< Ishaya 62 >

1 Saboda Sihiyona ba zan yi shiru ba, saboda Urushalima ba zan huta ba, sai adalcinta ya haskaka kamar hasken safiya, cetonta kuma ya haskaka kamar fitila mai haske.
למען ציון לא אחשה ולמען ירושלם לא אשקוט עד יצא כנגה צדקה וישועתה כלפיד יבער
2 Al’ummai za su ga adalcinki, sarakuna kuma za su ga ɗaukakarki; za a kira ki da sabon suna sunan da bakin Ubangiji zai ambata.
וראו גוים צדקך וכל מלכים כבודך וקרא לך שם חדש אשר פי יהוה יקבנו
3 Za ki zama rawanin daraja a hannun Ubangiji, rawanin sarauta a hannun Allahnki.
והיית עטרת תפארת ביד יהוה וצנוף (וצניף) מלוכה בכף אלהיך
4 Ba za a ƙara ce da ke Yasasshiya ba, ko a kira ƙasarki Kango. Amma za a ce da ke Hefziba ƙasarki kuma Bewula; gama Ubangiji zai ji daɗinki, ƙasarki kuma za tă yi aure.
לא יאמר לך עוד עזובה ולארצך לא יאמר עוד שממה--כי לך יקרא חפצי בה ולארצך בעולה כי חפץ יהוה בך וארצך תבעל
5 Kamar yadda saurayi kan auri yarinya, haka’ya’yanki maza za su aure ki; kamar kuma yadda ango yakan yi farin ciki da amaryarsa, haka Allahnki zai yi farin ciki da ke.
כי יבעל בחור בתולה יבעלוך בניך ומשוש חתן על כלה ישיש עליך אלהיך
6 Na sa matsara a kan katangarki, ya Urushalima; ba za su taɓa yin shiru ba, dare da rana. Ku da kuke kira bisa sunan Ubangiji, kada ku ba kanku hutu,
על חומתיך ירושלם הפקדתי שמרים--כל היום וכל הלילה תמיד לא יחשו המזכרים את יהוה--אל דמי לכם
7 kuma kada ku ba shi hutu sai ya kafa Urushalima ya kuma mai da ita yabon duniya.
ואל תתנו דמי לו עד יכונן ועד ישים את ירושלם תהלה--בארץ
8 Ubangiji ya rantse da hannunsa na dama ta hannunsa kuma mai iko cewa, “Ba zan ƙara ba da hatsinki ya zama abinci ga abokan gābanki ba, baƙi kuma ba za su ƙara shan ruwan inabin wanda kika sha wahala samu ba;
נשבע יהוה בימינו ובזרוע עזו אם אתן את דגנך עוד מאכל לאיביך ואם ישתו בני נכר תירושך אשר יגעת בו
9 amma waɗanda suka girbe shi za su ci shi su kuma yabi Ubangiji, waɗanda kuma suka tattara’ya’yan inabi za su sha shi a filayen wurina mai tsarki.”
כי מאספיו יאכלהו והללו את יהוה ומקבציו ישתהו בחצרות קדשי
10 Ku wuce, ku wuce ƙofofi! Ku shirya hanya saboda mutane. Ku gina, ku gina babbar hanya! Ku kawar da duwatsu. Ku ɗaga tuta saboda al’ummai.
עברו עברו בשערים פנו דרך העם סלו סלו המסלה סקלו מאבן הרימו נס על העמים
11 Ubangiji ya yi shela ga iyakokin duniya cewa, “Faɗa wa Diyar Sihiyona, ‘Ga Mai Cetonki yana zuwa! Ga ladarsa tana tare da shi, sakamakonsa yana raka shi.’”
הנה יהוה השמיע אל קצה הארץ אמרו לבת ציון הנה ישעך בא הנה שכרו אתו ופעלתו לפניו
12 Za a ce da shi Tsattsarkar Mutane, Fansassu na Ubangiji; za a kuma ce da ke Wadda Aka Nema Birnin da Ba Za a Ƙara Yashe ta ba.
וקראו להם עם הקדש גאולי יהוה ולך יקרא דרושה עיר לא נעזבה

< Ishaya 62 >