< Ishaya 8 >

1 Ubangiji ya ce mini, “Ka ɗauki naɗaɗɗen littafi mai girma ka yi rubutu a kai da alƙalami kurum, Maher-Shalal-Hash-Baz.
Then the LORD said to me, “Take a large scroll and write on it with an ordinary stylus: Maher-shalal-hash-baz.
2 Zan kuma kira Uriya firist da Zakariya ɗan Yeberekiya su zama mini amintattun shaidu.”
And I will appoint for Myself trustworthy witnesses—Uriah the priest and Zechariah son of Jeberekiah.”
3 Sa’an nan na tafi na yi jima’i da annabiya, ta kuwa yi ciki ta haifi ɗa. Ubangiji kuma ya ce mini, “Raɗa masa suna, Maher-Shalal-Hash-Baz.
And I had relations with the prophetess, and she conceived and gave birth to a son. The LORD said to me, “Name him Maher-shalal-hash-baz.
4 Kafin yaron yă san yadda zai ce ‘Babana’ ko ‘Mamana,’ sarkin Assuriya zai kwashe arzikin Damaskus da ganimar Samariya.”
For before the boy knows how to cry ‘Father’ or ‘Mother,’ the wealth of Damascus and the plunder of Samaria will be carried off by the king of Assyria.”
5 Ubangiji ya sāke yi mini magana ya ce,
And the LORD spoke to me further:
6 “Domin wannan jama’a ta ƙi natsattsen ruwan rafin Shilowa suka yi ta farin ciki a kan Rezin ɗan Remaliya,
“Because this people has rejected the gently flowing waters of Shiloah and rejoiced in Rezin and the son of Remaliah,
7 saboda haka Ubangiji yana shirin yă kawo musu rigyawar ruwan Kogi, wato, sarkin Assuriya da dukan sojojinsa. Zai cika dukan gaɓoɓinsa, yă kuma malala har zuwa bakin kogi.
the Lord will surely bring against them the mighty floodwaters of the Euphrates — the king of Assyria and all his pomp. It will overflow its channels and overrun its banks.
8 Yă yi ta malala har zuwa cikin Yahuda, yă shafe ta, yana ratsa ta ciki har yă kai kafaɗa. Fikafikansa da ya buɗe za su rufe fāɗin ƙasarka, Ya Immanuwel!”
It will pour into Judah, swirling and sweeping over it, reaching up to the neck; its spreading streams will cover your entire land, O Immanuel!
9 Ku yi kururuwar yaƙi, ku ƙasashe, ku kuma ji tsoro! Ku saurara, dukanku manisantan ƙasashe. Ku shirya don yaƙi, ku kuma ji tsoro!
Huddle together, O peoples, and be shattered; pay attention, all you distant lands; prepare for battle, and be shattered; prepare for battle, and be shattered!
10 Ku ƙirƙiro dabarunku, amma ba za su yi nasara ba; ku ƙulla shirye-shiryenku, amma ba za su yi amfani ba, gama Allah yana tare da mu.
Devise a plan, but it will be thwarted; state a proposal, but it will not happen. For God is with us.”
11 Ubangiji ya yi mini magana da hannunsa mai ƙarfi a kaina, yana yi mini gargaɗi kada in bi hanyar waɗannan mutane. Ya ce,
For this is what the LORD has spoken to me with a strong hand, instructing me not to walk in the way of this people:
12 “Kada ka kira wani abu makirci game da kome da waɗannan mutane suke kira makirci; kada ji tsoron abin da suke tsoro, kada kuma ka firgita game da shi.
“Do not call conspiracy everything these people regard as conspiracy. Do not fear what they fear; do not live in dread.
13 Ubangiji Maɗaukaki shi ne za ka ɗauka a matsayi mai tsarki, shi ne wanda za ka ji tsoro, shi ne za ka yi rawar jiki a gabansa,
The LORD of Hosts is the One you shall regard as holy. Only He should be feared; only He should be dreaded.
14 zai kuwa kasance a wuri mai tsarki; amma ga dukan gidajen Isra’ila zai zama dutsen da zai sa mutane su yi tuntuɓe dutse kuma da zai sa su fāɗi. Ga dukan mutanen Urushalima kuma zai zama tarko da raga.
And He will be a sanctuary— but to both houses of Israel a stone of stumbling and a rock of offense, to the dwellers of Jerusalem a trap and a snare.
15 Yawancinsu za su yi tuntuɓe; za su fāɗi a kuwa ragargaza su, za a sa musu tarko a kuma kama su.”
Many will stumble over these; they will fall and be broken; they will be ensnared and captured.”
16 Ɗaura shaidar nan ta gargadi ka kuma yimƙe umarnin Allah a cikin almajiraina.
Bind up the testimony and seal the law among my disciples.
17 Zan saurari Ubangiji, wanda ya ɓoye fuskarsa daga gidan Yaƙub. Zan dogara gare shi.
I will wait for the LORD, who is hiding His face from the house of Jacob. I will put my trust in Him.
18 Ga ni, da yaran da Ubangiji ya ba ni. Mu alamu ne da shaidu a cikin Isra’ila daga Ubangiji Maɗaukaki, wanda yake zama a Dutsen Sihiyona.
Here am I, and the children the LORD has given me as signs and symbols in Israel from the LORD of Hosts, who dwells on Mount Zion.
19 Sa’ad da mutane suka ce muku ku nemi shawarar’yan bori da masu sihiri, waɗanda suke shaƙe murya har ba a jin abin da suke faɗi, bai kamata mutane su nemi shawara daga Allahnsu ba? Me zai sa ku nemi shawara daga matattu a madadin masu rai?
When men tell you to consult the spirits of the dead and the spiritists who whisper and mutter, shouldn’t a people consult their God instead? Why consult the dead on behalf of the living?
20 Nemi umarnin Allah da kuma shaidar jan kunne. Duk wanda bai yi magana bisa ga wannan kalma ba, ba su da amfani.
To the law and to the testimony! If they do not speak according to this word, they have no light of dawn.
21 Cikin matsuwa da yunwa, za su yi ta kai komo ko’ina a ƙasar; sa’ad da suka ji yunwa, za su yi fushi su tā da idanu sama, su zagi sarkinsu da Allahnsu.
They will roam the land, dejected and hungry. When they are famished, they will become enraged; and looking upward, they will curse their king and their God.
22 Sa’an nan za su zura wa ƙasa idanu, abin da za su gani kawai shi ne matsuwa da duhu da kuma abin banrazana, za a kuma jefa su cikin baƙin duhu.
Then they will look to the earth and see only distress and darkness and the gloom of anguish. And they will be driven into utter darkness.

< Ishaya 8 >