< Ishaya 64 >

1 Da ma za ka tsage sammai ka sauko, ai, da duwatsu za su yi rawar jiki a gabanka!
2 Kamar sa’ad da wuta takan ci rassa ta sa ruwa ya tafasa, ka sauko ka sanar da sunanka ga abokan gābanka ka kuma sa al’ummai su yi rawan jiki a gabanka!
כִּקְדֹ֧חַ אֵ֣שׁ הֲמָסִ֗ים מַ֚יִם תִּבְעֶה־אֵ֔שׁ לְהֹודִ֥יעַ שִׁמְךָ֖ לְצָרֶ֑יךָ מִפָּנֶ֖יךָ גֹּויִ֥ם יִרְגָּֽזוּ׃
3 Gama sa’ad da ka aikata abubuwan bantsoron da ba mu sa tsammani ba, ka sauko, duwatsu kuma suka yi rawar jiki a gabanka.
בַּעֲשֹׂותְךָ֥ נֹורָאֹ֖ות לֹ֣א נְקַוֶּ֑ה יָרַ֕דְתָּ מִפָּנֶ֖יךָ הָרִ֥ים נָזֹֽלּוּ׃
4 Tun fil azal babu wanda ya taɓa ji, babu kunnen da ya gane, babu idon da ya ga wani Allah in ban da kai, wanda ya aikata waɗannan al’amura a madadin waɗanda suke sa zuciya a gare shi.
וּמֵעֹולָ֥ם לֹא־שָׁמְע֖וּ לֹ֣א הֶאֱזִ֑ינוּ עַ֣יִן לֹֽא־רָאָ֗תָה אֱלֹהִים֙ זוּלָ֣תְךָ֔ יַעֲשֶׂ֖ה לִמְחַכֵּה־לֹֽו׃
5 Kakan taimaki waɗanda suke murnan yin abin da yake daidai, waɗanda sukan tuna da hanyoyinka. Amma sa’ad da muka ci gaba da yin zunubi, kakan yi fushi. Ta yaya za mu sami ceto ke nan?
פָּגַ֤עְתָּ אֶת־שָׂשׂ֙ וְעֹ֣שֵׂה צֶ֔דֶק בִּדְרָכֶ֖יךָ יִזְכְּר֑וּךָ הֵן־אַתָּ֤ה קָצַ֙פְתָּ֙ וַֽנֶּחֱטָ֔א בָּהֶ֥ם עֹולָ֖ם וְנִוָּשֵֽׁעַ׃
6 Dukanmu mun zama kamar wanda yake marar tsabta, kuma dukan ayyukanmu masu adalci sun zama kamar ƙazaman tsummoki; duk mun zama kamar busasshen ganye, kamar iska haka zunubanmu sukan share mu.
וַנְּהִ֤י כַטָּמֵא֙ כֻּלָּ֔נוּ וּכְבֶ֥גֶד עִדִּ֖ים כָּל־צִדְקֹתֵ֑ינוּ וַנָּ֤בֶל כֶּֽעָלֶה֙ כֻּלָּ֔נוּ וַעֲוֹנֵ֖נוּ כָּר֥וּחַ יִשָּׂאֻֽנוּ׃
7 Babu wanda yake kira bisa sunanka ko ya yi ƙoƙarin riƙe ka; gama ka ɓoye fuskarka daga gare mu ka kuma sa muka lalace saboda zunubanmu.
וְאֵין־קֹורֵ֣א בְשִׁמְךָ֔ מִתְעֹורֵ֖ר לְהַחֲזִ֣יק בָּ֑ךְ כִּֽי־הִסְתַּ֤רְתָּ פָנֶ֙יךָ֙ מִמֶּ֔נּוּ וַתְּמוּגֵ֖נוּ בְּיַד־עֲוֹנֵֽנוּ׃
8 Duk da haka, Ubangiji, kai ne Ubanmu. Mu yumɓu ne, kai kuma mai ginin tukwane; dukanmu aikin hannunka ne.
וְעַתָּ֥ה יְהוָ֖ה אָבִ֣ינוּ אָ֑תָּה אֲנַ֤חְנוּ הַחֹ֙מֶר֙ וְאַתָּ֣ה יֹצְרֵ֔נוּ וּמַעֲשֵׂ֥ה יָדְךָ֖ כֻּלָּֽנוּ׃
9 Kada ka yi fushi fiye da kima, ya Ubangiji; kada ka tuna da zunubanmu har abada. Da ma ka dube mu, muna roƙonka, gama dukanmu mutanenka ne.
אַל־תִּקְצֹ֤ף יְהוָה֙ עַד־מְאֹ֔ד וְאַל־לָעַ֖ד תִּזְכֹּ֣ר עָוֹ֑ן הֵ֥ן הַבֶּט־נָ֖א עַמְּךָ֥ כֻלָּֽנוּ׃
10 Biranenka masu tsarki sun zama hamada; har Sihiyona ma ta zama hamada; Urushalima ta zama kango.
עָרֵ֥י קָדְשְׁךָ֖ הָי֣וּ מִדְבָּ֑ר צִיֹּון֙ מִדְבָּ֣ר הָיָ֔תָה יְרוּשָׁלַ֖͏ִם שְׁמָמָֽה׃
11 Haikalinmu mai tsarki da kuma mai daraja, inda kakanninmu suka yabe ka, an ƙone da wuta, kuma dukan abubuwan da muke ƙauna sun lalace.
בֵּ֧ית קָדְשֵׁ֣נוּ וְתִפְאַרְתֵּ֗נוּ אֲשֶׁ֤ר הִֽלְל֙וּךָ֙ אֲבֹתֵ֔ינוּ הָיָ֖ה לִשְׂרֵ֣פַת אֵ֑שׁ וְכָל־מַחֲמַדֵּ֖ינוּ הָיָ֥ה לְחָרְבָּֽה׃
12 Bayan dukan wannan, ya Ubangiji, ba za ka yi wani abu ba? Za ka yi shiru ka hore mu fiye da kima?
הַעַל־אֵ֥לֶּה תִתְאַפַּ֖ק יְהוָ֑ה תֶּחֱשֶׁ֥ה וּתְעַנֵּ֖נוּ עַד־מְאֹֽד׃ ס

< Ishaya 64 >