< Ishaya 66 >

1 Ga abin da Ubangiji yana cewa, “Sama kursiyina ce, duniya kuma matashin sawuna. Ina gidan da za ku gina mini? Ina wurin hutuna zai kasance?
כֹּ֚ה אָמַ֣ר יְהוָ֔ה הַשָּׁמַ֣יִם כִּסְאִ֔י וְהָאָ֖רֶץ הֲדֹ֣ם רַגְלָ֑י אֵי־זֶ֥ה בַ֙יִת֙ אֲשֶׁ֣ר תִּבְנוּ־לִ֔י וְאֵי־זֶ֥ה מָק֖וֹם מְנוּחָתִֽי׃
2 Ba hannuna ba ne ya yi dukan waɗannan abubuwa, ta haka suka kasance?” In ji Ubangiji. “Wannan mutum ne nake jin daɗi, shi da yake mai ƙasƙanci da kuma zuciyar yin tuba, yana kuma rawar jiki ga maganata.
וְאֶת־כָּל־אֵ֙לֶּה֙ יָדִ֣י עָשָׂ֔תָה וַיִּהְי֥וּ כָל־אֵ֖לֶּה נְאֻם־יְהוָ֑ה וְאֶל־זֶ֣ה אַבִּ֔יט אֶל־עָנִי֙ וּנְכֵה־ר֔וּחַ וְחָרֵ֖ד עַל־דְּבָרִֽי׃
3 Amma duk ya miƙa hadayar bijimi yana kama da wanda ya kashe mutum, kuma duk wanda ya miƙa ɗan rago, kamar wanda ya karye wuyan kare; duk wanda ya miƙa hadaya ta gari yana kama da wanda ya yi sadakar jinin alade, kuma duk wanda ya ƙone turaren tuni, kamar wanda yake bauta gunki ne. Sun zaɓi hanyoyinsu, rayukansu kuma suna jin daɗin abubuwan banƙyamarsu;
שׁוֹחֵ֨ט הַשּׁ֜וֹר מַכֵּה־אִ֗ישׁ זוֹבֵ֤חַ הַשֶּׂה֙ עֹ֣רֵֽף כֶּ֔לֶב מַעֲלֵ֤ה מִנְחָה֙ דַּם־חֲזִ֔יר מַזְכִּ֥יר לְבֹנָ֖ה מְבָ֣רֵֽךְ אָ֑וֶן גַּם־הֵ֗מָּה בָּֽחֲרוּ֙ בְּדַרְכֵיהֶ֔ם וּבְשִׁקּוּצֵיהֶ֖ם נַפְשָׁ֥ם חָפֵֽצָה׃
4 saboda haka ni ma zan aukar musu da masifa mai zafi in kuma kawo musu abin da suke tsoro. Gama sa’ad da na yi kira, ba wanda ya amsa, sa’ad da na yi magana, ba wanda ya saurara, Sun aikata mugunta a idona suka kuma zaɓa abin da ba na jin daɗi.”
גַּם־אֲנִ֞י אֶבְחַ֣ר בְּתַעֲלֻלֵיהֶ֗ם וּמְגֽוּרֹתָם֙ אָבִ֣יא לָהֶ֔ם יַ֤עַן קָרָ֙אתִי֙ וְאֵ֣ין עוֹנֶ֔ה דִּבַּ֖רְתִּי וְלֹ֣א שָׁמֵ֑עוּ וַיַּעֲשׂ֤וּ הָרַע֙ בְּעֵינַ֔י וּבַאֲשֶׁ֥ר לֹֽא־חָפַ֖צְתִּי בָּחָֽרוּ׃ ס
5 Ku ji maganar Ubangiji, ku da kuke rawar jiki ga maganarsa, “’Yan’uwanku da suke ƙinku, suna kuma ware ku saboda sunana, sun ce, ‘Bari a ɗaukaka Ubangiji, don mu ga farin cikinku!’ Duk da haka za su sha kunya.
שִׁמְעוּ֙ דְּבַר־יְהוָ֔ה הַחֲרֵדִ֖ים אֶל־דְּבָר֑וֹ אָמְרוּ֩ אֲחֵיכֶ֨ם שֹׂנְאֵיכֶ֜ם מְנַדֵּיכֶ֗ם לְמַ֤עַן שְׁמִי֙ יִכְבַּ֣ד יְהוָ֔ה וְנִרְאֶ֥ה בְשִׂמְחַתְכֶ֖ם וְהֵ֥ם יֵבֹֽשׁוּ׃
6 Ku ji wannan hayaniya daga birni, ku ji surutu daga haikali! Amon Ubangiji ne yana sāka wa abokan gābansa abin da ya dace da su.
