< Yaƙub 3 >
1 Kada yawancinku su so ɗaukan kansu a matsayin malamai,’yan’uwana, domin kun san cewa mu da muke koyarwa za a yi mana shari’a mafi tsanani.
2 Dukanmu mukan yi tuntuɓe a hanyoyi dabam-dabam. In wani bai taɓa yin kuskure a cikin maganarsa ba, shi cikakke ne, yana kuma iya ƙame dukan jikinsa.
3 Sa’ad da muka sa linzamai a bakunan dawakai don mu sa su yi mana biyayya, mukan iya bin da dabbar gaba ɗaya.
4 Ko kuwa misali, mu dubi jiragen ruwa, mana. Ko da yake suna da girma ƙwarai kuma iska mai ƙarfi ce take tura su, ana tuƙa su da ɗan ƙaramin sandan ƙarfe ne zuwa duk inda mai tuƙin jirgin yake so.
5 Haka ma harshe yake, ga shi ɗan ƙanƙanin gaɓar jiki ne, amma sai manyan fariya. Ku dubi yadda ɗan ƙaramin ƙyastu yake ƙuna wa babban jeji wuta mana.
6 Harshe ma wuta ne! A cikin duk gaɓoɓinmu, harshe shi ne tushen kowace irin mugunta, mai ɓata mutum gaba ɗaya, mai zuga zuciyar mutum ta tafasa, shi kuwa jahannama ce take zuga shi. (Geenna )
7 Kowace irin dabba, tsuntsu, masu ja da ciki da kuma halittun da suke cikin teku an sarrafa su kuma mutum ne ya sarrafa,
8 amma ba mutumin da zai iya ya sarrafa harshe. Mugu ne marar hutu, cike da dafi mai kisa.
9 Da harshe mukan yabi Ubangijinmu da kuma Ubanmu, da shi kuma muke la’antar mutane, waɗanda aka halitta a kamannin Allah.
10 Daga wannan baki guda yabo da la’ana suke fitowa.’Yan’uwana, wannan bai kamata yă zama haka ba.
11 Ruwa mai kyau da kuma ruwan gishiri zai iya fito daga maɓulɓula ɗaya?
12 ’Yan’uwana, itacen ɓaure yana iya haifar’ya’yan zaitun, ko kuma itacen inabi yă haifi’ya’yan ɓaure? Haka ma, maɓulɓular ruwan gishiri ba zai iya ba da ruwa mai kyau ba.
13 Wane ne mai hikima da fahimta a cikinku? Bari yă nuna ta ta wurin rayuwarsa mai kyau, ta wurin ayyukan da aka yi cikin tawali’un da suke fitowa daga hikima.
14 Amma in kuna cike da mugun kishi da kuma sonkai a cikin zukatanku, kada ku yi taƙama game da wannan, ko ku danne gaskiya.
15 Irin wannan “hikima” ba daga sama ta sauko ba, ta duniya ce, ta rashin ruhaniya, ta Iblis kuma.
16 Gama inda akwai kishi da sonkai, a can za a tarar da hargitsi da kowane irin mugun aiki.
17 Amma hikimar da ta zo daga sama da fari tana da tsabta gaba ɗaya; sa’an nan mai ƙaunar salama ce, mai sanin ya kamata, mai biyayya, cike da jinƙai da aiki mai kyau, marar nuna bambanci, sahihiya kuma.
18 Masu salama da suke shuki cikin salama sukan girbe adalci.