< Irmiya 34 >

1 Yayinda Nebukadnezzar sarkin Babilon da dukan sojojinsa da kuma dukan mulkokinsa da mutanen masarautar da yake mulki suna yaƙi da Urushalima da dukan garuruwan da suke kewaye, sai wannan magana ta zo wa Irmiya daga wurin Ubangiji cewa,
The word which came to Jeremiah from Jehovah, when Nebuchadnezzar king of Babylon and all his army and all the kingdoms of the earth that were under his dominion, and all the peoples, were fighting against Jerusalem, and against all the cities thereof, saying,
2 “Ga abin da Ubangiji, Allah na Isra’ila, yana cewa ka tafi wurin Zedekiya sarkin Yahuda ka faɗa masa, ‘Ga abin da Ubangiji yana cewa, ina gab da ba da wannan birni ga sarkin Babilon, zai kuwa ƙone ta.
Thus says Jehovah, the God of Israel: Go, and speak to Zedekiah king of Judah, and tell him, Thus says Jehovah: Behold, I will give this city into the hand of the king of Babylon, and he shall burn it with fire.
3 Ba za ka tsere daga hannunsa ba amma tabbatacce za a kama ka a kuma ba da kai gare shi. Za ka ga sarkin Babilon da idanunka, zai kuwa yi magana da kai fuska da fuska. Za ka kuwa tafi Babilon.
And thou shall not escape out of his hand, but shall surely be taken, and delivered into his hand. And thine eyes shall behold the eyes of the king of Babylon, and he shall speak with thee mouth to mouth, and thou shall go to Babylon.
4 “‘Duk da haka ka ji alkawarin Ubangiji, ya Zedekiya sarkin Yahuda. Ga abin da Ubangiji yake cewa game da kai. Ba za ka mutu ta takobi ba;
Yet hear the word of Jehovah, O Zedekiah king of Judah. Thus says Jehovah concerning thee, Thou shall not die by the sword;
5 za ka mutu cikin salama. Yadda mutane suka ƙuna wutar jana’iza don girmama kakanninka, sarakunan da suka riga ka, haka za su ƙuna wuta don girmama da kuma makokinka suna cewa, “Kaito, ya maigida!” Ni kaina na yi wannan alkawari, in ji Ubangiji.’”
thou shall die in peace. And with the burnings of thy fathers, the former kings who were before thee, so shall they make a burning for thee. And they shall lament thee, saying, Ah lord! For I have spoken the word, says Jehovah.
6 Sa’an nan annabi Irmiya ya faɗi dukan wannan wa Zedekiya sarkin Yahuda, a Urushalima,
Then Jeremiah the prophet spoke all these words to Zedekiah, king of Judah in Jerusalem,
7 yayinda sojojin sarkin Babilon suna yaƙi da Urushalima da sauran garuruwan Yahuda waɗanda suka ragu, Lakish da Azeka. Waɗannan su ne birane masu katanga kaɗai a Yahuda.
when the king of Babylon's army was fighting against Jerusalem, and against all the cities of Judah that were left, against Lachish and against Azekah, for these alone remained of the cities of Judah, fortified cities.
8 Maganar ta zo wa Irmiya daga Ubangiji bayan Sarki Zedekiya ya yi yarjejjeniya da duka mutane a Urushalima ya yi shelar’yanci wa bayi.
The word that came to Jeremiah from Jehovah, after the king Zedekiah had made a covenant with all the people who were at Jerusalem, to proclaim liberty to them,
9 Kowa ya’yantar da bayinsa da suke Ibraniyawa, maza da mata; kada kowa ya riƙe bawa wanda yake mutumin Yahuda.
that every man should let his man-servant, and every man his maid-servant, who is a Hebrew or a Hebrewess, go free, that none should make bondmen of them, namely, of a Jew his brother.
10 Saboda haka dukan fadawa da mutane suka yi yarjejjeniyar cewa za su’yantar da bayinsu maza da mata ba za su kuwa ƙara riƙe su bayi ba. Suka yarda, suka kuma sake su.
And all the rulers and all the people obeyed, who had entered into the covenant, that everyone should let his man-servant, and everyone his maid-servant, go free, that none should make bondmen of them any more. They obeyed, and let them go.
11 Amma daga baya suka canja ra’ayoyinsu suka maido bayinsu suka kuma sāke bautar da su.
But afterwards they turned, and caused the servants and the handmaids, whom they had let go free, to return, and brought them into subjection for servants and for handmaids.
