< Ishaya 55 >
1 “Ku zo, dukanku masu jin ƙishi, ku zo wurin ruwaye; ku kuma da ba ku da kuɗi, ku zo, ku saya ku kuma ci! Ku zo, ku saya ruwan inabi da madara ba tare da kuɗi ba ba za ku kuma biya kome ba.
2 Don me za ku kashe kuɗi a kan abin da ba abinci ba, ku kuma yi wahala a kan abin da ba za ku ƙoshi ba? Ku saurara, ku saurare ni, ku kuma ci abin da yake da kyau, ranku kuma zai ji daɗin abinci mafi kyau.
3 Ku kasa kunne ku kuma zo gare ni; ku saurare ni, don ranku ya rayu. Zan yi madawwamin alkawari da ku, zan nuna muku ƙaunata marar ƙarewa da na yi wa Dawuda alkawari.
4 Duba, na mai da shi shaida ga mutane, shugaba da kuma jagorar mutane.
5 Tabbatacce za ku kira al’umman da ba ku sani ba, kuma al’umman da ba ku sani ba za su sheƙo a guje zuwa wurinku, saboda Ubangiji Allahnku, Mai Tsarkin nan na Isra’ila, gama ya darjanta ku.”
6 Ku nemi Ubangiji tun yana samuwa; ku yi kira gare shi tun yana kusa.
7 Bari mugu ya bar irin halinsa mugu kuma ya sāke irin tunaninsa. Bari yă juyo ga Ubangiji, zai kuwa ji tausayinsa, ya juyo ga Allahnmu kuma, gama shi mai gafartawa ne a sauƙaƙe.
8 “Gama tunanina ba tunaninku ba ne, yadda kuke yin abubuwa ba yadda nake yin abubuwa ba ne,” in ji Ubangiji.
9 “Kamar yadda sammai suke can nesa da ƙasa, haka yadda nake yin abubuwa suke dabam da yadda kuke yin abubuwa tunanina kuma dabam da naku.
10 Kamar yadda ruwan sama da dusar ƙanƙara suke saukowa daga sama, ba sa komowa ba tare da sun jiƙe duniya sun kuma sa su yi’ya’ya su kuma yi toho, don su ba da iri ga mai shuki da kuma abinci ga mai ci,
11 haka maganata da take fitowa daga bakina. Ba za tă koma gare ni wofi ba, amma za tă cika abin da nake so ta kuma cika abin da na aike ta tă yi.
12 Za ku fita da farin ciki a kuma bi da ku da salama; duwatsu da tuddai za su ɓarke da waƙa a gabanku, dukan itatuwan jeji kuma za su tafa hannuwansu.
13 A maimakon sarƙaƙƙiya, itacen fir ne zai tsiro, a maimakon ƙayayyuwa kuma, itacen ci-zaƙi ne zai tsiro. Wannan zai zama matuni na abin da Ni Ubangiji na yi, madawwamiyar alama ce, wadda ba za a datse ba.”