< Irmiya 30 >

1 Ga maganar da ta zo wa Irmiya daga Ubangiji.
הדבר אשר היה אל ירמיהו מאת יהוה לאמר
2 “Ga abin da Ubangiji, Allah na Isra’ila, yana cewa, ‘Ka rubuta a cikin littafi dukan maganganun da na yi maka.
כה אמר יהוה אלהי ישראל לאמר כתב לך את כל הדברים אשר דברתי אליך--אל ספר
3 Kwanaki suna zuwa,’ in ji Ubangiji, ‘sa’ad da zan komo da mutanena Isra’ila da Yahuda daga bauta in kuma maido da su ga ƙasar da na ba wa kakanninsu mallaka,’ in ji Ubangiji.”
כי הנה ימים באים נאם יהוה ושבתי את שבות עמי ישראל ויהודה אמר יהוה והשבתים אל הארץ אשר נתתי לאבותם--וירשוה
4 Ga kalmomin Ubangiji da ya yi game da Isra’ila da Yahuda,
ואלה הדברים אשר דבר יהוה אל ישראל--ואל יהודה
5 “Ga abin da Ubangiji yana cewa, “‘Ana jin kukan tsoro, razana, ba salama ba.
כי כה אמר יהוה קול חרדה שמענו--פחד ואין שלום
6 Ku tambaya ku ji. Namiji zai iya haifi’ya’ya? To, me ya sa kuke ganin kowane mai ƙarfi da hannuwansa a kwankwaso kamar mace mai naƙuda, kowace fuska ta koma fari?
שאלו נא וראו אם ילד זכר מדוע ראיתי כל גבר ידיו על חלציו כיולדה ונהפכו כל פנים לירקון
7 Kaito, gama wannan rana za tă zama mai girma! Babu kamar ta. Zai zama lokacin wahala wa Yaƙub, amma za a cece shi daga cikinta.
הוי כי גדול היום ההוא--מאין כמהו ועת צרה היא ליעקב וממנה יושע
8 “‘A wannan rana,’ in ji Ubangiji Maɗaukaki, ‘Zan karya karkiya daga wuyansu zan kuma cire musu kangi; baƙi ba za su ƙara bautar da su ba.
והיה ביום ההוא נאם יהוה צבאות אשבר עלו מעל צוארך ומוסרותיך אנתק ולא יעבדו בו עוד זרים
9 A maimakon haka, za su bauta wa Ubangiji Allahnsu Dawuda sarkinsu kuwa, wanda na tayar musu.
ועבדו את יהוה אלהיהם ואת דוד מלכם אשר אקים להם
10 “‘Saboda haka kada ka ji tsoro, ya Yaƙub bawana; kada ka karai, ya Isra’ila,’ in ji Ubangiji. ‘Tabbatacce zan cece ka daga wuri mai nesa, zuriyarka daga ƙasar zaman bautansu. Yaƙub zai sami salama da zaman lafiya, kuma ba wanda zai sa ya ji tsoro.
ואתה אל תירא עבדי יעקב נאם יהוה ואל תחת ישראל--כי הנני מושיעך מרחוק ואת זרעך מארץ שבים ושב יעקב ושקט ושאנן ואין מחריד
11 Ina tare da kai zan kuma cece ka,’ in ji Ubangiji. ‘Ko da yake na hallakar da dukan al’umma gaba ɗaya a inda na warwatsa ku, ba zan hallaka ku gaba ɗaya ba. Zan hore ku amma da adalci kaɗai; ba zan ƙyale ku ku tafi gaba ɗaya ba hukunci ba.’
כי אתך אני נאם יהוה להושיעך כי אעשה כלה בכל הגוים אשר הפצותיך שם אך אתך לא אעשה כלה ויסרתיך למשפט ונקה לא אנקך
12 “Ga abin da Ubangiji yana cewa, “‘Mikinku marar warkewa ne, raunin da kuka ji ya sha ƙarfin warkarwa.