ק֤וֹל שָׁאוֹן֙ מֵעִ֔יר ק֖וֹל מֵֽהֵיכָ֑ל ק֣וֹל יְהוָ֔ה מְשַׁלֵּ֥ם גְּמ֖וּל לְאֹיְבָֽיו׃
7 “Kafin naƙuda ya fara mata, ta haihu; kafin zafi ya zo mata, ta haifi ɗa.
בְּטֶ֥רֶם תָּחִ֖יל יָלָ֑דָה בְּטֶ֨רֶם יָב֥וֹא חֵ֛בֶל לָ֖הּ וְהִמְלִ֥יטָה זָכָֽר׃
8 Wa ya taɓa jin irin wannan abu? Wa ya taɓa gani irin abubuwan nan? Za a iya ƙirƙiro ƙasa a rana ɗaya ko a haifi al’umma farat ɗaya? Duk da haka da zarar Sihiyona ta fara naƙuda sai ta haifi’ya’yanta.
מִֽי־שָׁמַ֣ע כָּזֹ֗את מִ֤י רָאָה֙ כָּאֵ֔לֶּה הֲי֤וּחַל אֶ֙רֶץ֙ בְּי֣וֹם אֶחָ֔ד אִם־יִוָּ֥לֵֽד גּ֖וֹי פַּ֣עַם אֶחָ֑ת כִּֽי־חָ֛לָה גַּם־יָלְדָ֥ה צִיּ֖וֹן אֶת־בָּנֶֽיהָ׃
9 Zan kai mace har haihuwa in kuma sa ta kāsa haihu?” In ji Ubangiji. “Zan rufe mahaihuwa sa’ad da lokacin haihuwa ya yi?” In ji Allahnku.
הַאֲנִ֥י אַשְׁבִּ֛יר וְלֹ֥א אוֹלִ֖יד יֹאמַ֣ר יְהוָ֑ה אִם־אֲנִ֧י הַמּוֹלִ֛יד וְעָצַ֖רְתִּי אָמַ֥ר אֱלֹהָֽיִךְ׃ ס
10 “Ku yi farin ciki tare da Urushalima ku kuma yi murna saboda ita, dukanku waɗanda kuke ƙaunarta; ku yi farin ciki matuƙa tare da ita, dukanku waɗanda kuke makoki a kanta.
שִׂמְח֧וּ אֶת־יְרוּשָׁלִַ֛ם וְגִ֥ילוּ בָ֖הּ כָּל־אֹהֲבֶ֑יהָ שִׂ֤ישׂוּ אִתָּהּ֙ מָשׂ֔וֹשׂ כָּל־הַמִּֽתְאַבְּלִ֖ים עָלֶֽיהָ׃
11 Gama za ku tsotsa ku kuma ƙoshi da nonon ta’aziyyarta; za ku sha sosai ku kuma ji daɗin yalwarta.”
לְמַ֤עַן תִּֽינְקוּ֙ וּשְׂבַעְתֶּ֔ם מִשֹּׁ֖ד תַּנְחֻמֶ֑יהָ לְמַ֧עַן תָּמֹ֛צּוּ וְהִתְעַנַּגְתֶּ֖ם מִזִּ֥יז כְּבוֹדָֽהּ׃ ס
12 Gama ga abin da Ubangiji ya faɗa, “Zan fadada salama gare ta kamar kogi, wadatar al’ummai kuma kamar rafi mai gudu; za ku tsotsa a kuma riƙe ku a hannunta ku kuma yi wasa a gwiwoyinta.
