< Ishaya 7 >

1 Sa’ad da Ahaz ɗan Yotam, ɗan Uzziya, yake sarkin Yahuda, Sarki Rezin na Aram da Feka ɗan Remaliya sarkin Isra’ila suka haura don su yaƙi Urushalima, amma ba su iya cinta da yaƙi ba.
Now in the days that Ahaz son of Jotham, the son of Uzziah, was king of Judah, Rezin king of Aram marched up to wage war against Jerusalem. He was accompanied by Pekah son of Remaliah the king of Israel, but he could not overpower the city.
2 Sai fa aka faɗa wa gidan Dawuda cewa, “Aram ya haɗa kansa da Efraim”; saboda haka zuciyar Ahaz da ta mutanensa suka firgita, sai ka ce itatuwa a kurmin da iska ta girgiza.
When it was reported to the house of David that Aram was in league with Ephraim, the hearts of Ahaz and his people trembled like trees in the forest shaken by the wind.
3 Sai Ubangiji ya ce wa Ishaya, “Fita, kai da ɗanka Sheyar-Yashub, don ku sadu da Ahaz a ƙarshen wuriyar da take kawo ruwa daga Tafkin Tudu, a hanyar Filin Mai Wanki.
Then the LORD said to Isaiah, “Go out with your son Shear-jashub to meet Ahaz at the end of the aqueduct that feeds the upper pool, on the road to the Launderer’s Field,
4 Ka faɗa masa, ‘Ka yi hankali, ka natsu kada kuma ka ji tsoro ko ka damu, kada ka ji tsoron fushin sarki Rezin da na Aram da na ɗan Remaliya, ba wani abu mai hatsari ba ne, bai fi hayaƙin’yan ƙirare biyu da suke cin wuta ba.
and say to him: Calm down and be quiet. Do not be afraid or disheartened over these two smoldering stubs of firewood—over the fierce anger of Rezin and Aram and of the son of Remaliah.
5 Aram, Efraim da ɗan Remaliya sun ƙulla maƙarƙashiya, suna cewa,
For Aram, along with Ephraim and the son of Remaliah, has plotted your ruin, saying:
6 “Bari mu kai wa Yahuda hari; bari mu yayyage su mu rarraba su a tsakaninmu, mu naɗa Tabeyel sarki a kansu.”
‘Let us invade Judah, terrorize it, and divide it among ourselves. Then we can install the son of Tabeal over it as king.’
7 Duk da haka ga abin da Ubangiji Mai Iko Duka ya ce, “‘Ba zai faru ba, ba zai auku ba,
But this is what the Lord GOD says: ‘It will not arise; it will not happen.
8 gama kan Aram shi ne Damaskus, kan Damaskus kuma kawai shi ne Rezin. Cikin shekaru sittin da biyar za a wargaje Efraim har ba za tă iya rayuwa ta zama al’umma ba.
For the head of Aram is Damascus, and the head of Damascus is Rezin. Within sixty-five years Ephraim will be shattered as a people.
9 Kan Efraim shi ne Samariya, kan Samariya kuma kawai shi ne ɗan Remaliya. In ba ku tsaya da ƙarfi cikin bangaskiyarku ba, ba za ku dawwama ba.’”
The head of Ephraim is Samaria, and the head of Samaria is the son of Remaliah. If you do not stand firm in your faith, then you will not stand at all.’”
10 Ubangiji ya kuma yi magana wa Ahaz ya ce,
Again the LORD spoke to Ahaz, saying,
11 “Ka roƙi Ubangiji Allahnka yă ba ka alama, ko daga zurfafa masu zurfi ko kuwa daga can cikin sama.” (Sheol h7585)
“Ask for a sign from the LORD your God, whether from the depths of Sheol or the heights of heaven.” (Sheol h7585)
12 Amma Ahaz ya ce, “Ba zan nema ba; ba zan gwada Ubangiji ba.”
But Ahaz replied, “I will not ask; I will not test the LORD.”
