< Ishaya 61 >

1 Ruhun Ubangiji Mai Iko Duka yana a kaina, domin Ubangiji ya shafe ni domin in yi wa’azi labari mai daɗi ga matalauta. Ya aiko ni in warkar da waɗanda suka karai a zuci, don in yi shelar’yanci don ɗaurarru in kuma kunce’yan kurkuku daga duhu
רוח אדני יהוה עלי--יען משח יהוה אתי לבשר ענוים שלחני לחבש לנשברי לב לקרא לשבוים דרור ולאסורים פקח קוח
2 don in yi shelar shekarar tagomashin Ubangiji da kuma ranar ɗaukan fansar Allahnmu, don in ta’azantar da dukan waɗanda suke makoki,
לקרא שנת רצון ליהוה ויום נקם לאלהינו לנחם כל אבלים
3 in tanada wa waɗanda suke baƙin ciki a Sihiyona, in maido musu rawani mai kyau a maimako na toka, man murna a maimako na makoki, da kuma rigar yabo a maimako na ruhun fid da zuciya. Za a ce da su itatuwan oak na adalci, shukin Ubangiji don bayyana darajarsa.
לשום לאבלי ציון לתת להם פאר תחת אפר שמן ששון תחת אבל--מעטה תהלה תחת רוח כהה וקרא להם אילי הצדק מטע יהוה להתפאר
4 Za su sāke gina kufai na dā su raya wurare da aka lalace tun da daɗewa; za su sabunta biranen da aka rurrushe da aka lalace tun zamanai masu yawa da suka wuce.
ובנו חרבות עולם שממות ראשנים יקוממו וחדשו ערי חרב שממות דור ודור
5 Baƙi za su yi kiwon garkunanki; baƙi za su yi miki noman gonaki da gonakin inabinki.
ועמדו זרים ורעו צאנכם ובני נכר אכריכם וכרמיכם
6 Za a kuma kira ku firistocin Ubangiji, za a kira ku masu hidimar Allahnmu. Za ku ci wadatar waɗansu al’ummai, kuma a cikin dukiyarsu za ku yi taƙama.
ואתם כהני יהוה תקראו--משרתי אלהינו יאמר לכם חיל גוים תאכלו ובכבודם תתימרו
7 A maimakon kunyarsu mutanena za su sami rabi riɓi biyu, a maimakon wulaƙanci za su yi farin ciki cikin gādonsu; ta haka za su gāji rabo riɓi biyu a ƙasarsu, da kuma madawwamin farin ciki zai zama nasu.
תחת בשתכם משנה וכלמה ירנו חלקם לכן בארצם משנה יירשו שמחת עולם תהיה להם
8 “Gama ni, Ubangiji, ina ƙaunar adalci; na ƙi fashi da aikata laifi. Cikin adalcina zan sāka musu in kuma yi madawwamin alkawari da su.
כי אני יהוה אהב משפט שנא גזל בעולה ונתתי פעלתם באמת וברית עולם אכרות להם
9 Za a san da zuriyarsu a cikin al’ummai’ya’yansu kuma a cikin mutane. Dukan waɗanda suka gan su za su san cewa su mutane ne da Ubangiji ya sa wa albarka.”
ונודע בגוים זרעם וצאצאיהם בתוך העמים כל ראיהם יכירום כי הם זרע ברך יהוה
10 Ina jin daɗi ƙwarai a cikin Ubangiji; raina yana farin ciki a cikin Allahna. Gama ya suturce ni da rigunan ceto ya yi mini ado da rigar adalci, yadda ango yakan yi wa kansa ado kamar firist kamar kuma yadda amarya takan sha ado da duwatsunta masu daraja.
שוש אשיש ביהוה תגל נפשי באלהי--כי הלבישני בגדי ישע מעיל צדקה יעטני כחתן יכהן פאר וככלה תעדה כליה
11 Gama kamar yadda ƙasa takan sa tsire-tsire su tohu lambu kuma ya sa iri ya yi girma, haka Ubangiji Mai Iko Duka zai sa adalci da yabo su tsiro a gaban dukan al’ummai.
כי כארץ תוציא צמחה וכגנה זרועיה תצמיח--כן אדני יהוה יצמיח צדקה ותהלה נגד כל הגוים

< Ishaya 61 >