כִּֽי־כֹ֣ה ׀ אָמַ֣ר יְהוָ֗ה הִנְנִ֣י נֹטֶֽה־אֵ֠לֶיהָ כְּנָהָ֨ר שָׁל֜וֹם וּכְנַ֧חַל שׁוֹטֵ֛ף כְּב֥וֹד גּוֹיִ֖ם וִֽינַקְתֶּ֑ם עַל־צַד֙ תִּנָּשֵׂ֔אוּ וְעַל־בִּרְכַּ֖יִם תְּשָׁעֳשָֽׁעוּ׃
13 Kamar yadda uwa takan ta’azantar da ɗanta haka zan ta’azantar da ku; za ku kuma ta’azantu a Urushalima.”
כְּאִ֕ישׁ אֲשֶׁ֥ר אִמּ֖וֹ תְּנַחֲמֶ֑נּוּ כֵּ֤ן אָֽנֹכִי֙ אֲנַ֣חֶמְכֶ֔ם וּבִירֽוּשָׁלִַ֖ם תְּנֻחָֽמוּ׃
14 Sa’ad da kuka ga wannan, zuciyarku za tă yi farin ciki za ku kuma haɓaka kamar ciyawa; za a sanar da hannun Ubangiji ga bayinsa, amma za a nuna wa maƙiyansa fushinsa.
וּרְאִיתֶם֙ וְשָׂ֣שׂ לִבְּכֶ֔ם וְעַצְמוֹתֵיכֶ֖ם כַּדֶּ֣שֶׁא תִפְרַ֑חְנָה וְנוֹדְעָ֤ה יַד־יְהוָה֙ אֶת־עֲבָדָ֔יו וְזָעַ֖ם אֶת־אֹיְבָֽיו׃
15 Ga shi, Ubangiji yana zuwa da wuta, kuma kekunan yaƙinsa suna kama da guguwa; zai sauko da fushinsa da zafi, tsawatawarsa kuma da harsunan wuta.
כִּֽי־הִנֵּ֤ה יְהוָה֙ בָּאֵ֣שׁ יָב֔וֹא וְכַסּוּפָ֖ה מַרְכְּבֹתָ֑יו לְהָשִׁ֤יב בְּחֵמָה֙ אַפּ֔וֹ וְגַעֲרָת֖וֹ בְּלַהֲבֵי־אֵֽשׁ׃
16 Gama da wuta da kuma takobi Ubangiji zai yi hukunci a kan dukan mutane, kuma yawanci za su kasance waɗanda Ubangiji zai kashe.
כִּ֤י בָאֵשׁ֙ יְהוָ֣ה נִשְׁפָּ֔ט וּבְחַרְבּ֖וֹ אֶת־כָּל־בָּשָׂ֑ר וְרַבּ֖וּ חַֽלְלֵ֥י יְהוָֽה׃
17 “Waɗanda suka tsarkake suka kuma tsabtacce kansu don su je lambu, suna bin wannan da yake tsakiya waɗannan da suke cin naman aladu da ɓeraye da waɗansu abubuwan banƙyama, za su sadu da ƙarshensu tare,” in ji Ubangiji.
הַמִּתְקַדְּשִׁ֨ים וְהַמִּֽטַּהֲרִ֜ים אֶל־הַגַּנּ֗וֹת אַחַ֤ר אַחַת֙ בַּתָּ֔וֶךְ אֹֽכְלֵי֙ בְּשַׂ֣ר הַחֲזִ֔יר וְהַשֶּׁ֖קֶץ וְהָעַכְבָּ֑ר יַחְדָּ֥ו יָסֻ֖פוּ נְאֻם־יְהוָֽה׃
18 “Ni kuwa, saboda ayyukansu da kuma tunaninsu, ina dab da zuwa in tattara dukan al’ummai da harsuna, za su kuma zo su ga ɗaukakata.
וְאָנֹכִ֗י מַעֲשֵׂיהֶם֙ וּמַחְשְׁבֹ֣תֵיהֶ֔ם בָּאָ֕ה לְקַבֵּ֥ץ אֶת־כָּל־הַגּוֹיִ֖ם וְהַלְּשֹׁנ֑וֹת וּבָ֖אוּ וְרָא֥וּ אֶת־כְּבוֹדִֽי׃
19 “Zan kafa alama a cikinsu, zan kuma aika waɗansu da suka tsira zuwa al’ummai, zuwa Tarshish, zuwa Libiya da Lidiya (sanannun’yan aika), zuwa Tubal da kuma Girka, da kuma zuwa manisantan tsibirai da ba su taɓa jin labarin sunana ba ko su ga ɗaukakata. Za su yi shelar ɗaukakata a cikin al’ummai.
