< Irmiya 22 >

1 Ga abin da Ubangiji yana cewa, “Ka gangara zuwa fadan sarkin Yahuda ka yi shelar wannan saƙo a can ka ce,
Thus saith the Lord; Go thou, and go down to the house of the king of Juda, and thou shalt speak there this word,
2 ‘Ka ji maganar Ubangiji, ya sarkin Yahuda, kai da kake zaune kan gadon sarautar Dawuda, kai, da fadawanka da mutanenka waɗanda suke shiga ta waɗannan ƙofofi.
and thou shalt say, Hear the word of the Lord, O king of Juda, that sittest on the throne of David, thou, and thy house, and thy people, and they that go in at these gates:
3 Ga abin da Ubangiji yana cewa, ka yi abin da yake gaskiya da kuma daidai. Ka kuɓutar da wannan da aka yi masa ƙwace daga hannun mai zaluntarsa. Kada ka yi abin da ba daidai ba ko ka cuci baƙo, maraya ko gwauruwa, kuma kada ka zub da jini marar laifi a wannan wuri.
thus saith the Lord; Execute ye judgment and justice, and rescue the spoiled out of the hand of him that wrongs him: and oppress not the stranger, and orphan, and widow, and sin not, and shed no innocent blood in this place.
4 Gama in ka lura da bin waɗannan umarnai, to, sarakunan da suke zaune a gadon sarautar Dawuda za su shiga ta ƙofofin wannan fada, suna hawan kekunan yaƙi da dawakai, fadawansu da mutanensu suna musu rakiya.
For if ye will indeed perform this word, then shall there enter in by the gates of this house kings sitting upon the throne of David, and riding on chariots and horses, they, and their servants, and their people.
5 Amma in ba ku kiyaye waɗannan umarnai ba, in ji Ubangiji, na rantse da kaina cewa wannan fada za tă zama kufai.’”
But if ye will not perform these words, by myself have I sworn, saith the Lord, that this house shall be [brought] to desolation.
6 Gama ga abin da Ubangiji yana cewa game da wannan fadar sarkin Yahuda, “Ko da yake kina kamar Gileyad a gare ni, kamar ƙwanƙolin Lebanon, tabbatacce zan maishe ki hamada, kamar garuruwan da ba mazauna.
For thus saith the Lord concerning the house of the king of Juda; Thou art Galaad to me, [and] the head of Libanus: [yet] surely I will make thee a desert, [even] cities that shall not be inhabited:
7 Zan aika da mai hallakarwa a kanki, kowane mutum da makamansa, za su kuma yayyanka gumaguman al’ul na ki masu kyau su jefa su cikin wuta.
and I will bring upon thee a destroying man, and his axe: and they shall cut down thy choice cedars, and cast [them] into the fire.
8 “Mutane daga al’ummai da yawa za su ratsa cikin wannan birni su kuma tambayi juna suna cewa, ‘Me ya sa Ubangiji ya yi haka da wannan babban birni?’
And nations shall pass through this city, and each shall say to his neighbour, Why has the Lord done thus to this great city?
9 Amsar kuwa za tă zama, ‘Domin sun keta alkawarin Ubangiji Allahnsu, suka yi sujada suka kuma bauta wa waɗansu alloli.’”
And they shall say, Because they forsook the covenant of the Lord their God, and worshipped strange gods, and served them.
10 Kada ku yi kuka domin sarkin da ya mutu ko ku yi makoki saboda rashinsa; a maimako, ku yi kuka mai zafi saboda wanda aka kai zaman bauta, domin ba zai ƙara dawowa ba ko ya ƙara ganin ƙasarsa ta haihuwa.
Weep not for the dead, nor lament for him: weep bitterly for him that goes away: for he shall return no more, nor see his native land.
11 Gama ga abin da Ubangiji yana cewa game da Shallum ɗan Yosiya, wanda ya gāji mahaifinsa a matsayin sarkin Yahuda amma bai bar wurin nan ba, “Ba zai ƙara dawowa ba.
For thus saith the Lord concerning Sellem the son of Josias, who reigns in the place of Josias his father, who has gone forth out of this place; He shall not return thither any more:
12 Zai mutu a inda suka kai shi zaman bauta; ba zai ƙara ganin wannan ƙasa ba.”
but in that place whither I have carried him captive, there shall he die, and shall see this land no more.
13 “Kaiton wanda ya gina gidansa ta hanyar rashin adalci, ɗakunansa na sama kuma ta hanyar rashin gaskiya, yana sa mutanen ƙasarsa suna aiki a banza ba ya biyansu wahalarsu.
He that builds his house not with justice, and his upper chambers not with judgment, who works by means of his neighbour for nothing, and will by no means give him his reward.
14 Yana cewa, ‘Zan gina wa kaina babban fada da manyan ɗakuna.’ Ta haka sai ya yi musu manyan tagogi ya manne musu al’ul ya yi musu ado kuma da ruwan ja.
Thou hast built for thyself a well-proportioned house, airy chambers, fitted with windows, and wainscoted with cedar, and painted with vermilion.
