< Irmiya 19 >
1 Ga abin da Ubangiji yana cewa, “Tafi ka sayo tulu a wurin mai ginin tukwane. Ka ɗauki waɗansu dattawan jama’a da kuma na firistoci
Thus saith the LORD, Go and get a potter’s earthen bottle, and [take] of the ancients of the people, and of the ancients of the priests;
2 ku fita zuwa Kwarin Ben Hinnom, kusa da mashigin Ƙofar Kasko. A can ka furta maganganun da na faɗa maka,
And go forth unto the valley of the son of Hinnom, which [is] by the entry of the east gate, and proclaim there the words that I shall tell thee,
3 ka ce, ‘Ku ji maganar Ubangiji, ya sarakunan Yahuda da kuma mutanen Urushalima. Ga abin da Ubangiji Maɗaukaki, Allah na Isra’ila, yana cewa ku saurara! Zan kawo masifa a wannan wuri, wanda duk ya ji, kunnuwansa za su kaɗa.
And say, Hear ye the word of the LORD, O kings of Judah, and inhabitants of Jerusalem; Thus saith the LORD of hosts, the God of Israel; Behold, I will bring evil upon this place, the which whosoever heareth, his ears shall tingle.
4 Gama sun yashe ni suka kuma mai da wannan wuri ya zama na baƙin alloli; sun ƙone hadayu a cikinsa wa allolin da ko su ko kakanninsu ko sarakunan Yahuda ba su taɓa sani ba, suka kuma cika wannan wuri da jini marasa laifi.
Because they have forsaken me, and have estranged this place, and have burned incense in it unto other gods, whom neither they nor their fathers have known, nor the kings of Judah, and have filled this place with the blood of innocents;
5 Suka gina masujadai na kan tudu na Ba’al don su ƙona’ya’yansu maza a cikin wuta a matsayin hadaya ga Ba’al abin da ban umarta ba, ban ambata ba, bai kuma zo mini ba.
They have built also the high places of Baal, to burn their sons with fire [for] burnt offerings unto Baal, which I commanded not, nor spake [it], neither came [it] into my mind:
6 Saboda haka ku lura, kwanaki suna zuwa, in ji Ubangiji, sa’ad da mutane ba za su ƙara ce da wannan wuri Tofet ko Kwarin Ben Hinnom ba, amma za su ce da shi Kwarin Kisa.
Therefore, behold, the days come, saith the LORD, that this place shall no more be called Tophet, nor The valley of the son of Hinnom, but The valley of slaughter.
7 “‘A wannan wuri zan lalace dabarun Yahuda da na Urushalima. Zan sa a kashe su da takobi a gaban abokan gābansu, a hannuwan waɗanda suke neman ransu, zan kuma ba da gawawwakinsu su zama abinci ga tsuntsayen sararin sama da kuma namun jeji.
And I will make void the counsel of Judah and Jerusalem in this place; and I will cause them to fall by the sword before their enemies, and by the hands of them that seek their lives: and their carcases will I give to be meat for the fowls of the heaven, and for the beasts of the earth.
8 Zan ragargazar da wannan birni in mai da shi abin reni, duk wanda ya wuce zai yi mamaki ya kuma yi tsaki saboda dukan masifunsa.
And I will make this city desolate, and an hissing; every one that passeth thereby shall be astonished and hiss because of all the plagues thereof.
9 Zan sa su ci naman’ya’yansu maza da mata, za su kuma ci naman juna a lokacin damuwar ƙawanya da abokan gāban da suke neman ransu za su yi musu.’
And I will cause them to eat the flesh of their sons and the flesh of their daughters, and they shall eat every one the flesh of his friend in the siege and straitness, wherewith their enemies, and they that seek their lives, shall straiten them.
10 “Sa’an nan ka fasa tulun yayinda waɗanda suka tafi tare da kai suna duba,
Then shalt thou break the bottle in the sight of the men that go with thee,
11 ka kuma ce musu, ‘Ga abin da Ubangiji Maɗaukaki yana cewa zan farfasa wannan al’umma da wannan birni kamar yadda aka farfasa wannan tulu mai ginin tukwane ba kuwa zai gyaru ba. Za a binne matattu a Tofet har sai ba sauran wuri.
And shalt say unto them, Thus saith the LORD of hosts; Even so will I break this people and this city, as [one] breaketh a potter’s vessel, that cannot be made whole again: and they shall bury [them] in Tophet, till [there be] no place to bury.
12 Ga abin da zan yi wa wannan wuri da waɗanda suke zaune a nan, in ji Ubangiji. Zan mai da wannan birni kamar Tofet.
Thus will I do unto this place, saith the LORD, and to the inhabitants thereof, and [even] make this city as Tophet:
13 Gidaje a Urushalima da waɗannan na sarakunan Yahuda za su ƙazantu kamar wannan wuri, Tofet, dukan gidajen da suke ƙone turare a kan rufi wa duk rundunan taurari suna kuma zuba hadayun sha ga sauran alloli.’”
And the houses of Jerusalem, and the houses of the kings of Judah, shall be defiled as the place of Tophet, because of all the houses upon whose roofs they have burned incense unto all the host of heaven, and have poured out drink offerings unto other gods.
14 Sa’an nan Irmiya ya komo daga Tofet, inda Ubangiji ya aike shi don yă yi annabci, ya tsaya a filin haikalin Ubangiji ya ce wa mutane duka,
Then came Jeremiah from Tophet, whither the LORD had sent him to prophesy; and he stood in the court of the LORD’s house; and said to all the people,
15 “Ga abin da Ubangiji Maɗaukaki, Allah na Isra’ila, yana cewa, ‘Ku saurara! Zan kawo wa wannan birni da ƙauyukan da suke kewayensa kowace masifar da na furta a kansu, domin sun yi taurinkai, ba su kuwa saurari maganata ba.’”
Thus saith the LORD of hosts, the God of Israel; Behold, I will bring upon this city and upon all her towns all the evil that I have pronounced against it, because they have hardened their necks, that they might not hear my words.