< Ishaya 56 >

1 Ga abin da Ubangiji yana cewa, “Ku riƙe gaskiya ku yi abin da yake daidai, gama cetona yana kusa za a kuma bayyana adalcina nan da nan.
כה אמר יהוה שמרו משפט ועשו צדקה כי קרובה ישועתי לבוא וצדקתי להגלות׃
2 Mai albarka ne mutumin da ya aikata wannan, mutumin da ya riƙe kam yana kiyaye Asabbaci ba tare da ƙazantar da shi ba, yana kuma kiyaye kansa daga yin mugun abu.”
אשרי אנוש יעשה זאת ובן אדם יחזיק בה שמר שבת מחללו ושמר ידו מעשות כל רע׃
3 Kada baƙon da ya miƙa kansa ga Ubangiji ya ce, “Ai Ubangiji zai ware ni daga mutanensa.” Kada kuma wani bābā ya yi gunaguni cewa, “Ni busasshen itace ne kawai.”
ואל יאמר בן הנכר הנלוה אל יהוה לאמר הבדל יבדילני יהוה מעל עמו ואל יאמר הסריס הן אני עץ יבש׃
4 Gama ga abin da Ubangiji ya faɗa, “Wa bābānnin da suna kiyaye Asabbatai, waɗanda suka zaɓi yin abin da ya gamshe ni suna kuma riƙe da alkawarina kankan,
כי כה אמר יהוה לסריסים אשר ישמרו את שבתותי ובחרו באשר חפצתי ומחזיקים בבריתי׃
5 a gare su cikin haikalina da kuma bangayensa zan ba da matuni da kuma suna mafi kyau fiye da’ya’ya maza da kuma’ya’ya mata; zan ba su madawwamin sunan da ba za a raba su da shi ba.
ונתתי להם בביתי ובחומתי יד ושם טוב מבנים ומבנות שם עולם אתן לו אשר לא יכרת׃
6 Baƙin da suka miƙa kansu ga Ubangiji don su bauta masa, su kuma ƙaunaci sunan Ubangiji, waɗanda kuma suke yin masa sujada, duk waɗanda suka kiyaye Asabbaci ba tare da ƙazantar da shi ba suka kuma riƙe alkawarina kankan,
ובני הנכר הנלוים על יהוה לשרתו ולאהבה את שם יהוה להיות לו לעבדים כל שמר שבת מחללו ומחזיקים בבריתי׃
7 waɗannan ne zan kai tsattsarkan dutsena in sa su yi farin ciki a gidana na addu’a. Hadayunsu na ƙonawa da sadakokinsu za su zama abin karɓa a bagadena; gama za a ce da gidana gidan addu’a domin dukan al’ummai.”
והביאותים אל הר קדשי ושמחתים בבית תפלתי עולתיהם וזבחיהם לרצון על מזבחי כי ביתי בית תפלה יקרא לכל העמים׃
8 Ubangiji Mai Iko Duka ya furta cewa, zai tattara korarru na Isra’ila, “Zan ƙara tattaro waɗansu bayan waɗanda na riga na tattara.”
נאם אדני יהוה מקבץ נדחי ישראל עוד אקבץ עליו לנקבציו׃
9 Ku zo, dukanku namun jeji, ku zo ku ci, dukanku namun jeji!
כל חיתו שדי אתיו לאכל כל חיתו ביער׃
10 Matsaran Isra’ila makafi ne, dukansu jahilai ne; dukansu bebayen karnuka ne ba za su iya haushi ba; suna kwance ne kawai suna mafarki, suna son barci ba dama.
צפו עורים כלם לא ידעו כלם כלבים אלמים לא יוכלו לנבח הזים שכבים אהבי לנום׃
11 Su karnuka ne masu kwaɗayi; ba su taɓa ƙoshi. Su makiyaya ne marasa ganewa; duk sun nufi inda suka ga dama, kowa yana nemar wa kansa riba.
והכלבים עזי נפש לא ידעו שבעה והמה רעים לא ידעו הבין כלם לדרכם פנו איש לבצעו מקצהו׃
12 Kowanne yakan ce, “Zo, bari in samo ruwan inabi! Bari mu cika cikinmu da barasa! Gobe ma zai zama kamar yau, ko ma fiye da haka.”
אתיו אקחה יין ונסבאה שכר והיה כזה יום מחר גדול יתר מאד׃

< Ishaya 56 >