< Irmiya 17 >
1 “An rubuta zunubin Yahuda da alƙalamin ƙarfe, an rubuta da tsinin dutse, a kan allunan zukatansu da kuma a kan ƙahonin bagadansu.
“O pecado de Judá é escrito com uma caneta de ferro, e com a ponta de um diamante. Ela está gravada na tábua de seu coração, e nos chifres de seus altares.
2 Har’ya’yansu ma sun tuna bagadansu da ginshiƙan Asheransu kusa da itatuwa masu duhuwa da kuma a kan tuddai masu tsayi.
Até seus filhos se lembram de seus altares e seus postes de Asherah junto às árvores verdes nas altas colinas.
3 Dutsena a ƙasar da dukiyarku na ƙasar da dukan arzikinku za a ba da su ganima, tare da masujadanku na kan tuddai, saboda zunubi ko’ina a ƙasarku.
Minha montanha no campo, Darei sua substância e todos os seus tesouros por um saque, e seus lugares altos, por causa do pecado, por todas as suas fronteiras.
4 Saboda laifinku za ku rasa gādon da na ba ku. Zan bautar da ku ga abokan gābanku a ƙasar da ba ku sani ba, domin kun husata ni, zai kuwa ci har abada.”
Você, mesmo de si mesmo, deixará de fazer parte de sua herança que lhe dei. Eu farei com que você sirva seus inimigos na terra que você não conhece, pois vocês acenderam um fogo em minha raiva que arderá para sempre”.
5 Ga abin da Ubangiji yana cewa, “La’ananne ne mutumin da yake dogara ga mutum, wanda ya dogara ga jiki don ƙarfi wanda kuma zuciyarsa ta juya wa Ubangiji baya.
diz Yahweh: “Maldito é o homem que confia no homem”, depende da força da carne, e cujo coração parte de Yahweh.
6 Zai zama kamar ɗan kurmi a ƙasar da take kango; ba za su ga arziki sa’ad da ya zo ba. Za su zauna a busassun wuraren hamada, a cikin ƙasar gishiri inda ba kowa.
Pois ele será como um arbusto no deserto, e não verá quando o bem vier, mas habitará os lugares ressequidos do deserto, uma terra salgada desabitada.
7 “Amma mai albarka ne mutumin da yake dogara ga Ubangiji, wanda ƙarfin halinsa yana daga Ubangiji.
“Abençoado é o homem que confia em Yahweh, e cuja confiança está em Yahweh.
8 Za su zama kamar itacen da aka dasa kusa da ruwa wanda ya miƙa saiwoyinsa zuwa cikin rafi. Ba ya jin tsoro sa’ad da zafi ya zo; ganyayensa kullum kore suke. Ba shi da damuwa a shekarar fări ba ya taɓa fasa ba da’ya’ya.”
Pois ele será como uma árvore plantada junto às águas, que espalha suas raízes pelo rio, e não terá medo quando o calor chegar, mas sua folha será verde, e não se preocupará no ano da seca. Não deixará de dar frutos.
9 Zuciya ta fi kome ruɗu ta fi ƙarfin warkewa. Wa zai iya gane ta?
O coração é enganador acima de todas as coisas e é extremamente corrupto. Quem pode conhecê-lo?
10 “Ni Ubangiji nakan bincike zuciya in gwada tunani, don in sāka wa kowane mutum bisa ga halinsa, bisa ga ayyukansa.”
“Eu, Yahweh, procuro a mente. Eu tento o coração, mesmo para dar a cada homem de acordo com suas maneiras, de acordo com o fruto de seus atos”.
11 Kamar makwarwar da ta kwanta a kan ƙwan da ba ita ta zuba ba haka yake da mutumin da ya sami arziki a hanyar da ba daidai ba. A tsakiyar rayuwarsa za su rabu da shi, a ƙarshe kuma zai zama wawa.
Como a perdiz que fica sobre ovos que ela não pôs, assim é aquele que enriquece, e não por direito. No meio de seus dias, eles o deixarão. Em seu final, ele será um tolo.
12 Kursiyi mai daraja, da aka ɗaukaka tun daga farko, shi ne wuri mai tsarkinmu.
A trono glorioso, erguido no alto desde o início, é o lugar de nosso santuário.
13 Ya Ubangiji, sa zuciyar Isra’ila, duk waɗanda suka rabu da kai za su sha kunya. Waɗanda suka juya maka baya za a rubuta su a ƙura domin sun yashe Ubangiji, maɓulɓular ruwan rai.
Yahweh, a esperança de Israel, todos aqueles que o abandonarem ficarão desapontados. Aqueles que se afastarem de mim serão escritos na terra, porque eles abandonaram Yahweh, a fonte das águas vivas.
14 Ka warkar da ni, ya Ubangiji, zan kuwa warke; ka cece ni zan kuwa cetu, gama kai ne nake yabo.
Cura-me, ó Yahweh, e eu serei curado. Salve-me, e eu serei salvo; pois vocês são meus elogios.
15 Sun riƙa ce mini, “Ina maganar Ubangiji take? Bari tă cika yanzu!”
Veja, eles me perguntam, “Onde está a palavra de Yahweh? Que seja cumprido agora”.
