< Irmiya 13 >
1 Ga abin da Ubangiji ya faɗa mini, “Tafi ka sayo abin ɗamara na lilin ka sha ɗamara da shi, amma kada ka bari yă taɓa ruwa.”
2 Saboda haka na sayo abin ɗamara, yadda Ubangiji ya umarce ni, na kuwa sha ɗamara da shi.
3 Sai maganar Ubangiji ta zo mini sau na biyu cewa,
4 “Ka ɗauki abin ɗamara da ka sayo, wanda ka ɗaura, ka tafi yanzu zuwa Fera ka ɓoye shi a cikin kogon dutse.”
5 Saboda haka na tafi na ɓoye shi a Fera, yadda Ubangiji ya ce mini.
6 Bayan’yan kwanaki sai Ubangiji ya ce mini, “Tafi yanzu zuwa Fera ka ɗauko abin ɗamara da na ce maka ka ɓoye a can.”
7 Sai na tafi Fera da haka na ɗauko abin ɗamara daga wurin da na ɓoye shi, amma abin ɗamara yanzu ya lalace ya zama ba shi da amfani sam.
8 Sai maganar Ubangiji ta zo mini cewa,
9 “Ga abin da Ubangiji yana cewa, ‘Haka zan lalatar da alfarmar Yahuda da yawan alfarmar Urushalima.
10 Waɗannan mugayen mutane, waɗanda suka ƙi saurari maganata, waɗanda suka biye wa taurin zuciyarsu suka bi waɗansu alloli don su bauta su kuma yi musu sujada, za su zama kamar wannan abin ɗamara gaba ɗaya marasa amfani!
11 Gama kamar yadda abin ɗamara kan kame gindin mutum tam, haka zan daure dukan gidan Isra’ila da dukan gidan Yahuda gare ni,’ in ji Ubangiji, ‘domin su zama jama’a, da suna, da yabo, da daraja a gare ni, amma sun ƙi ji.’
12 “Faɗa musu cewa, ‘Ga abin da Ubangiji, Allah na Isra’ila, yana cewa a cika kowace salkar ruwan inabi da ruwan inabi.’ In kuwa suka ce maka, ‘Ba mu san cewa ya kamata a cika kowace salkar ruwan inabi da ruwan inabi ba?’
13 Sai ka ce musu, ‘Ga abin da Ubangiji yana cewa, zan cika dukan waɗanda suke zama a ƙasar da buguwa, har ma da sarakunan da suke zama a kursiyin Dawuda, firistoci, annabawa da dukan waɗanda suke zaune a Urushalima.
14 Zan fyaɗe su a kan juna, iyaye da’ya’yansu maza, in ji Ubangiji. Tausayi ko jinƙai, ko juyayi ba zai hana ni hallaka su ba.’”
15 Ku ji ku kuma saurara, kada ku yi girman kai, gama Ubangiji ya yi magana.
16 Ku ɗaukaka Ubangiji Allahnku kafin ya kawo duhu, kafin ƙafafunku su yi tuntuɓe a kan tuddai masu duhu. Za ku sa zuciya ganin haske amma zai mai da shi duhu mai kauri ya kuma canja shi zuwa duhu baƙi ƙirin.
17 Amma in ba ku saurara ba, zan yi kuka a ɓoye saboda girmankanku; idanuna za su yi kuka mai zafi, suna zub da hawaye ƙwarai, domin zan kwashe garken Ubangiji zuwa zaman bauta.
18 Ka faɗa wa sarki da kuma mahaifiyar sarauniya cewa, “Ku sauko daga kursiyinku, gama rawaninku na ɗaukaka za su fāɗi daga kawunanku.”
19 Za a kulle biranen da suke a Negeb, kuma babu wanda zai buɗe su. Za a kwashe dukan Yahuda zuwa zaman bauta, za a kwashe su tas.
20 Ku tā da idanunku ku ga waɗanda suke zuwa daga arewa. Ina garken da aka ba ku tumakin da kuke taƙama a kai?
21 Me za ku ce sa’ad da Ubangiji ya naɗa muku waɗanda ku kanku kuka koya musu a matsayi abokai na musamman? Ashe, azaba ba za tă auko muku kamar na mace mai naƙuda ba?
22 In kuma kuka tambaye kanku “Me ya sa wannan ya faru da mu?” Wannan kuwa saboda yawan zunubanku ne ya sa fatarinku ya yage aka kuma wahalshe jikinku.
23 Mutumin Habasha zai iya canja launin fatar jikinsa ko damisa ta canja dabbare dabbarenta? Ba za ku iya yin alheri ku da kuka saba da yin mugunta ba.
24 “Zan watsar da ku kamar yayin da iskar hamada take hurawa.
25 Rabonku ne wannan, sashen da na auka muku,” in ji Ubangiji “domin kun manta da ni kuka kuma dogara ga allolin ƙarya.
26 Zan kware fatarinku sama ya rufe fuskarku don a iya ga tsiraicinku
27 zinace zinacenku da haniniya kamar dawakai, karuwancinku na bankunya! Na ga ayyukanku na banƙyama a kan tuddai da kuma a filaye. Kaitonki, ya Urushalima! Har yaushe za ki ci gaba da rashin tsarki?”