< Irmiya 24 >
1 Bayan Nebukadnezzar ya kwashi Yekoniya ɗan Yehohiyakim sarkin Yahuda da fadawa, da masu sana’a da masu zane zanen Yahuda daga Urushalima zuwa Babilon zaman bauta, Ubangiji ya nuna mini kwanduna biyu na’ya’yan ɓaure ajiye a gaban haikalin Ubangiji.
Jehovah shewed me, and behold, two baskets of figs, set before the temple of Jehovah, after that Nebuchadrezzar king of Babylon had carried away captive from Jerusalem, Jeconiah the son of Jehoiakim, the king of Judah, and the princes of Judah, and the craftsmen and smiths, and had brought them to Babylon.
2 Kwando guda yana da’ya’yan ɓaure masu kyau sosai, kamar waɗanda suka nuna da wuri; ɗayan kwandon kuma yana da’ya’yan ɓaure marasa kyau, sun yi muni har ba a iya ci.
One basket had very good figs, like the figs first ripe; and the other basket had very bad figs, which could not be eaten for badness.
3 Sa’an nan Ubangiji ya tambaye ni ya ce, “Me ka gani, Irmiya?” Na ce, “’Ya’yan ɓaure. Masu kyau ɗin suna da kyau sosai, amma munanan sun yi muni har ba a iya ci.”
And Jehovah said unto me, What seest thou, Jeremiah? And I said, Figs: the good figs very good; and the bad very bad, which cannot be eaten for badness.
4 Sai maganar Ubangiji ta zo mini cewa,
And the word of Jehovah came unto me, saying,
5 “Ga abin da Ubangiji, Allah na Isra’ila, yana cewa, ‘Kamar’ya’yan ɓauren nan masu kyau, haka zan kula da mutanen Yahuda waɗanda aka kwaso waɗanda na fisshe su daga wannan wuri zuwa ƙasar Babiloniyawa
Thus saith Jehovah, the God of Israel: Like these good figs, so will I regard for good them that are carried away captive of Judah, whom I have sent out of this place into the land of the Chaldeans;
6 Idanuna za su kula da su don kyautatawarsu, zan kuma komo da su wannan ƙasa. Zan gina su ba zan rushe su ba; zan dasa su ba kuwa zan tumɓuke su ba.
and I will set mine eyes upon them for good, and I will bring them again to this land; and I will build them and not pull them down, and I will plant them and not pluck them up.
7 Zan ba su zuciya don su san ni, cewa ni ne Ubangiji. Za su zama mutanena, zan zama Allahnsu, gama za su komo gare ni da dukan zuciyarsu.
And I will give them a heart to know me, that I am Jehovah; and they shall be my people, and I will be their God: for they shall return unto me with their whole heart.
8 “‘Amma kamar’ya’yan ɓauren nan marasa kyau, waɗanda sun yi muni har ba a iya ci,’ in ji Ubangiji, ‘haka zan yi da Zedekiya sarkin Yahuda, fadawansa da sauran mutanen da suka tsira a Urushalima, ko suna a wannan ƙasa ko suna zama a Masar.
And as the bad figs, which cannot be eaten for badness, surely, thus saith Jehovah: So will I make Zedekiah the king of Judah, and his princes, and the remnant of Jerusalem, that remain in this land, and them that dwell in the land of Egypt.
9 Zan mai da su abin ƙyama da masifa ga dukan mulkokin duniya, abin zargi da abin karin magana, abin ba’a da abin la’ana a duk inda zan kore su zuwa.
And I will give them over to be driven hither and thither unto all the kingdoms of the earth for evil, to be a reproach and a proverb, a taunt and a curse, in all places whither I shall drive them;
10 Zan aika da takobi, yunwa da annoba a kansu sai an hallaka su sarai daga ƙasar da na ba su da kuma kakanninsu.’”
and I will send among them the sword, the famine, and the pestilence, until they be consumed from off the land that I gave unto them and to their fathers.