< Yaƙub 4 >
1 Me yake jawo faɗace-faɗace da gardandami a tsakaninku? Ashe, ba sha’awace-sha’awacenku da suke yaƙi a zukatanku ba ne?
Πόθεν πόλεμοι καὶ πόθεν μάχαι ἐν ὑμῖν; οὐκ ἐντεῦθεν, ἐκ τῶν ἡδονῶν ὑμῶν τῶν στρατευομένων ἐν τοῖς μέλεσιν ὑμῶν;
2 Kukan nemi abu ku rasa, sai ku yi kisa da ƙyashi. In kuka rasa abin da kuke nema sai ku shiga yin gardama da faɗa. Kukan rasa ne, domin ba ku roƙi Allah ba.
ἐπιθυμεῖτε, καὶ οὐκ ἔχετε· φονεύετε καὶ ζηλοῦτε, καὶ οὐ δύνασθε ἐπιτυχεῖν· μάχεσθε καὶ πολεμεῖτε. οὐκ ἔχετε διὰ τὸ μὴ αἰτεῖσθαι ὑμᾶς·
3 Sa’ad da kuka roƙa, ba kwa samu, don kun roƙa da mugun nufi, don ku kashe abin da kuka samu a kan sha’awace-sha’awacenku.
αἰτεῖτε, καὶ οὐ λαμβάνετε, διότι κακῶς αἰτεῖσθε, ἵνα ἐν ταῖς ἡδοναῖς ὑμῶν δαπανήσητε.
4 Ku mazinata, ba ku san cewa abokantaka da duniya gāba ce da Allah ba? Duk wanda ya zaɓa yă zama abokin duniya ya zama abokin gāban Allah ke nan.
μοιχαλίδες, οὐκ οἴδατε ὅτι ἡ φιλία τοῦ κόσμου ἔχθρα τοῦ θεοῦ ἐστιν; ὃς ἂν οὖν βουληθῇ φίλος εἶναι τοῦ κόσμου, ἐχθρὸς τοῦ θεοῦ καθίσταται.
5 Ko kuna tsammani a banza ne Nassi ya ce ruhun da ya sa yă zauna a cikinmu yana kishi sosai?
ἢ δοκεῖτε ὅτι κενῶς ἡ γραφὴ λέγει; πρὸς φθόνον ἐπιποθεῖ τὸ πνεῦμα ὃ κατῴκισεν ἐν ἡμῖν;
6 Amma yakan ba mu alheri a yalwace. Shi ya sa Nassi ya ce, “Allah yana gāba da masu girman kai amma yakan ba da alheri ga masu tawali’u.”
μείζονα δὲ δίδωσιν χάριν· διὸ λέγει, Ὁ θεὸς ὑπερηφάνοις ἀντιτάσσεται, ταπεινοῖς δὲ δίδωσιν χάριν.
7 Saboda haka, ku miƙa kanku ga Allah. Ku yi tsayayya da Iblis, zai kuwa guje ku.
Ὑποτάγητε οὖν τῷ θεῷ. ἀντίστητε δὲ τῷ διαβόλῳ καὶ φεύξεται ἀφ᾽ ὑμῶν,
8 Ku matso kusa da Allah shi kuwa zai matso kusa da ku. Ku wanke hannuwanku, ku masu zunubi, ku kuma tsarkake zukatanku, ku masu zuciya biyu.
ἐγγίσατε τῷ θεῷ καὶ ἐγγιεῖ ὑμῖν. καθαρίσατε χεῖρας, ἁμαρτωλοί, καὶ ἁγνίσατε καρδίας, δίψυχοι.
9 Ku yi baƙin ciki, ku yi makoki ku kuma yi kuka. Ku mai da dariyarku ta zama makoki, farin cikinku kuma yă zama ɓacin zuciya.
ταλαιπωρήσατε καὶ πενθήσατε καὶ κλαύσατε· ὁ γέλως ὑμῶν εἰς πένθος μεταστραφήτω, καὶ ἡ χαρὰ εἰς κατήφειαν.
10 Ku ƙasƙantar da kanku a gaban Ubangiji, zai kuwa ɗaukaka ku.
ταπεινώθητε ἐνώπιον κυρίου, καὶ ὑψώσει ὑμᾶς.
11 ’Yan’uwa, kada ku ɓata wa juna suna. Duk wanda ya zargi ɗan’uwansa ko ya ɗora masa laifi, yana gāba da doka ne yana kuma yin mata shari’a ke nan. In kuwa ka ɗora wa shari’a laifi, kai ba mai binta ba ne, mai ɗora mata laifi ne.
Μὴ καταλαλεῖτε ἀλλήλων, ἀδελφοί· ὁ καταλαλῶν ἀδελφοῦ, ἢ κρίνων τὸν ἀδελφὸν αὐτοῦ καταλαλεῖ νόμου καὶ κρίνει νόμον· εἰ δὲ νόμον κρίνεις, οὐκ εἶ ποιητὴς νόμου, ἀλλὰ κριτής.
12 Akwai Mai ba da doka da kuma Alƙali guda ɗaya tak, shi ne yake da ikon ceto da kuma hallakarwa. Amma kai, wane ne da za ka hukunta maƙwabcinka?
εἷς ἐστιν ὁ νομοθέτης καὶ κριτὴς ὁ δυνάμενος σῶσαι καὶ ἀπολέσαι· σὺ δὲ τίς εἶ ὁ κρίνων τὸν πλησίον;
13 Yanzu fa sai ku saurara, ku da kuke cewa, “Yau ko gobe za mu je wannan ko wancan birni, mu yi shekara a can, mu yi kasuwanci, mu ci riba.”
Ἄγε νῦν οἱ λέγοντες, Σήμερον ἢ αὔριον πορευσόμεθα εἰς τήνδε τὴν πόλιν, καὶ ποιήσωμεν ἐκεῖ ἐνιαυτόν, καὶ ἐμπορευσόμεθα καὶ κερδήσομεν·
14 Alhali kuwa ba ku ma san abin da zai faru gobe ba. Wane iri ne ranku? Ku kamar hazo ne da yake bayyana na ɗan lokaci sa’an nan yă ɓace.
οἵτινες οὐκ ἐπίστασθε τὸ τῆς αὔριον· ποία [γὰρ] ἡ ζωὴ ὑμῶν; ἀτμὶς γάρ ἐστε ἡ πρὸς ὀλίγον φαινομένη ἔπειτα καὶ ἀφανιζομένη·
15 A maimakon haka, ya kamata ku ce, “In Ubangiji ya yarda, muna kuma a raye, za mu yi wannan ko wancan.”
ἀντὶ τοῦ λέγειν ὑμᾶς, Ἐὰν ὁ κύριος θελήσῃ καὶ ζήσομεν, καὶ ποιήσομεν τοῦτο ἢ ἐκεῖνο.
16 Ga shi, kuna fariya da taƙama. Duk irin wannan taƙama mugun abu ne.
νῦν δὲ καυχᾶσθε ἐν ταῖς ἀλαζονείαις ὑμῶν· πᾶσα καύχησις τοιαύτη πονηρά ἐστιν.
17 Saboda haka, duk wanda ya san abu mai kyan da ya kamata yă yi, bai kuwa yi ba, ya yi zunubi ke nan.
εἰδότι οὖν καλὸν ποιεῖν καὶ μὴ ποιοῦντι, ἁμαρτία αὐτῷ ἐστιν.