< Ishaya 63 >

1 Wane ne wannan mai zuwa daga Edom, daga Bozra, saye da jajjayen rigunarsa? Wane ne wannan, sanye cikin daraja, tafe cikin girmar ƙarfinsa? “Ni ne, mai magana cikin adalci, mai ikon ceto.”
Who is this that cometh from Edom, with dyed garments from Bozrah? this that is glorious in his apparel, marching in the greatness of his strength? I that speak in righteousness, mighty to save.
2 Me ya sa rigunanka suka yi ja, sai ka ce na wanda yake tattaka’ya’yan inabi?
Wherefore art thou red in thine apparel, and thy garments like him that treadeth in the winefat?
3 “Na tattake’ya’yan inabi ni kaɗai; cikin al’ummai kuma babu wani tare da ni. Na tattake su cikin fushina Na matse su cikin hasalata; jininsu ya fantsamar wa rigunana, na kuma ɓata dukan tufafina.
I have trodden the winepress alone; and of the peoples there was no man with me: yea, I trod them in mine anger, and trampled them in my fury; and their lifeblood is sprinkled upon my garments, and I have stained all my raiment.
4 Gama ranar ɗaukan fansa tana a cikin zuciyata, kuma shekarar fansata ta zo.
For the day of vengeance was in mine heart, and the year of my redeemed is come.
5 Na duba, amma babu wanda zai taimaka, na yi mamaki cewa ba wanda ya goyi baya; saboda haka hannuna ya yi mini ceto, fushina kuma ya rayar da ni.
And I looked, and there was none to help; and I wondered that there was none to uphold: therefore mine own arm brought salvation unto me; and my fury, it upheld me.
6 Na tattake al’ummai cikin fushina; cikin hasalata kuma na sa sun bugu na kuma zub da jininsu a ƙasa.”
And I trod down the peoples in mine anger, and made them drunk in my fury, and I poured out their lifeblood on the earth.
7 Zan ba da labarin alherin Ubangiji, ayyukan da suka sa a yabe shi, bisa ga dukan abubuwan da Ubangiji ya yi mana, I, ayyuka masu kyan da ya yi domin gidan Isra’ila, bisa ga jinƙansa da yawan alheransa.
I will make mention of the lovingkindnesses of the LORD, [and] the praises of the LORD, according to all that the LORD hath bestowed on us; and the great goodness toward the house of Israel, which he hath bestowed on them according to his mercies, and according to the multitude of his lovingkindnesses.
8 Ya ce, “Babu shakka su mutanena ne,’ya’ya maza waɗanda ba za su ruɗe ni ba”; ta haka ya zama Mai Cetonsu.
For he said, Surely, they are my people, children that will not deal falsely: so he was their saviour.
9 Cikin dukan damuwarsu shi ma ya damu, mala’ikan da yake gabansa ya cece su. Cikin ƙauna da jinƙai ya fanshe su; ya kuma ɗaga su ya riƙe su dukan kwanakin dā
In all their affliction he was afflicted, and the angel of his presence saved them: in his love and in his pity he redeemed them; and he bare them, and carried them all the days of old.
10 Duk da haka suka yi tawaye suka ɓata wa Ruhu Mai Tsarki rai. Saboda haka ya juya ya kuma zama abokin gābansu shi kansa kuma ya yaƙe su.
But they rebelled, and grieved his holy spirit: therefore he was turned to be their enemy, [and] himself fought against them.
11 Sa’an nan mutanensa suka tuna kwanakin dā, kwanakin Musa da mutanensa, ina yake shi wanda ya fitar da su ta teku, da makiyayan garkensa? Ina shi yake wanda ya sa Ruhunsa Mai Tsarki a cikinsu,
Then he remembered the days of old, Moses, [and] his people, [saying], Where is he that brought them up out of the sea with the shepherds of his flock? where is he that put his holy spirit in the midst of them?
12 wanda ya aika hannu ɗaukakarsa mai iko ya kasance a hannun dama na Musa, wanda ya raba ruwaye a gabansu, don yă sami wa kansa madawwamin suna,
that caused his glorious arm to go at the right hand of Moses? that divided the water before them, to make himself an everlasting name?
13 wanda ya bishe su cikin zurfafa? Kamar doki a fili, ba su yi tuntuɓe ba;
that led them through the depths, as an horse in the wilderness, that they stumbled not?
14 kamar shanun da suke gangarawa zuwa kwari, haka Ruhun Ubangiji ya ba su hutu. Ga yadda ka bishe mutanenka don ka ba wa kanka suna mai ɗaukaka.
As the cattle that go down into the valley, the spirit of the LORD caused them to rest: so didst thou lead thy people, to make thyself a glorious name.
15 Ka duba daga sama ka gani daga kursiyinka da yake bisa, mai tsarki da kuma mai ɗaukaka. Ina kishinka da kuma ikonka? Ka janye juyayi da kuma tausayin da kake yi mana daga gare mu.
Look down from heaven, and behold from the habitation of thy holiness and of thy glory: where is thy zeal and thy mighty acts? the yearning of thy bowels and thy compassions are restrained toward me.
16 Amma kai Ubanmu ne, ko Ibrahim bai san mu ba Isra’ila kuma bai yarda da mu ba; kai, ya Ubangiji, kai ne Ubanmu, Mai Fansarmu tun fil azal ne sunanka.
For thou art our father, though Abraham knoweth us not, and Israel doth not acknowledge us: thou, O LORD, art our father; our redeemer from everlasting is thy name.
17 Don me, ya Ubangiji, ka sa muna barin hanyoyinka muka kuma taurare zukatanmu don kada mu girmama ka? Ka komo domin darajar bayinka, kabilan da suke abin gādonka.
O LORD, why dost thou make us to err from thy ways, and hardenest our heart from thy fear? Return for thy servants’ sake, the tribes of thine inheritance.
18 Gama a ɗan lokaci mutanenka suka mallaki wurinka mai tsarki, amma yanzu abokan gābanmu sun tattake wurinka mai tsarki.
Thy holy people possessed [it] but a little while: our adversaries have trodden down thy sanctuary.
19 Mu naka tun fil azal; ba ka taɓa yin mulki a kansu ba, ba a taɓa kira su da sunanka ba.
We are become as they over whom thou never barest rule; as they that were not called by thy name.

< Ishaya 63 >