12 Sai maganar Ubangiji ta zo wa Irmiya cewa,
Therefore the word of Jehovah came to Jeremiah from Jehovah, saying,
13 “Ga abin da Ubangiji, Allah na Isra’ila, yana cewa na yi alkawari da kakanni-kakanninku sa’ad da na fitar da su daga Masar, daga ƙasar bauta. Na ce,
Thus says Jehovah, the God of Israel: I made a covenant with your fathers in the day that I brought them forth out of the land of Egypt, out of the house of bondage, saying,
14 ‘A kowace shekara ta bakwai dole kowannenku yă’yantar da duk wani ɗan’uwa mutumin Ibraniyawa wanda aka sayar masa. Bayan ya yi muku hidima shekaru shida, dole ku bar shi yă tafi’yantacce.’ Amma kakanninku ba su saurare ni ba, ba su ji ni ba.
At the end of seven years ye shall let go every man his brother who is a Hebrew, who has been sold to thee, and has served thee six years. Thou shall let him go free from thee. But your fathers hearkened not to me, nor inclined their ear.
15 Bai daɗe ba da kuka tuba, kuka kuma yi abin da yake mai kyau a idona. Kowannenku ya yi shelar’yanci ga ɗan’uwansa. Kun ma yi yarjejjeniya a gabana a gidan da ake kira da Sunana.
And ye were now turned, and had done that which is right in my eyes, in proclaiming liberty every man to his neighbor. And ye had made a covenant before me in the house which is called by my name.
16 Amma yanzu kun juya kun kuma ɓata sunana; kowannenku ya mayar da bayi maza da matan da kuka’yantar su tafi inda suka ga dama. Kun sāke tilasta su su zama bayinku.
But ye turned and profaned my name, and caused every man his servant, and every man his handmaid, whom ye had let go free at their pleasure, to return. And ye brought them into subjection, to be to you for servants and for handmaids.
17 “Saboda haka, ga abin da Ubangiji yana cewa, kun yi mini rashin biyayya; ba ku yi shelar’yanci don’yan’uwanku ba. Saboda haka yanzu na yi muku shelar’yanci in ji Ubangiji,’yanci ga mutuwa ta takobi, annoba da kuma yunwa. Zan sa ku zama abin ƙyama ga sauran mulkokin duniya.
Therefore thus says Jehovah: Ye have not hearkened to me, to proclaim liberty, every man to his brother, and every man to his neighbor. Behold, I proclaim to you a liberty, says Jehovah-to the sword, to the pestilence, and to the famine. And I will make you to be tossed to and fro among all the kingdoms of the earth.
18 Mutanen da suka keta alkawarina da ba su cika sharuɗan alkawarin da suka yi a gabana ba, zan yi da su kamar ɗan maraƙin da suka yanka biyu suka bi ta tsakiyarsa.
And I will give the men who have transgressed my covenant, who have not performed the words of the covenant which they made before me, when they cut the calf in two and passed between the parts of it,
19 Shugabannin Yahuda da Urushalima, fadawa, firistoci da kuma dukan mutanen ƙasar waɗanda suka bi tsakanin ɗan maraƙin da aka yanka,
the rulers of Judah, and the rulers of Jerusalem, the eunuchs, and the priests, and all the people of the land, who passed between the parts of the calf,
20 zan ba da su ga abokan gābansu waɗanda suke neman ransu. Gawawwakinsu za su zama abincin tsuntsayen sararin sama da na namun jeji.
I will even give them into the hand of their enemies, and into the hand of those who seek their life. And their dead bodies shall be for food to the birds of the heavens, and to the beasts of the earth.
21 “Zan ba da Zedekiya sarkin Yahuda da fadawansa ga abokan gābansu waɗanda suke neman ransu, ga sojojin sarkin Babilon, waɗanda suke janye daga gare ku.
And I will give Zedekiah king of Judah, and his rulers, into the hand of their enemies, and into the hand of those who seek their life, and into the hand of the king of Babylon's army that has gone away from you.
22 Zan yi umarni, in ji Ubangiji, zan kuma komo da su wannan birni. Za su kuwa yi yaƙi da ita, su ƙwace ta su kuma ƙone ta. Zan kuma mai da garuruwan Yahuda kufai don kada wani ya zauna a can.”
Behold, I will command, says Jehovah, and cause them to return to this city. And they shall fight against it, and take it, and burn it with fire. And I will make the cities of Judah a desolation, without inhabitant.

< Irmiya 34 >