< Irmiya 27 >

1 A farkon sarautar Zedekiya ɗan Yosiya sarkin Yahuda, wannan magana ta zo wa Irmiya daga Ubangiji.
猶大王約史雅的兒子漆德克雅第四年,上主有這話傳給耶肋米亞說:「
2 Ga abin da Ubangiji ya ce mini, “Ka yi karkiyar itace da maɗaurai ka ɗaura a wuyanka.
上主對我這樣說:你要備製繩索和木軛,放在你頸上;
3 Sa’an nan ka aika da saƙo zuwa wurin sarakunan Edom, Mowab, Ammon, Taya da Sidon ta bakin jakadu waɗanda suka zo Urushalima wurin Zedekiya sarkin Yahuda.
然後託那些來耶路撒冷覲見猶大王漆德克雅的使者,送給厄東王和摩阿布王,阿孟子民的王和提洛王以及漆冬王,
4 Ka ba su saƙo wa iyayengijinsu su ce, ‘Ga abin da Ubangiji Maɗaukaki, Allah na Isra’ila, yana cewa, “Ku faɗa wa iyayengijinku wannan.
吩咐他們對自己的主上說:萬軍的上主,以色列的天主這樣說:你們應如此對你們的主上說:
5 Da ikon mai ƙarfi da kuma hannuna da na miƙa na yi duniya da mutanenta da kuma dabbobin da suke ciki, na ba da ita ga duk wanda na ga dama.
是我以我的大能和我伸展的手臂,創造了大地、人類及地面上的走獸,我能把大地賜給我喜歡給的人。
6 Yanzu zan ba da dukan ƙasashenku ga bawana Nebukadnezzar sarkin Babilon; zan sa namun jeji ma su bauta masa.
現在我把這些土地交在我的僕人巴比倫王拿步高的手中,連田野的走獸我也賜給他,作他的奴隸;
7 Dukan al’ummai za su bauta masa da ɗansa da kuma jikansa har sai har lokacin ƙasarsa ya kai; sa’an nan al’ummai masu yawa da kuma manyan sarakuna za su kasance a ƙarƙashinsa.
列國要作他、他的兒子和孫子的奴隸,直到他國家的時運終於來到──他也不例外──那時必有強盛的民族和強大的君王來使他作奴隸。
8 “‘“Amma fa, duk al’umma ko mulkin da bai bauta wa Nebukadnezzar sarkin Babilon ba bai kuwa rusunar da wuyarsa ga karkiyarsa ba, zan hukunta wannan al’umma da takobi, yunwa da annoba, in ji Ubangiji, har sai na hallaka ta ta wurin hannunsa.
若一個民族或國家,不願作巴比倫王拿步高的奴隸,或不願屈服在巴比倫王軛下,我必以戰爭、饑饉和瘟疫懲罰這民族──上主的斷語──直至將他們悉數交在他手中。
9 Saboda haka kada ku saurari annabawanku, masu dubanku, masu fassarar mafarkanku, bokayenku ko masu maitancinku waɗanda suke ce muku, ‘Ba za ku bauta wa sarkin Babilon ba.’
所以你們不要聽從常對你們說:「你們決不會作巴比倫王的奴隸」的先知、占卦師、卜夢者、巫士和術士的話,
10 Suna muku annabcin ƙaryar ne kawai da za tă kau da ku daga ƙasarku; zan kore ku za ku kuwa hallaka.
因為他們給你們預言的只是謊話,致使你們遠故土,叫我驅逐你們,令你們趨於滅亡。
11 Amma duk al’ummar da ta rusuna da wuyarta a ƙarƙashin karkiyar sarkin Babilon ta kuma bauta masa, zan bar al’ummar ta zauna a ƙasarta ta noma ta, ta kuma zauna a can, in ji Ubangiji.”’”
至於引領接受巴比倫王的軛,甘願作他奴隸的民族,我必使他們仍留在本土──上主的斷語──在那裏安居樂業。
12 Na ba da wannan saƙo guda ga Zedekiya sarkin Yahuda. Na ce, “Ka rusunar da wuyanka a ƙarƙashin sarkin Babilon; ka bauta masa da kuma mutanensa, za ka kuwa rayu.