וְשַׂמְתִּ֨י בָהֶ֜ם א֗וֹת וְשִׁלַּחְתִּ֣י מֵהֶ֣ם ׀ פְּ֠לֵיטִים אֶֽל־הַגּוֹיִ֞ם תַּרְשִׁ֨ישׁ פּ֥וּל וְל֛וּד מֹ֥שְׁכֵי קֶ֖שֶׁת תֻּבַ֣ל וְיָוָ֑ן הָאִיִּ֣ים הָרְחֹקִ֗ים אֲשֶׁ֨ר לֹא־שָׁמְע֤וּ אֶת־שִׁמְעִי֙ וְלֹא־רָא֣וּ אֶת־כְּבוֹדִ֔י וְהִגִּ֥ידוּ אֶת־כְּבוֹדִ֖י בַּגּוֹיִֽם׃
20 Za su kuma dawo da dukan’yan’uwanku, daga dukan al’ummai, zuwa dutsena mai tsarki a Urushalima kamar hadaya ga Ubangiji, a kan dawakai, a kekunan yaƙi da wagonu, da kuma a kan alfadarai da kuma raƙuma,” in ji Ubangiji. “Za su kawo su, kamar yadda Isra’ilawa suke kawo hadayun hatsi, zuwa haikalin Ubangiji a cikin tsabtatattun kore.
וְהֵבִ֣יאוּ אֶת־כָּל־אֲחֵיכֶ֣ם מִכָּל־הַגּוֹיִ֣ם ׀ מִנְחָ֣ה ׀ לַֽיהוָ֡ה בַּסּוּסִ֡ים וּ֠בָרֶכֶב וּבַצַּבִּ֨ים וּבַפְּרָדִ֜ים וּבַכִּרְכָּר֗וֹת עַ֣ל הַ֥ר קָדְשִׁ֛י יְרוּשָׁלִַ֖ם אָמַ֣ר יְהוָ֑ה כַּאֲשֶׁ֣ר יָבִיאוּ֩ בְנֵ֨י יִשְׂרָאֵ֧ל אֶת־הַמִּנְחָ֛ה בִּכְלִ֥י טָה֖וֹר בֵּ֥ית יְהוָֽה׃
21 Zan kuwa zaɓa waɗansunsu kuma su zama firistoci da Lawiyawa,” in ji Ubangiji.
וְגַם־מֵהֶ֥ם אֶקַּ֛ח לַכֹּהֲנִ֥ים לַלְוִיִּ֖ם אָמַ֥ר יְהוָֽה׃
22 “Kamar yadda sabuwar duniya da sabuwar sama za su tabbata a gabana,” in ji Ubangiji, “haka sunanku da zuriyarku za su tabbata.
כִּ֣י כַאֲשֶׁ֣ר הַשָּׁמַ֣יִם הַ֠חֳדָשִׁים וְהָאָ֨רֶץ הַחֲדָשָׁ֜ה אֲשֶׁ֨ר אֲנִ֥י עֹשֶׂ֛ה עֹמְדִ֥ים לְפָנַ֖י נְאֻם־יְהוָ֑ה כֵּ֛ן יַעֲמֹ֥ד זַרְעֲכֶ֖ם וְשִׁמְכֶֽם׃
23 Daga wannan sabon wata zuwa wancan, kuma daga wannan Asabbaci zuwa wancan, dukan mutane za su zo su rusuna a gabana,” in ji Ubangiji.
וְהָיָ֗ה מִֽדֵּי־חֹ֙דֶשׁ֙ בְּחָדְשׁ֔וֹ וּמִדֵּ֥י שַׁבָּ֖ת בְּשַׁבַּתּ֑וֹ יָב֧וֹא כָל־בָּשָׂ֛ר לְהִשְׁתַּחֲוֹ֥ת לְפָנַ֖י אָמַ֥ר יְהוָֽה׃
24 “Za su kuma fita su ga gawawwakin mutanen da suka yi mini tayarwa; tsutsotsin da suke cinsu ba za su taɓa mutuwa ba, balle wutar da take ƙona su ta mutu, za su kuma zama abin ƙyama ga dukan mutane.”
וְיָצְא֣וּ וְרָא֔וּ בְּפִגְרֵי֙ הָאֲנָשִׁ֔ים הַפֹּשְׁעִ֖ים בִּ֑י כִּ֣י תוֹלַעְתָּ֞ם לֹ֣א תָמ֗וּת וְאִשָּׁם֙ לֹ֣א תִכְבֶּ֔ה וְהָי֥וּ דֵרָא֖וֹן לְכָל־בָּשָֽׂר׃

< Ishaya 66 >