15 “Wannan zai mai da kai sarki ne in kana da al’ul a kai a kai? Mahaifinka bai kasance da abinci da abin sha ba? Ya yi abin da yake gaskiya da kuma daidai saboda haka kome ya kasance da lafiya da shi.
Shalt thou reign, because thou art provoked with thy father Achaz? they shall not eat, and they shall not drink: it is better for thee to execute judgment and justice.
16 Ya kāre muradin matalauta da mabukata, ta haka kome ya tafi masa daidai. Ba abin da ake nufi da ba san ni ke nan ba?” In ji Ubangiji.
They understood not, they judged not the cause of the afflicted, nor the cause of the poor: is not this thy not knowing me? saith the Lord.
17 “Amma idanunka da zuciyarka sun kahu kawai a kan ƙazamar riba, da a kan zub da jinin marar laifi da kuma a kan danniya da zalunci.”
Behold, thine eyes are not good, nor thine heart, but [they go] after thy covetousness, and after the innocent blood to shed it, and after acts of injustice and slaughter, to commit them.
18 Saboda haka ga abin da Ubangiji yana cewa game da Yehohiyakim ɗan Yosiya sarkin Yahuda, “Ba za su yi kuka dominsa ba, ‘Kaito, ɗan’uwana! Kaito,’yar’uwata!’ Ba za su yi kuka dominsa ba, ‘Kaito, maigidana! Kaito, darajarsa!’
Therefore thus saith the Lord concerning Joakim son of Josias, king of Juda, even concerning this man; they shall not bewail him, [saying], Ah brother! neither shall they at all weep for him, [saying], Alas Lord.
19 Za a binne shi kamar jaki za a ja shi a ƙasa a jefar a bayan ƙofofin Urushalima.”
He shall be buried with the burial of an ass; he shall be dragged roughly along and cast outside the gate of Jerusalem.
20 “Ka haura zuwa Lebanon ka yi kuka, bari a ji muryarka a Bashan, yi kuka daga Abarim, gama an murƙushe dukan abokanka.
Go up to Libanus, and cry; and utter thy voice to Basan, and cry aloud to the extremity of the sea: for all thy lovers are destroyed.
21 Na ja maka kunne sa’ad da kake zama lafiya, amma sai ka ce, ‘Ba zan saurara ba!’ Wannan halinka ne tun kana matashi; ba ka yi mini biyayya ba.
I spoke to thee on [occasion of] thy trespass, but thou saidst, I will not hearken. This [has been] thy way from thy youth, thou hast not hearkened to my voice.
22 Iska za tă koro dukan makiyayanka abokanka kuma za su tafi zaman bauta. Sa’an nan za ka sha kunya a kuma walaƙanta ka saboda dukan muguntarka.
The wind shall tend all thy shepherds, and thy lovers shall go into captivity; for then shalt thou be ashamed and disgraced because of all thy lovers.
23 Kai da kake zama a ‘Lebanon,’ kai da kake sheƙa a gine-ginen al’ul za ka yi nishi sa’ad da zafi ya auka maka, zafi kamar na mace mai naƙuda!
O thou that dwellest in Libanus, making thy nest in the cedars, thou shalt groan heavily, when pangs as of a travailing woman are come upon thee.
24 “Muddin ina raye,” in ji Ubangiji, “ko kai, Yehohiyacin ɗan Yehohiyakim sarkin Yahuda, ka zama zoben hatimin dama a hannuna na dama, zan kwaɓe ka.
[As] I live, saith the Lord, though Jechonias son of Joakim king of Juda were indeed the seal upon my right hand, thence would I pluck thee;
25 Zan ba da kai ga waɗanda suke neman ranka, waɗanda kake tsoro, ga Nebukadnezzar sarkin Babilon da kuma ga Babiloniyawa.
and I will deliver thee into the hands of them that seek thy life, before whom thou art afraid, into the hands of the Chaldeans.
26 Zan jefar da kai da mahaifiyar da ta haife ka zuwa wata ƙasa, inda babu ɗayanku da aka haifa a wurin, a can kuma za ka mutu.
And I will cast forth thee, and thy mother that bore thee, into a land where thou wast not born; and there ye shall die.
27 Ba za ka ƙara dawo ƙasar da kake marmarin dawowa ba.”
But they shall by no means return to the land which they long for in their souls.
28 Wannan mutum Yehohiyacin ne da aka rena, fasasshen tukunya, abin da babu wanda yake so? Me ya sa za a jefar da shi da’ya’yansa a jefar da su a ƙasar da ba su sani ba?
Jechonias is dishonoured as a good-for-nothing vessel; for he is thrown out and cast forth into a land which he knew not.
29 Ya ke ƙasa, ƙasa, ƙasa, ki ji maganar Ubangiji!
Land, land, hear the word of the Lord.
30 Ga abin da Ubangiji yana cewa, “Ka rabu da wannan mutum sai ka ce marar’ya’ya, mutumin da ba zai yi nasara a rayuwarsa ba, gama babu zuriyarsa da za tă yi nasara babu wani da zai zauna a kursiyin Dawuda ko ya ƙara yin mulkin Yahuda.”
Write ye this man an outcast: for there shall none of his seed at all grow up to sit on the throne of David, [or as] a prince yet in Juda.

< Irmiya 22 >