< Irmiya 25 >
1 Magana ta zo wa Irmiya game da dukan mutanen Yahuda a shekara ta huɗu ta Yehohiyakim ɗan Yosiya sarkin Yahuda, wadda ta kasance shekara ta fari ta Nebukadnezzar sarkin Babilon.
The word which came to Jeremiah concerning all the people of Judah in the fourth year of Jehoiakim, the son of Josiah, king of Judah, which was the first year of Nebuchadnezzar, king of Babylon;
2 Saboda haka Irmiya annabi ya ce wa dukan mutanen Yahuda da dukan mazaunan Urushalima.
which Jeremiah the prophet spake to all the people of Judah, and to all the inhabitants of Jerusalem, saying: —
3 Shekaru ashirin da uku, daga shekara ta goma sha uku ta Yosiya ɗan Amon sarkin Yahuda har zuwa wannan rana, maganar Ubangiji ta zo mini na kuma yi muku magana sau da sau, amma ba ku saurara ba.
From the thirteenth year of Josiah, the son of Amon, king of Judah, even to this day, for three and twenty years, the word of Jehovah hath come to me, and I have spoken to you, rising early and speaking; but ye have not hearkened.
4 Ko da yake Ubangiji ya aika dukan bayinsa annabawa gare ku sau da sau, ba ku saurara ba, ba ku kuma kula ba.
Also Jehovah hath sent to you all his servants the prophets, rising early and sending them; but ye have not hearkened, nor inclined your ear to hear.
5 Sun ce, “Ku juye yanzu, kowannenku, daga mugayen hanyoyinku da mugayen ayyukanku, za ku kuwa iya zauna a ƙasar da Ubangiji ya ba ku da kuma kakanninku har abada abadin.
“Turn ye now,” said they, “every one from your evil way, and from your evil doings, and ye shall dwell in the land which Jehovah gave to you and to your fathers for ever and ever.
6 Kada ku bi waɗansu alloli don ku bauta ku kuma yi musu sujada; kada ku tsokane ni in yi fushi da abin da hannuwanku suka yi. Sa’an nan ba zan kawo muku lahani ba.”
And go not after strange gods to serve them, and to worship them, and provoke me not to anger with the work of your hands; and I will do you no hurt.”
7 “Amma ba ku saurare ni ba,” in ji Ubangiji, “kun tsokane ni da abin da kuka yi da hannuwanku, kuka kuma kawo lahani wa kanku.”
But ye have not hearkened to me, saith Jehovah, that ye might provoke me to anger with the works of your hands to your own hurt.
8 Saboda haka Ubangiji Maɗaukaki ya ce, “Domin kun ƙi ku saurara ga maganata,
Therefore thus saith Jehovah of hosts: Because ye have not hearkened to my words,
9 zan kira dukan mutanen arewa da bawana Nebukadnezzar sarkin Babilon,” in ji Ubangiji, “zan kuma kawo su su yi gāba da wannan ƙasa da mazaunanta da kuma gāba da dukan al’ummai da suke kewaye. Zan hallaka su sarai in kuma mai da su abin bantsoro da abin dariya, za su kuma zama kufai har abada.
behold, I will send and take all the nations of the North, saith Jehovah, and Nebuchadnezzar, the king of Babylon, my servant, and will bring them against this land and its inhabitants, and against all these nations round about, and will utterly destroy them, and make them an astonishment, and a hissing, and a perpetual desolation.
10 Zan kawar da muryoyin farin ciki da murna daga gare su, muryoyin amarya da na ango, ƙarar dutsen niƙa da hasken fitila.
Yea, I will take from them the voice of mirth, and the voice of gladness, the voice of the bridegroom and the voice of the bride, the sound of the mill-stones, and the light of the lamp.
11 Dukan wannan ƙasa za tă zama kango, kuma waɗannan al’ummai za su bauta wa sarkin Babilon shekaru saba’in.
And this whole land shall be a desolation and an astonishment; and these nations shall serve the king of Babylon seventy years.
12 “Amma sa’ad da shekaru saba’in ɗin suka cika, zan hukunta sarkin Babilon da kuma al’ummarsa, ƙasar Babiloniyawa, saboda laifinsu,” in ji Ubangiji, “in kuma mai da ita kango har abada.