16 Ban gudu zaman mai yin maka kiwo ba; ka sani ban marmarin ranan nan ta masifa ba. Abin da ya fito daga leɓunana kuwa, a bayyane suke gare ka.
Quanto a mim, não tenho pressa de ser pastor depois de você. Eu não desejei o dia lamentável. Você sabe. O que saiu dos meus lábios foi antes do seu rosto.
17 Kada ka zama mini abin razana; kai ne mafakata a ranar masifa.
Não seja um terror para mim. Você é meu refúgio no dia do mal.
18 Bari masu tsananta mini su sha kunya, amma ka kiyaye ni daga shan kunya; bari su tsorata, amma ka kiyaye ni da razana. Ka kawo musu ranar masifa; ka hallaka su da hallaka riɓi biyu.
Que fiquem desapontados com quem me persegue, mas não me deixe decepcionado. Que fiquem consternados, mas não me deixem ficar consternado. Traga neles o dia do mal, e destruí-los com dupla destruição.
19 Ga abin da Ubangiji ya ce mini, “Ka je ka tsaya a ƙofar mutane, inda sarakunan Yahuda sukan shiga su fita; ka tsaya kuma a dukan sauran ƙofofin Urushalima.
Yahweh me disse isto: “Vá e fique no portão dos filhos do povo, pelo qual entram e saem os reis de Judá, e em todos os portões de Jerusalém.
20 Ka ce musu, ‘Ku ji maganar Ubangiji, ku sarakunan Yahuda, da dukan mutanen Yahuda da dukan mazaunan Urushalima waɗanda suke bi ta waɗannan ƙofofi.
Diga-lhes: 'Ouçam a palavra de Javé, vocês reis de Judá, todo Judá e todos os habitantes de Jerusalém, que entram por estes portões':
21 Ga abin da Ubangiji yana cewa, ku yi hankali kada ku ɗauki kaya a ranar Asabbaci ko ku shigar da shi ta ƙofofin Urushalima.
Yahweh diz: “Tenham cuidado e não carreguem nenhuma carga no dia de sábado, nem a tragam pelos portões de Jerusalém”.
22 Kada ku fitar da kayan gidajenku ko ku yi wani aiki a ranar Asabbaci mai tsarki, yadda na umarci kakanni-kakanninku.
Não carreguem um fardo para fora de suas casas no dia de sábado. Não façam nenhum trabalho, mas tornem o Sábado sagrado, como ordenei a seus pais.
23 Duk da haka ba su saurara ba, ba su kuwa mai da hankali ba; suka taurare ba su kuwa saurara ko su karɓi horo ba.
Mas eles não ouviram. Eles não viraram o ouvido, mas endureceram o pescoço, para que não ouvissem, e talvez não recebessem instruções.
24 Amma in kuka yi hankali kuka yi mini biyayya, in ji Ubangiji, ba ku kuwa shigar da kaya ta ƙofofi a ranar Asabbaci ba, amma kuka kiyaye ranar Asabbaci da tsarki ba tare da yin wani aiki a cikinta ba,
Acontecerá, se vocês diligentemente me escutarem”, diz Javé, “para não trazer nenhuma carga através dos portões desta cidade no dia de sábado, mas para tornar o dia de sábado santo, para não fazer nenhum trabalho nele;
25 sa’an nan sarakuna da suke zama a kursiyin Dawuda za su shiga ta ƙofofin wannan birni tare da fadawansu. Su da fadawansu za su shiga a kan kekunan yaƙi da kuma a kan dawakai, mutanen Yahuda suna musu rakiya tare da waɗanda suke zaune a Urushalima, wannan birni kuwa za tă kasance da mazauna har abada.
então entrarão pelos portões desta cidade reis e príncipes sentados no trono de Davi, cavalgando em carros e em cavalos, eles e seus príncipes, os homens de Judá e os habitantes de Jerusalém; e esta cidade permanecerá para sempre.
26 Mutane za su zo daga garuruwan Yahuda da ƙauyukan kewaye da Urushalima, daga iyakar Benyamin da gindin tuddan yamma, daga ƙasar tudu da kuma Negeb, suna kawo hadayun ƙonawa da hadayun gari, sadakokin turare da na godiya zuwa gidan Ubangiji.
Eles virão das cidades de Judá, e dos lugares ao redor de Jerusalém, da terra de Benjamim, da planície, da região montanhosa, e do Sul, trazendo holocaustos, sacrifícios, ofertas de refeições e incenso, e trazendo sacrifícios de ação de graças para a casa de Iavé.
27 Amma in ba ku yi mini biyayya ba, ba ku kiyaye ranar Asabbaci da tsarki ba, kuka ɗauki wani kaya yayinda kuke shiga ƙofofin Urushalima a ranar Asabbaci, to, sai in cinna wa ƙofofin Urushalima wutar da ba a iya kashewa, tă cinye kagaranta.’”
Mas se vocês não me escutarem para santificar o Sábado, e não carregar um fardo e entrar às portas de Jerusalém no dia de sábado, então acenderei um fogo em suas portas, e ele devorará os palácios de Jerusalém. Não se apagará””.