatiya ɗan Mattan, Gedaliya ɗan Fashhur, Yukal ɗan Shelemiya da Fashhur ɗan Malkiya ya ji abin da Irmiya yana faɗa wa dukan mutane sa’ad da ya ce,
2 “Ga abin da Ubangiji yana cewa, ‘Duk wanda ya zauna a wannan birni zai mutu ta takobi, yunwa ko annoba, amma duk wanda ya je wurin Babiloniyawa zai rayu. Zai tsira da ransa, ya rayu.’
3 Kuma ga abin da Ubangiji yana cewa, ‘Tabbatacce za a ba da wannan birni ga sojojin sarkin Babilon, wanda zai ci shi.’”
4 Sai fadawa suka ce wa sarki, “Ya kamata a kashe wannan mutum. Yana karya zuciyar sojojin da suka ragu a birnin, da zuciyar sauran mutane, ta wurin abubuwan da yake faɗa musu. Wannan mutum ba ya neman jin daɗin zaman wannan sai dai wahala.”
5 “Yana a hannuwanku” Sarki Zedekiya ya amsa. “Sarki ba zai iya yin kome ya hana ku ba.”
6 Saboda haka suka kama Irmiya suka sa a rijiyar da ba ruwa a ciki ta Malkiya, ɗan sarki, wadda take a sansanin matsara. Suka saukar da Irmiya cikin rijiyar da ba ruwa da igiya; babu ruwa a cikinta, sai laka, Irmiya ya nutse cikin laka.
7 Amma Ebed-Melek mutumin Kush, wani hafsa a fada, ya ji cewa sun sa Irmiya a rijiyar da ba ruwa. Yayinda sarki yana zama a Ƙofar Benyamin,
8 Ebed-Melek ya fita daga fadar ya ce masa,
9 “Ranka yă daɗe sarki, waɗannan mutane sun yi mugun abu a duk abin da suka yi wa Irmiya annabi. Sun jefa shi cikin rijiyar da ba ruwa, inda zai mutu da yunwa gama ba sauran wani burodi a birnin.”
10 Sai sarki ya umarce Ebed-Melek mutumin Kush, “Ka ɗauko mutane talatin daga nan ku fid da Irmiya annabi daga rijiyar kafin ya mutu.”
11 Saboda haka Ebed-Melek ya ɗauki mutane tare da shi suka shiga ɗaki a ƙarƙashin baitulmali a cikin fada. Ya ɗauko waɗansu tsofaffin tsummoki da tsofaffi riguna daga can ya kuma zurara su da igiya wa Irmiya a cikin rijiyar.
12 Ebed-Melek mutumin Kush ya ce wa Irmiya, “Ka sa waɗannan tsummoki da tsofaffin rigunan a hammatarka, ya zarga igiya.” Irmiya ya yi haka,
13 suka kuma ja shi sama da igiya suka fid da shi daga rijiyar. Irmiya kuwa ya zauna a sansanin matsara.
14 Sai Sarki Zedekiya ya aika a kawo Irmiya annabi, ya sa aka kawo shi a ƙofa ta uku ta haikalin Ubangiji. Sai sarki ya ce wa Irmiya, “Zan tambaye ka wani abu, kada ka ɓoye mini wani abu.”
15 Irmiya ya ce wa Zedekiya, “In na ba ka amsa, ba za ka kashe ni ba? Ko da na ba ka shawara, ba za ka saurare ni ba.”
16 Amma Sarki Zedekiya ya yi wannan rantsuwa a kaɗaice ga Irmiya cewa, “Muddin Ubangiji yana a raye, wanda ya ba mu numfashi, ba zan kashe ka ko in ba da kai ga waɗanda suke neman ranka ba.”
17 Sa’an nan Irmiya ya ce wa Zedekiya, “Ga abin da Ubangiji Allah Maɗaukaki, Allah na Isra’ila, yana cewa, ‘In ka miƙa wuya ga hafsoshin sarkin Babilon, za a bar ka da rai ba za a kuma ƙone wannan birni ba; da kai da iyalinka za ku rayu.
18 Amma in ba ka miƙa wuya ga hafsoshin sarkin Babilon ba, za a ba da wannan birni ga Babiloniyawa za su kuma cinna mata wuta; kai kanka ba za ka tsira daga hannuwansu ba.’”
19 Sarki Zedekiya ya ce wa Irmiya, “Ina jin tsoron Yahudawan da suka tafi wurin Babiloniyawa, gama Babiloniyawa mai yiwuwa su ba da ni gare su su kuma wulaƙanta ni.”
20 Irmiya ya ce, “Ba za su ba da kai ba, ka yi biyayya ga Ubangiji ta wurin yin abin da na faɗa maka. Ta haka zai zama maka da amfani, za ka kuwa rayu.
21 Amma in ka ƙi miƙa wuya, ga abin da Ubangiji ya bayyana mini.
22 Za a fitar da dukan matan da suka ragu a fadan sarkin Yahuda wa hafsoshin sarkin Babilon. Waɗannan mata za su ce maka, “‘Sun ruɗe ka suka kuma rinjaye ka, waɗannan abokanka. Ƙafafunka sun nutse a cikin laka; abokanka sun yashe ka.’
23 “Za a kawo dukan matanka da’ya’yanka wa Babiloniyawa. Kai kanka ba za ka tsira daga hannuwansu ba amma za su sa sarkin Babilon zai kama ka; za a kuma ƙone wannan birni.”
24 Sai Zedekiya ya ce wa Irmiya, “Kada ka bar wani ya san wannan zance, in ba haka ba za ka mutu.
25 In fadawa suka ji cewa na yi magana da kai, suka kuma zo wurinka suka ce, ‘Faɗa mana abin da ka faɗa wa sarki da kuma abin da sarki ya faɗa maka; kada ka ɓoye mana, in ba haka za mu kashe ka,’
26 sai ka ce musu cewa, ‘Na roƙi sarki kada yă mai da ni gidan Yonatan in mutu a can.’”
27 Dukan fadawa kuwa suka zo wurin Irmiya suka tambaye shi, ya kuma faɗa musu dukan abin da sarki ya umarce shi ya faɗa. Saboda haka ba su ƙara ce masa kome ba, gama ba wanda ya ji zance da suka yi da sarki.
28 Irmiya kuwa ya zauna a sansanin masu gadi har ranar da aka ci Urushalima da yaƙi. Ga yadda aka ci Urushalima,