< Ishaya 54 >
1 “Ki rera, ya ke bakararriya, ke da ba ki taɓa haihuwa ba; ki ɓarke da waƙa, ki yi sowa don farin ciki, ke da ba ki taɓa naƙuda ba; domin’ya’yan mace mai kaɗaici sun fi na mai miji yawa,” in ji Ubangiji.
“Sing, you barren woman, you who have not given birth; break into joyful singing and cry aloud, you who have never been in birth labor. For the children of the desolate one are more than the children of the married woman,” says Yahweh.
2 “Ki fadada wurin tentinki, ki miƙe labulen tentinki da fāɗi, kada ki janye; ƙara tsawon igiyoyinta, ki kuma ƙara ƙarfin turakunta.
“Make your tent larger and spread your tent curtains farther out, unsparingly; lengthen your ropes and strengthen your stakes.
3 Gama za ki fadada zuwa dama da hagu; zuriyarki za su kori al’ummai su kuma zauna a kufan biranensu.
For you will spread out to the right hand and to the left, and your descendants will conquer nations and resettle desolate cities.
4 “Kada ki ji tsoro; ba za ki sha kunya ba. Kada ki ji tsoron wulaƙanci, ba za a ƙasƙantar da ke ba. Za ki manta da kunyar ƙuruciyarki ba kuwa za ki tuna da zargin zaman gwauruwarki ba.
Do not fear for you will not be ashamed, nor be discouraged for you will not be disgraced; you will forget the shame of your youth and the disgrace of your abandonment.
5 Gama Mahaliccinki shi ne mijinki, Ubangiji Maɗaukaki ne sunansa, Mai Tsarkin nan na Isra’ila ne Mai Fansarki; ana ce da shi Allahn dukan duniya.
For your Maker is your husband; Yahweh of hosts is his name. The Holy One of Israel is your Redeemer; he is called the God of the whole earth.
6 Ubangiji zai kira sai ka ce ke mace ce da aka yashe ta tana kuma damuwa a ranta, macen da ta yi aure a ƙuruciya, sai kawai aka ƙi ta,” in ji Allahnki.
For Yahweh has called you back as a wife abandoned and grieved in spirit, like a woman married young and rejected,” says your God.
7 “Gama a ɗan ƙanƙanen lokaci na rabu da ke, amma da ƙauna mai zurfi zan sāke dawo da ke.
“For a short time I abandoned you, but with great compassion I will gather you.
8 Cikin fushi mai zafi na ɓoye fuskata daga gare ki na ɗan lokaci, amma da madawwamin alheri zan ji tausayinki,” in ji Ubangiji Mai Fansarki.
In a flood of anger I hid my face from you momentarily; but with everlasting covenant faithfulness I will have mercy on you— says Yahweh, the one who rescues you.
9 “A gare ni wannan ya yi kamar kwanakin Nuhu, sa’ad da na rantse cewa ruwan Nuhu ba za su ƙara rufe duniya ba. Yanzu fa na rantse ba zan yi fushi da ke ba, ba zan ƙara tsawata miki kuma ba.
For this is like the waters of Noah to me: as I swore that the waters of Noah would never again pass over the earth, so have I sworn that I will not be angry with you or rebuke you.
10 Ko da duwatsu za su girgiza a kuma tumɓuke tuddai, duk da haka madawwamiyar ƙaunata da nake yi miki ba za tă jijjigu ba ba kuwa za a kawar da alkawarin salamata ba,” in ji Ubangiji, wanda ya ji tausayinki.
Though the mountains may fall and the hills be shaken, yet my steadfast love will not turn away from you, nor will my covenant of peace be shaken— says Yahweh, who has mercy on you.
11 “Ya ke birni mai shan azaba, wadda hadari ya bulale ki ba a kuma ta’azantar da ke ba, zan gina ke da duwatsu turkuwoyis, zan kafa harsashenki da duwatsun saffaya.
Afflicted one, storm-driven and uncomforted one, look, I will set your pavement in turquoise, and lay your foundations with sapphires.
12 Zan gina hasumiyarki da jan yakutu, ƙofofinki kuma da duwatsu masu haske, dukan katangarki kuma da duwatsu masu daraja.
I will make your pinnacles of rubies and your gates of sparkling stones, and your outer wall of beautiful stones.
13 Ubangiji zai koya wa dukan’ya’yanki maza, da girma kuma salamar’ya’yanki zai zama.
Then all your children will be taught by Yahweh; and the peace of your children will be great.
14 Da adalci za a kafa ke. Zalunci zai yi nesa da ke; ba za ki kasance da wani abin da za ki ji tsoro ba. Za a kawar da duk wani abin banrazana; ba zai yi kusa da ke ba.
In righteousness you will be established, and you will be far from oppression, for you will not fear; and from terror, for it will not come near to you.
15 In wani ya far miki, ba daga wurina ba ne; duk wanda ya far miki zai miƙa wuya gare ki.
Look, if anyone stirs up trouble, it will not be from me; anyone who stirs up trouble with you will fall in defeat.
16 “Duba, ni ne wanda na halicci maƙeri wanda yake zuga garwashi ya zama harshen wuta ya kuma ƙera makamin da ya dace da aikinsa. Ni ne kuma na halicci mai hallakarwa ya yi ɓarna;
See, I have created the craftsman, who blows the burning coals and forges weapons as his work, and I have created the destroyer to destroy.
17 ba makamin da aka ƙera don yă cuce ki da zai yi nasara, za ki kuma mayar da magana ga duk wanda ya zarge ki. Wannan ne gādon bayin Ubangiji, kuma wannan ita ce nasararsu daga gare ni,” in ji Ubangiji.
No weapon that is formed against you will succeed; and you will condemn everyone who accuses you. This is the heritage of the servants of Yahweh, and their vindication from me—this is Yahweh's declaration.”