But when seventy years shall have passed, I will punish the king of Babylon and his nation for their iniquity, saith Jehovah, and the land of the Chaldaeans, and I will make it a perpetual desolation.
13 Zan kawo wa wannan ƙasa dukan abubuwan na yi magana a kanta, dukan abubuwan da aka rubuta a wannan littafi, abubuwan da Irmiya kuma ya yi annabci a kan dukan al’ummai.
And I will bring upon that land all my words which I have pronounced against it, all that is written in this book, which Jeremiah hath prophesied against all the nations.
14 Su kansu al’ummai da sarakuna masu yawa za su bautar da su; zan sāka musu bisa ga ayyukansu da aikin hannuwansu.”
For they, even they, shall be brought into subjection to many nations and great kings. I will render to them according to their deeds, and according to the works of their own hands.
15 Ga abin da Ubangiji, Allah na Isra’ila, ya faɗa mini, “Ka karɓi kwaf ruwan inabin nan na fushina a wurina, ka sa dukan al’umman da na aike ka gare su, su sha.
For thus hath Jehovah, the God of Israel, said to me: Take this cup of the wine of wrath from my hand; and let all the nations to which I shall send thee drink of it.
16 Sa’ad da suka sha, za su yi ta tangaɗi su kuma yi hauka saboda takobin da zan aika a cikinsu.”
Let them drink, and stagger, and become mad because of the sword which I am about to send among them.
17 Saboda haka na karɓi kwaf daga hannun Ubangiji na sa dukan al’ummai waɗanda ya aiko ni wurinsu su sha.
So I took the cup from the hand of Jehovah, and gave it to all the nations to drink, to which Jehovah sent me;
18 Urushalima da garuruwan Yahuda, sarakunan da fadawanta, don su mai da su kufai da kuma abin bantsoro da ba’a da la’ana, yadda suke a yau;
to Jerusalem and to the cities of Judah, and to the kings thereof, and the princes thereof, to make them a desolation, and an astonishment, and a hissing, and a curse; [[as it is this day.]]
19 Fir’auna sarkin Masar, ma’aikatansa, fadawansa da dukan mutanensa,
To Pharaoh, king of Egypt, and to his servants, and to his princes, and to all his people,
20 da dukan baƙin da suke can; dukan sarakunan Uz; dukan sarakunan Filistiyawa (waɗannan na Ashkelon, Gaza, Ekron da mutanen da aka bari a Ashdod);
and all the allied people; and to all the kings of the land of Uz, and to all the kings of the land of the Philistines, and to Askelon, and to Gaza, and to Ekron, and to the remnant of Ashdod;
to Edom, and to Moab, and to the children of Ammon;
22 dukan sarakunan Taya da Sidon; sarakunan bakin teku a ƙetaren teku;
and to all the kings of Tyre, and to all the kings of Sidon, and to the kings of the lands which are beyond the sea;
23 Dedan, Tema, Buz da dukan waɗanda suke a manisantan wurare;
to Dedan, and to Tema, and to Buz, and to all that shave the cheek;
24 dukan sarakunan Arabiya da dukan sarakunan baƙin da suke zama a hamada;
and to all the kings of Arabia, and to all the kings of the allied people who dwell in the desert;
25 dukan sarakunan Zimri, Elam da Mediya;
and to all the kings of Zimri, and to all the kings of Elam, and to all the kings of Media;
26 da kuma dukan sarakunan arewa, nesa da kuma kusa, bi da bi, dukan mulkokin duniya. Bayan dukansu kuma, sai sarkin Sheshak ma yă sha.
and to all the kings of the North, those that are near, and those that are afar off with respect to each other, and to all the kingdoms of the earth which are upon the face of the ground; and the king of Sheshach shall drink after them.
27 “Sa’an nan na faɗa musu cewa, ‘Ga abin da Ubangiji Maɗaukaki, Allah na Isra’ila, yana cewa ku sha, ku bugu ku kuma yi amai, ku fāɗi, kada kuma ku ƙara tashi saboda takobin da zan aiko muku.’
And say to them, Thus saith Jehovah of hosts, the God of Israel: Drink ye and be drunken, and vomit, and fall to rise no more because of the sword which I am about to send among you.