כי כה אמר יהוה אנוש לשברך--נחלה מכתך
13 Babu wanda zai yi roƙo saboda damuwarku, ba magani domin mikinku babu warkarwa dominku.
אין דן דינך למזור רפאות תעלה אין לך
14 Dukan abokanku sun manta da ku; ba su ƙara kulawa da ku. Na buge ku kamar yadda abokin gāba zai yi na kuma hukunta ku yadda mai mugunta zai yi, domin laifinku da girma yake zunubanku kuma da yawa suke.
כל מאהביך שכחוך אותך לא ידרשו כי מכת אויב הכיתיך מוסר אכזרי--על רב עונך עצמו חטאתיך
15 Me ya sa kuke kuka a kan mikinku, wahalarku da ba ta da magani? Domin laifinku da girma yake da kuma zunubanku masu yawa na yi muku waɗannan abubuwa.
מה תזעק על שברך אנוש מכאבך על רב עונך עצמו חטאתיך--עשיתי אלה לך
16 “‘Amma duk wanda ya cinye ku za a cinye shi; dukan abokan gābanku za su tafi zaman bauta. Waɗanda suka washe ku su ma za a washe su; dukan waɗanda suka mai da ku ganima su ma zan mai da su ganima.
לכן כל אכליך יאכלו וכל צריך כלם בשבי ילכו והיו שאסיך למשסה וכל בזזיך אתן לבז
17 Amma zan mayar muku da lafiya in kuma warkar da mikinku,’ in ji Ubangiji, ‘domin ana ce da ku yasassu, Sihiyona wadda ba wanda ya kula da ita.’
כי אעלה ארכה לך וממכותיך ארפאך נאם יהוה כי נדחה קראו לך--ציון היא דרש אין לה
18 “Ga abin da Ubangiji yana cewa, “‘Zan mayar da wadatar tentin Yaƙub in kuma ji tausayin wuraren zamansa; za a sāke gina birnin a kufansa, fadar kuwa za tă tsaya a wurin da ya dace da ita.
כה אמר יהוה הנני שב שבות אהלי יעקוב ומשכנתיו ארחם ונבנתה עיר על תלה וארמון על משפטו ישב
19 Daga gare su waƙoƙi za su fito na godiya da kuma sowa ta farin ciki. Zan riɓaɓɓanya su, ba za su kuwa ragu ba; zan kawo musu ɗaukaka, ba kuwa za a ƙasƙanta su ba.
ויצא מהם תודה וקול משחקים והרבתים ולא ימעטו והכבדתים ולא יצערו
20 ’Ya’yansu za su kasance kamar a kwanakin dā jama’arsu kuma za su kahu a gabana; zan hukunta duk wanda ya zalunce su.
והיו בניו כקדם ועדתו לפני תכון ופקדתי על כל לחציו
21 Shugabansu zai zama ɗaya daga cikinsu; mai mulkinsu zai taso daga cikinsu. Zan kawo shi kusa zai kuma zo kusa da ni, gama wane ne zai miƙa kansa don yă yi kusa da ni?’ In ji Ubangiji.
והיה אדירו ממנו ומשלו מקרבו יצא והקרבתיו ונגש אלי כי מי הוא זה ערב את לבו לגשת אלי--נאם יהוה
22 ‘Saboda haka za ku zama mutanena, ni kuwa in zama Allahnku.’”
והייתם לי לעם ואנכי אהיה לכם לאלהים
23 Ga shi, hadarin Ubangiji zai fasu cikin hasala, iskar guguwa mai hurawa a kan kawunan mugaye.
הנה סערת יהוה חמה יצאה--סער מתגורר על ראש רשעים יחול
24 Fushi mai zafi na Ubangiji ba zai kawu ba sai ya cika manufofin zuciyarsa gaba ɗaya. A kwanaki masu zuwa za ku gane wannan.
לא ישוב חרון אף יהוה עד עשתו ועד הקימו מזמות לבו באחרית הימים תתבוננו בה

< Irmiya 30 >