< Yaƙub 2 >

1 ’Yan’uwana, a matsayinmu cikin Ubangiji Yesu Kiristi maɗaukaki, kada ku nuna bambanci.
My brothers, don’t hold the faith of our glorious Lord Jesus Christ with partiality.
2 A ce wani ya shigo cikin taronku saye da zoben zinariya da riguna masu tsada, wani matalauci kuma saye da tsummoki shi ma ya shigo,
For if a man with a gold ring, in fine clothing, comes into your synagogue, and a poor man in filthy clothing also comes in,
3 in kuka mai da hankali na musamman ga mutumin da yake da riguna masu tsadan nan kuka kuma ce, “Ga wurin zama mai kyau dominka,” amma kuka ce wa matalaucin nan, “Kai tsaya daga can,” ko kuwa, “Ka zauna a ƙasa kusa da ƙafafuna,”
and you pay special attention to him who wears the fine clothing and say, “Sit here in a good place;” and you tell the poor man, “Stand there,” or “Sit by my footstool”
4 ashe, ba ku nuna bambanci a tsakaninku ke nan ba, kuka kuma zama alƙalai masu mugayen tunani?
haven’t you shown partiality among yourselves, and become judges with evil thoughts?
5 Ku saurara,’yan’uwana ƙaunatattu. Ashe, Allah bai zaɓi waɗanda suke matalauta a idon duniya don su zama masu wadata cikin bangaskiya, su kuma gāji mulkin da ya yi wa masu ƙaunarsa alkawari ba?
Listen, my beloved brothers. Didn’t God choose those who are poor in this world to be rich in faith and heirs of the Kingdom which he promised to those who love him?
6 Ga shi kun wulaƙanta matalauta. Ashe, ba masu arziki ne suke cutarku ba? Ba su ba ne suke jan ku zuwa kotu?
But you have dishonored the poor man. Don’t the rich oppress you and personally drag you before the courts?
7 Ba su ba ne suke ɓata sunan nan mai martaba wanda aka san ku da shi ba?
Don’t they blaspheme the honorable name by which you are called?
8 In fa kun kiyaye dokan nan ta mulki wadda take cikin Nassi mai cewa, “Ƙaunaci maƙwabcinka kamar kanka,” kun yi daidai.
However, if you fulfill the royal law according to the Scripture, “You shall love your neighbor as yourself,” you do well.
9 Amma in kuka nuna bambanci, kun yi zunubi ke nan shari’a kuma ta same ku da laifi a matsayin masu karya doka.
But if you show partiality, you commit sin, being convicted by the law as transgressors.
10 Gama duk wanda ya kiyaye dukan doka amma ya yi tuntuɓe a kan abu ɗaya kaɗai, ya zama mai laifin karya dukansu ke nan.
For whoever keeps the whole law, and yet stumbles in one point, he has become guilty of all.
11 Gama shi da ya ce, “Kada ka yi zina,” shi ne kuma ya ce, “Kada ka yi kisankai.” In kuwa ba ka zina amma kana kisankai, ka zama mai karya doka ke nan.
For he who said, “Do not commit adultery,” also said, “Do not commit murder.” Now if you do not commit adultery but do murder, you have become a transgressor of the law.
12 Ku yi magana ku kuma yi aiki kamar waɗanda za a yi musu shari’a bisa ga doka mai ba da’yanci,
So speak and so do as men who are to be judged by the law of freedom.
13 gama za a yi wa duk wanda bai nuna jinƙai ba hukunci babu jinƙai. Jinƙai yakan yi nasara a kan hukunci!
For judgment is without mercy to him who has shown no mercy. Mercy triumphs over judgment.
14 Wanda amfani ne,’yan’uwana, a ce wani yă ce yana da bangaskiya, amma ba shi da ayyuka? Anya, wannan bangaskiya za tă iya cetonsa kuwa?
What good is it, my brothers, if a man says he has faith, but has no works? Can faith save him?
15 A ce wani ɗan’uwa ko’yar’uwa ba shi da riguna ko abincin yini,
And if a brother or sister is naked and in lack of daily food,
16 sai waninku yă ce masa, “Sauka lafiya, Allah ya ba da ci da sha da kuma sutura,” amma bai yi wani abu game da bukatunsa na jiki ba, ina amfani?
and one of you tells them, “Go in peace. Be warmed and filled;” yet you didn’t give them the things the body needs, what good is it?
17 Haka ma bangaskiya ita kaɗai, in ba tare da ayyuka ba, matacciya ce.
Even so faith, if it has no works, is dead in itself.
18 Amma wani zai ce, “Kai kana da bangaskiya; ni kuma ina da ayyuka.” Ka nuna mini bangaskiyarka ba tare da ayyuka ba, ni kuma zan nuna maka bangaskiyata ta wurin abin da nake yi.
Yes, a man will say, “You have faith, and I have works.” Show me your faith without works, and I will show you my faith by my works.
19 Ka gaskata cewa Allah ɗaya ne. To, da kyau! Ai, ko aljanu ma sun gaskata wannan, har da rawan jiki.
You believe that God is one. You do well. The demons also believe—and shudder.
20 Kai wawa, kana son tabbaci cewa bangaskiya marar ayyuka banza ce?
But do you want to know, vain man, that faith apart from works is dead?
21 Ashe, ba a mai da kakanmu Ibrahim mai adalci saboda abin da ya yi ba ne sa’ad da ya miƙa ɗansa Ishaku a bisa bagade?
Wasn’t Abraham our father justified by works, in that he offered up Isaac his son on the altar?
22 Ai, ka gani cewa bangaskiyarsa da ayyukansa sun yi aiki tare, bangaskiyarsa kuma ta zama cikakkiya ta wurin abin da ya yi.
You see that faith worked with his works, and by works faith was perfected.
23 Aka kuma cika nassin nan da ya ce, “Ibrahim ya gaskata Allah, aka kuma lissafta wannan adalci ne gare shi,” aka kuma ce da shi abokin Allah.
So the Scripture was fulfilled which says, “Abraham believed God, and it was accounted to him as righteousness,” and he was called the friend of God.
24 Kun ga cewa ashe mutum zai sami kuɓuta ta wurin abin da ya yi ne ba ta wurin bangaskiya kaɗai ba.
You see then that by works a man is justified, and not only by faith.
25 Ta haka kuma ashe, Rahab karuwan nan ba a ɗauke ta mai adalci ce saboda abin da ta yi ba ne sa’ad da ta ba wa’yan leƙen asirin nan masauƙi ta kuma sallame su suka tafi ta wata hanya dabam?
In the same way, wasn’t Rahab the prostitute also justified by works when she received the messengers and sent them out another way?
26 Kamar yadda jikin da babu ruhu matacce ne, haka ma bangaskiyar da babu ayyuka matacciya ce.
For as the body apart from the spirit is dead, even so faith apart from works is dead.

< Yaƙub 2 >