13 Sa’an nan Ishaya ya ce, “To, ku saurara, ya ku gidan Dawuda! Abin kirki kuke yi ne da kuka ƙure haƙurin jama’a? Ko haƙurin Allah ne kuma kuke so ku ƙure?
Then Isaiah said, “Hear now, O house of David! Is it not enough to try the patience of men? Will you try the patience of my God as well?
14 Saboda haka Ubangiji kansa zai ba ku alama. Ga shi budurwa za tă yi ciki, za tă haifi ɗa, za tă kuwa kira shi Immanuwel.
Therefore the Lord Himself will give you a sign: Behold, the virgin will be with child and will give birth to a son, and will call Him Immanuel.
15 In ya yi girma har ya isa yanke shawara don kansa, madara da zuma ne abincinsa.
By the time He knows enough to reject evil and choose good, He will be eating curds and honey.
16 Amma kafin yaron yă isa yanke shawara yă ƙi abin da yake mummuna, yă zaɓi abin da yake nagari, ƙasashen sarakunan nan biyu da kuke tsoro za su zama kango.
For before the boy knows enough to reject evil and choose good, the land of the two kings you dread will be laid waste.
17 Ubangiji zai aukar maka da kwanakin wahala, kai da jama’arka, da dukan iyalin gidan sarauta, waɗanda suka fi muni tun lokacin da aka raba mulkin Efraim daga na Yahuda, zai kawo sarkin Assuriya.”
The LORD will bring on you and on your people and on the house of your father a time unlike any since the day Ephraim separated from Judah—He will bring the king of Assyria.”
18 A wannan rana Ubangiji zai yi feɗuwa yă kira ƙudaje daga rafuffuka masu nisa na Masar da kuma ƙudan zuma daga ƙasar Assuriya.
On that day the LORD will whistle to the flies at the farthest streams of the Nile and to the bees in the land of Assyria.
19 Za su zo su mamaye kwazazzabai da kogwanni cikin duwatsu, a kan dukan ƙayayyuwa da dukan rammukan ruwa.
And they will all come and settle in the steep ravines and clefts of the rocks, in all the thornbushes and watering holes.
20 A wannan rana Ubangiji zai yi amfani da rezan da aka yi haya daga ƙetaren Kogi, sarkin Assuriya ke nan, yă aske kanku da gashin ƙafafunku, zai kuma aske gemunku.
On that day the Lord will use a razor hired from beyond the Euphrates —the king of Assyria—to shave your head and the hair of your legs, and to remove your beard as well.
21 A ranar, mutum zai bar karsana ɗaya da awaki biyu da rai.
On that day a man will raise a young cow and two sheep,
22 Kuma saboda yalwa madarar da suke bayarwa, zai kasance da madarar da zai sha. Dukan waɗanda suka rage a ƙasar za su sha madara da zuma.
and from the abundance of milk they give, he will eat curds; for all who remain in the land will eat curds and honey.
23 A wannan rana, a kowane wuri inda akwai kuringa dubu da kuɗinsu ya kai shekel dubu na azurfa, ƙayayyuwa da sarƙaƙƙiya ne kawai za su kasance a can.
And on that day, in every place that had a thousand vines worth a thousand shekels of silver, only briers and thorns will be found.
24 Mutane za su je can da baka da kibiyoyi, gama ƙayayyuwa da sarƙaƙƙiya ne za su rufe ƙasar.
Men will go there with bow and arrow, for the land will be covered with briers and thorns.
25 Game da dukan tuddai da dā ake nome da garemani kuwa, ba za ku ƙara je wurin ba saboda tsoron ƙayayyuwa da sarƙaƙƙiya; za su zama wuraren da ake kai shanu a sake su su yi ta yawo da kansu, tumaki kuma su yi ta gudu.
For fear of the briers and thorns, you will no longer traverse the hills once tilled by the hoe; they will become places for oxen to graze and sheep to trample.

< Ishaya 7 >