< Irmiya 18 >

1 Ga maganar da ta zo wa Irmiya daga wurin Ubangiji.
הדבר אשר היה אל ירמיהו מאת יהוה לאמר
2 “Ka gangara zuwa gidan mai ginin tukwane, a can zan ba ka saƙona.”
קום וירדת בית היוצר ושמה אשמיעך את דברי
3 Sai na gangara zuwa gidan mai ginin tukwane, na gan shi yana aiki a na’urar ginin tukwanen.
וארד בית היוצר והנהו (והנה הוא) עשה מלאכה על האבנים
4 Amma tukunyar da yake ginawa ta lalace a hannuwansa, sai mai ginin tukwanen ya sāke gina wata tukunya dabam, yana gyara ta yadda ya ga dama.
ונשחת הכלי אשר הוא עשה בחמר--ביד היוצר ושב ויעשהו כלי אחר כאשר ישר בעיני היוצר לעשות
5 Sai maganar Ubangiji ta zo mini cewa,
ויהי דבר יהוה אלי לאמור
6 “Ya gidan Isra’ila, ashe, ba zan yi da ku yadda mai ginin tukwanen nan yake yi ba?” In ji Ubangiji. “Kamar yumɓu a hannun mai ginin tukwane, haka kuke a hannuna, ya gidan Isra’ila.
הכיוצר הזה לא אוכל לעשות לכם בית ישראל--נאם יהוה הנה כחמר ביד היוצר כן אתם בידי בית ישראל
7 A duk lokacin da na yi shela cewa za a tumɓuke, a kakkarya a kuma hallaka wata al’umma ko mulki,
רגע אדבר על גוי ועל ממלכה לנתוש ולנתוץ ולהאביד
8 in wannan al’ummar da na yi wa gargaɗi ta tuba daga muguntarta, sai in janye in kuma fasa kawo mata masifar da na yi niyya aukar mata.
ושב הגוי ההוא מרעתו אשר דברתי עליו--ונחמתי על הרעה אשר חשבתי לעשות לו
9 In kuma wani lokaci na yi shela cewa za a gina wata al’umma ko mulki a kuma kafa ta,
ורגע אדבר על גוי ועל ממלכה לבנות ולנטוע
10 in ta yi mugunta a gabana ba tă kuwa yi mini biyayya ba, sai in janye alherin da na yi niyya in yi mata.
ועשה הרעה (הרע) בעיני לבלתי שמע בקולי--ונחמתי על הטובה אשר אמרתי להיטיב אותו
11 “Yanzu fa, sai ka faɗa wa mutanen Yahuda da waɗanda suke zaune a Urushalima, ‘Ga abin da Ubangiji yana cewa ga shi! Ina shirya muku masifa ina ƙirƙiro dabara a kanku. Saboda haka ku juya daga mugayen hanyoyinku, kowannenku, ku canja hanyoyinku da kuma ayyukanku.’
ועתה אמר נא אל איש יהודה ועל יושבי ירושלם לאמר כה אמר יהוה הנה אנכי יוצר עליכם רעה וחשב עליכם מחשבה שובו נא איש מדרכו הרעה והיטיבו דרכיכם ומעלליכם
12 Amma za su amsa su ce, ‘Ba amfani. Za mu ci gaba da shirye-shiryenmu; kowannenmu zai bi taurin muguwar zuciyarsa.’”
ואמרו נואש כי אחרי מחשבותינו נלך ואיש שררות לבו הרע נעשה
13 Saboda haka ga abin da Ubangiji yana cewa, “Ku tattambaya a cikin al’ummai. Wa ya taɓa jin irin wannan abu? Budurwa Isra’ila ta yi mugun abu mafi banƙyama.
לכן כה אמר יהוה שאלו נא בגוים מי שמע כאלה שעררת עשתה מאד בתולת ישראל
14 Dusar ƙanƙarar Lebanon ta taɓa rabuwa da kan duwatsun Lebanon? Ruwan mai sanyinsa daga rafuffukansa masu nesa sun taɓa daina gudu?
היעזב מצור שדי שלג לבנון אם ינתשו מים זרים קרים--נוזלים
15 Duk da haka mutanena sun manta da ni; sun ƙone turare wa gumaka marasa amfani, waɗanda suka sa su tuntuɓe a al’amuransu a hanyoyin dā. Sun sa suka yi tafiya a ɓarayin hanyoyi a hanyoyin da ba a gina ba.
כי שכחני עמי לשוא יקטרו ויכשלום בדרכיהם שבילי עולם ללכת נתיבות דרך לא סלולה
16 Ƙasarsu za tă zama kufai, abin reni har abada; dukan waɗanda suka wuce za su yi mamaki su kaɗa kai.
לשום ארצם לשמה שרוקת (שריקת) עולם כל עובר עליה ישם ויניד בראשו
17 Kamar iska daga gabas zan warwatsa su a gaban abokan gābansu; zan juya musu bayana, ba zan nuna musu fuskata ba a ranar masifarsu.”
כרוח קדים אפיצם לפני אויב ערף ולא פנים אראם ביום אידם
18 Suka ce, “Zo mu shirya wa Irmiya maƙarƙashiya; gama koyarwar doka da firist ya yi ba za tă ɓace ba, haka ma shawara daga mai hikima da kuma magana daga annabawa. Saboda haka ku zo, mu fāɗa masa da harsunanmu kada mu saurari wani abin da zai faɗa.”
ויאמרו לכו ונחשבה על ירמיהו מחשבות--כי לא תאבד תורה מכהן ועצה מחכם ודבר מנביא לכו ונכהו בלשון ואל נקשיבה אל כל דבריו
19 Ka saurare ni, ya Ubangiji ka ji abin da masu zargina suke cewa!
הקשיבה יהוה אלי ושמע לקול יריבי
20 Ya kamata a sāka wa alheri da mugunta? Duk da haka sun haƙa mini rami. Ka tuna cewa na tsaya a gabanka na kuma yi magana a madadinsu don ka janye fushinka daga gare su.
הישלם תחת טובה רעה כי כרו שוחה לנפשי זכר עמדי לפניך לדבר עליהם טובה להשיב את חמתך מהם
21 Saboda haka ka kawo wa’ya’yansu yunwa; ka miƙa su ga ikon takobi. Bari matansu su zama marasa’ya’ya da gwauraye; bari a kashe mazansu, a kuma kashe samarinsu da takobi a yaƙi.
לכן תן את בניהם לרעב והגרם על ידי חרב ותהינה נשיהם שכלות ואלמנות ואנשיהם יהיו הרגי מות בחוריהם מכי חרב במלחמה
22 Bari a ji kuka daga gidajensu sa’ad da ka kawo masu hari a kansu farat ɗaya, gama sun haƙa rami don su kama ni suka kuma kafa tarko wa ƙafafuna.
תשמע זעקה מבתיהם כי תביא עליהם גדוד פתאם כי כרו שיחה (שוחה) ללכדני ופחים טמנו לרגלי
23 Amma Ya Ubangiji, ka san duk maƙarƙashiyarsu, na neman su kashe ni. Kada ka gafarta musu laifofinsu ko ka shafe zunubansu daga gabanka. Bari a tumɓuke su a gabanka; ka yi da su sa’ad da kake fushi.
ואתה יהוה ידעת את כל עצתם עלי למות--אל תכפר על עונם וחטאתם מלפניך אל תמחי והיו (ויהיו) מכשלים לפניך בעת אפך עשה בהם

< Irmiya 18 >