我於是全依照這些話轉告猶大王漆德克雅說:「你應引頸接受巴比倫王的軛,服事他和他的人民,你們纔可生存。
13 Me ya sa kai da mutanenka za ku mutu saboda takobi, yunwa da annoba waɗanda Ubangiji ya yi barazana wa duk al’ummar da ba za tă bauta wa sarkin Babilon ba?
為什麼你和你的人民寧願死於刀劍、饑饉和瘟疫,如同上主對不願服事巴比倫王的民族所警告的呢﹖
14 Kada ku saurari maganganun annabawa waɗanda suke ce muku, ‘Ba za ku bauta wa sarkin Babilon ba,’ gama annabcin ƙarya suke muku.
你們不要聽從對你們說:「不要服事巴比倫王」的先知的話,因為他們給你們預言的只是謊話;
15 ‘Ban aike su ba,’ in ji Ubangiji. ‘Suna annabcin ƙarya ne da sunana. Saboda haka, zan kore ku za ku kuwa hallaka, da ku da kuma annabawan da suke muku annabci.’”
我並沒有派遣他們──上主的斷語──他們竟奉我的名向你們預言,叫我驅逐你們,使你們和對你們說預言的先知同趨滅亡。」
16 Sai na ce wa firistoci da dukan waɗannan mutane, “Ga abin da Ubangiji yana cewa, kada ku saurari annabawan da suke cewa, ‘Ba daɗewa ba za a komo da kayan gidan Ubangiji daga Babilon.’ Suna muku annabcin ƙarya ne.
對司祭和這全體人民我也曾警告說:「上主這樣說:你們的先知們對你們說:看,上主殿宇的器皿,現在快要由巴比送回來了! 你們不要聽信,因為他們對你們預言的只是謊話。
17 Kada ku saurare su. Ku bauta wa sarkin Babilon, za ku kuwa rayu. Don me wannan birni zai zama kufai?
你們不要聽信他們,只管服事巴比倫王,就必生存。為什麼要使這城變為荒野﹖
18 In su annabawa ne da gaske suna kuma da maganar Ubangiji, bari su roƙi Ubangiji Maɗaukaki ya sa kada a kwashe kayayyakin da suka ragu a gidan Ubangiji da kuma a cikin fadar sarkin Yahuda da kuma cikin Urushalima a kai Babilon.
假使他們是先知,真有上主的話,請他們祈求萬軍的上主,使尚留在上主殿宇,猶大王宮和耶路撒冷的器皿,不致運到巴比倫去。
19 Gama ga abin da Ubangiji Maɗaukaki yana cewa game da ginshiƙai, kwatarniya, da dakalai, da sauran kayayyaki da aka bar su a birnin nan,
因為萬軍的上主這樣論到銅柱、銅海和銅座,以及在這城剩下的殘餘器皿,
20 waɗanda Nebukadnezzar sarkin Babilon ya kwashe sa’ad da ya kame Yekoniya ɗan Yehohiyakim sarkin Yahuda zuwa zaman bauta daga Urushalima zuwa Babilon tare da dukan manyan mutanen Yahuda da Urushalima,
即巴比倫王拿步高把猶大王約雅金的兒子耶苛尼雅,及猶大和耶路撒冷所有的貴族,從耶路撒冷擄到巴比倫時,沒有帶走的器皿,
21 I, ga abin da Ubangiji Maɗaukaki, Allah na Isra’ila yana cewa game da abubuwan da aka bari a gidan Ubangiji da kuma a cikin fadar sarkin Yahuda da Urushalima,
萬軍的上主,以色列的天主論到這些尚存在上主殿宇、猶大王宮和耶路撒冷的器皿,這樣說:
22 ‘Za a kwashe su zuwa Babilon a can kuwa za su kasance sai ranar da na neme su,’ in ji Ubangiji. ‘Sa’an nan zan komo da su in maido da su wannan wuri.’”
都要運到巴比倫去,留在那裏,直到我再來眷顧的一天──上主的斷語──那時,我必再取回來,放在原處。」

< Irmiya 27 >