< Irmiya 21 >

1 Magana ta zo wa Irmiya daga Ubangiji sa’ad da Sarki Zedekiya ya aiki Fashhur ɗan Malkiya da firist Zefaniya ɗan Ma’asehiya gare shi. Suka ce masa,
The word which came to Jeremiah from the LORD, when king Zedekiah sent to him Pashhur the son of Malchijah, and Zephaniah the son of Maaseiah, the priest, saying,
2 “Yanzu ka roƙi mana Ubangiji saboda Nebukadnezzar sarkin Babilon yana kawo mana yaƙi. Wataƙila Ubangiji zai yi mana waɗansu abubuwa banmamaki kamar a lokacin baya don yă janye daga gare mu.”
"Please inquire of the LORD for us; for Nebuchadnezzar king of Babylon makes war against us: perhaps the LORD will deal with us according to all his wondrous works, that he may go up from us."
3 Amma Irmiya ya amsa musu ya ce, “Ku faɗa wa Zedekiya cewa,
Then Jeremiah said to them, "You shall tell Zedekiah:
4 ‘Ga abin da Ubangiji, Allah na Isra’ila, yake cewa ina shirin juya kayan yaƙin da suke a hannuwanka a kanka, waɗanda kake amfani don ka yaƙi sarki Babilon da kuma Babiloniyawa waɗanda suka kewaye katangar birnin, zan kuwa tsiba kayan yaƙinka a tsakiyar birnin nan.
'Thus says the LORD, the God of Israel, "Look, I will turn back the weapons of war that are in your hands, with which you fight against the king of Babylon, and against the Chaldeans who besiege you, without the walls; and I will gather them into the midst of this city.
5 Ni da kaina zan yi yaƙi da kai da miƙaƙƙen hannu mai ƙarfi cikin fushi da hasala mai girma.
I myself will fight against you with an outstretched hand and with a strong arm, even in anger, and in wrath, and in great indignation.
6 Zan kashe waɗanda suke zaune a wannan birni, mutane da dabbobi za su kuwa mutu da muguwar annoba.
I will strike the inhabitants of this city, both man and animal: they shall die of a great pestilence.
7 Bayan wannan, in ji Ubangiji, zan ba da Zedekiya sarkin Yahuda, fadawansa da kuma mutanen wannan birni waɗanda suka tsira daga annoba, takobi da kuma yunwa, ga Nebukadnezzar sarkin Babilon da kuma ga abokan gābansu waɗanda suke neman ransu. Zai kashe su da takobi; ba zai ji tausayinsu ko ya yi musu jinƙai ko ya yi juyayinsu ba.’
Afterward," says the LORD, "I will deliver Zedekiah king of Judah, and his servants, and the people, even such as are left in this city from the pestilence, from the sword, and from the famine, into the hand of Nebuchadnezzar king of Babylon, and into the hand of their enemies, and into the hand of those who seek their life: and he shall strike them with the edge of the sword; he shall not spare them, neither have pity, nor have mercy."'
8 “Bugu da ƙari, ka faɗa wa mutanen cewa, ‘Ga abin da Ubangiji yana cewa, ga shi na sa a gabanku hanyar rai da hanyar mutuwa.
To this people you shall say, "Thus says the LORD: 'Look, I set before you the way of life and the way of death.
9 Duk wanda ya zauna a wannan birni zai mutu ta takobi, yunwa ko annoba. Amma duk wanda ya fita ya miƙa kansa ga Babiloniyawa waɗanda suka kewaye ku zai rayu; zai kuɓutar da ransa.
He who remains in this city shall die by the sword, and by the famine, and by the pestilence; but he who goes out, and passes over to the Chaldeans who besiege you, he shall live, and his life shall be to him for a prey.
10 Na ƙudura in yi wa wannan birni lahani ba alheri ba, in ji Ubangiji. Za a ba da shi a hannuwan sarki Babilon, zai kuwa hallaka shi da wuta.’
For I have set my face on this city for evil, and not for good,' says the LORD: 'it shall be given into the hand of the king of Babylon, and he shall burn it with fire.'
11 “Ban haka ma, ka faɗa wa gidan sarauta na Yahuda cewa, ‘Ku saurari maganar Ubangiji;
Touching the house of the king of Judah, hear the word of the LORD:
12 Ya gidan Dawuda ga abin da Ubangiji yana cewa, “‘Ku yi gaskiya kowace safiya; ku kuɓuta daga hannun mai danniya wannan da aka yi wa fashi in ba haka ba hasalata za tă sauka ta kuma ci kamar wuta saboda muguntar da kuka aikata za tă ci babu wanda zai kashe ta.
'House of David, thus says the LORD, "Execute justice in the morning, and deliver him who is robbed out of the hand of the oppressor, lest my wrath go forth like fire, and burn so that none can quench it, because of the evil of your doings.
13 Ina gāba da ku, mazaunan Urushalima, ku da kuke zama a bisa wannan kwari kan dutsen da yake a fili, in ji Ubangiji ku da kuke cewa, “Wa zai iya yaƙe mu? Wa zai iya shiga mafakarmu?”
Look, I am against you, O inhabitant of the valley, and of the rock of the plain," says the LORD; "you that say, 'Who shall come down against us? Or who shall enter into our habitations?'
14 Zan hukunta ku gwargwadon ayyukanku, in ji Ubangiji. Zan sa wuta a kurminku da za tă cinye kome da yake kewaye da ku.’”
I will punish you according to the fruit of your doings," says the LORD; "and I will kindle a fire in her forest, and it shall devour all that is around her."'"

< Irmiya 21 >