28 Amma in suka ki su karɓi kwaf ɗin daga hannunka su sha, ka faɗa musu cewa, ‘Ga abin da Ubangiji Maɗaukaki yana cewa dole ku sha!
And if they refuse to take the cup from thy hand to drink, then say to them, Thus saith Jehovah of hosts: Ye shall surely drink!
29 Ga shi, na sa masifa tă yi aiki cikin birnin da ake kira da sunana, kuna gani za ku tafi ba hukunci? Ba za ku tafi ba hukunci ba, gama ina kawo wa dukan mazaunan duniya takobi, in ji Ubangiji Maɗaukaki.’
For behold, upon the city which is called by my name I begin to bring evil; and shall ye go wholly unpunished? Ye shall not go unpunished; for I am about to call the sword upon all the inhabitants of the earth, saith Jehovah of hosts.
30 “Yanzu ka yi annabcin dukan waɗannan maganganu a kansu ka kuma ce musu, “‘Ubangiji zai yi ruri daga bisa; zai yi tsawa daga mazauninsa mai tsarki ya kuma yi ruri da ƙarfi a kan ƙasarsa. Zai yi ihu kamar waɗanda suke matsin’ya’yan inabi, yi ihu a kan dukan waɗanda suke zaune a duniya.
Therefore, prophesy against them all these words, and say to them: —Jehovah shall roar from on high, From his holy habitation shall he utter his voice; He shall roar aloud against his dwelling-place; A shout like that of vintagers shall he raise Against all the inhabitants of the earth.
31 Hayaniya za tă taso har iyakar duniya, gama Ubangiji zai kawo tuhume-tuhume a kan al’ummai; zai kawo shari’a a kan dukan’yan adam ya kuma kashe mugaye da takobi,’” in ji Ubangiji.
An outcry shall reach to the ends of the earth; For Jehovah hath a controversy with the nations; He entereth into judgment with all flesh; The wicked will he give up to the sword, saith Jehovah.
32 Ga abin da Ubangiji Maɗaukaki yana cewa, “Duba! Masifa tana yaɗuwa daga al’umma zuwa al’umma; hadari mai girma yana tasowa daga iyakar duniya.”
Thus saith Jehovah of hosts: Behold, evil shall go forth from nation to nation, And a great whirlwind shall be raised up from the extremities of the earth.
33 A lokacin waɗanda Ubangiji ya kashe za su kasance a ko’ina, daga wannan bangon duniya zuwa wancan. Ba za a yi kuka dominsu, ba za a tattara su don a binne ba, amma za su zama kamar juji da an tsiba a ƙasa.
At that day shall the slain of Jehovah lie From one end of the earth to the other end of the earth; They shall not be lamented, nor gathered, nor buried; They shall be dung upon the ground.
34 Ku yi kuka ku kuma yi makoki, ku makiyaya; ku yi ta birgima a ƙura, ku shugabannin garke. Gama lokacin da za a yanka ku ya zo; za ku fāɗi ku kuma farfasa kamar tukunyar yumɓu mai kyau.
Howl, O ye shepherds, and cry! Roll yourselves in the dust, ye leaders of the flock, For your time to be slaughtered has come! And I will scatter you, and ye shall fall like a goodly vessel.
35 Makiyaya ba za su sami wurin da za su gudu su tafi ba, shugabannin garke ba za su sami wurin kuɓuta ba.
The shepherds shall have no way to flee, Nor the leaders of the flock to escape.
36 Ji kukan makiyaya, kururuwan shugabannin garke, gama Ubangiji yana hallaka wurin kiwo.
[[Hark!]] the voice of the cry of the shepherds, And the wailing of the leaders of the flock, Because Jehovah layeth waste their pasture!
37 Rafi mai gudu a hankali zai zama kango saboda zafin fushin Ubangiji.
Yea, the peaceful pastures are destroyed Because of the fierce anger of Jehovah.
38 Kamar zaki zai bar wurin ɓuyarsa, ƙasarsu kuma za tă zama kufai saboda takobin masu danniya da kuma saboda zafin fushin Ubangiji.
He hath left, like a lion, his covert; For their land is become desolate, Because of the wrath of the destroying sword, And because of the fierceness of his anger.