< Ishaya 48 >

1 “Ku kasa kunne ga wannan, ya gidan Yaƙub, waɗanda ake kira da sunan Isra’ila suka kuma fito daga zuriyar Yahuda, ku da kuke yin rantsuwa da sunan Ubangiji kuna kuma kira sunan Allah na Isra’ila, amma ba da gaskiya ko adalci ba,
Audite hæc, domus Jacob, qui vocamini nomine Israël, et de aquis Juda existis; qui juratis in nomine Domini, et Dei Israël recordamini non in veritate neque in justitia.
2 ku da kuke kiran kanku’yan ƙasar birni mai tsarki kuna kuma dogara ga Allah na Isra’ila, Ubangiji Maɗaukaki ne sunansa,
De civitate enim sancta vocati sunt, et super Deum Israël constabiliti sunt: Dominus exercituum nomen ejus.
3 na nanata abubuwan da suka riga suka faru tuntuni, bakina ya yi shelar su na kuma sanar da su; sai nan da nan na aikata, suka kuma faru.
Priora ex tunc annuntiavi, et ex ore meo exierunt, et audita feci ea: repente operatus sum, et venerunt.
4 Gama na san yadda kuke da taurinkai; jijiyoyin wuyanku ƙarafa ne, goshinku tagulla ne.
Scivi enim quia durus es tu, et nervus ferreus cervix tua, et frons tua ærea.
5 Saboda haka na faɗa waɗannan abubuwa tuntuni; kafin su faru na yi shelarsu gare ku saboda kada ku ce, ‘Gumakana ne suka yi su; siffar itacena da allahn zinariyana ne ya ƙaddara su.’
Prædixi tibi ex tunc; antequam venirent, indicavi tibi, ne forte diceres: Idola mea fecerunt hæc, et sculptilia mea et conflatilia mandaverunt ista.
6 Kun riga kun ji waɗannan abubuwa; kuka gan su duka. Ba za ku yarda da su ba? “Daga yanzu zuwa gaba zan faɗa muku sababbin abubuwa, na ɓoyayyun abubuwan da ba ku sani ba.
Quæ audisti, vide omnia; vos autem, num annuntiastis? Audita feci tibi nova ex tunc, et conservata sunt quæ nescis.
7 Yanzu an halicce su, ba da daɗewa ba; ba ku riga kun ji game da su kafin yau ba. Saboda haka ba za ku ce, ‘I, na san da su ba.’
Nunc creata sunt et non ex tunc; et ante diem, et non audisti ea, ne forte dicas: Ecce ego cognovi ea.
8 Ba ku ji ko balle ku gane ba; tun da kunnenku bai buɗu ba. Tabbatacce na san yadda kun zama masu tayarwa; an kira ku’yan tawaye daga haihuwa.
Neque audisti, neque cognovisti, neque ex tunc aperta est auris tua: scio enim quia prævaricans prævaricaberis, et transgressorem ex utero vocavi te.
9 Saboda girman sunana na jinkirta fushina; saboda girman yabona na janye shi daga gare ku, don dai kada a yanke ku.
Propter nomen meum longe faciam furorem meum, et laude mea infrenabo te, ne intereas.
10 Duba, na tace ku, ko da yake ba kamar azurfa ba; na gwada ku cikin wutar wahala.
Ecce excoxi te, sed non quasi argentum; elegi te in camino paupertatis.
11 Saboda girmana, saboda girmana, na yi haka. Yaya zan ƙyale a ƙazantar da kaina? Ba zan raba ɗaukakata da wani ba.
Propter me, propter me faciam, ut non blasphemer; et gloriam meam alteri non dabo.
12 “Ka kasa kunne gare ni, ya Yaƙub, Isra’ila, wanda na kira cewa, Ni ne shi; ni ne na farko ni ne kuma na ƙarshe.
Audi me, Jacob, et Israël, quem ego voco: ego ipse, ego primus, et ego novissimus.
13 Hannuna ne ya kafa harsashen duniya, hannuna na dama kuma ya shimfiɗa sammai; sa’ad da na kira su, duka suka miƙe tsaye gaba ɗaya.
Manus quoque mea fundavit terram, et dextera mea mensa est cælos; ego vocabo eos, et stabunt simul.
14 “Ku tattaru, dukanku ku kuma saurara, Wanne a cikin gumakan ya iya faɗa waɗannan abubuwa? Zaɓaɓɓen da Ubangiji yake ƙauna zai aikata nufinsa a kan Babilon; hannunsa zai yi gāba da Babiloniyawa.
Congregamini, omnes vos, et audite: quis de eis annuntiavit hæc? Dominus dilexit eum, faciet voluntatem suam in Babylone, et brachium suum in Chaldæis.
15 Ni kaina, na faɗa; I, na kira shi. Zan kawo shi, zai kuma yi nasara a cikin aikinsa.
Ego, ego locutus sum, et vocavi eum; adduxi eum, et directa est via ejus.
16 “Ku zo kusa da ni ku kuma saurari wannan. “Daga farkon shela ban yi magana a ɓoye ba; a lokacin da ya faru, ina nan a wurin.” Yanzu kuwa Ubangiji Mai Iko Duka ya aiko ni, da Ruhunsa.
Accedite ad me et audite hoc: non a principio in abscondito locutus sum: ex tempore antequam fieret, ibi eram: et nunc Dominus Deus misit me, et spiritus ejus.
17 Ga abin da Ubangiji yana cewa, Mai Fansarku, Mai Tsarkin nan na Isra’ila ya ce, “Ni ne Ubangiji Allahnku, wanda ya koya muku abin da ya fi muku kyau, wanda ya muku hanyar da za ku bi.
Hæc dicit Dominus, redemptor tuus, Sanctus Israël: Ego Dominus Deus tuus, docens te utilia, gubernans te in via qua ambulas.
18 Da a ce kawai za ku mai da hankali ga umarnaina, da salamarku ta zama kamar kogi, adalcinku kamar raƙuman teku.
Utinam attendisses mandata mea: facta fuisset sicut flumen pax tua, et justitia tua sicut gurgites maris:
19 Da zuriyarku ta zama kamar yashi,’ya’yanku kamar tsabar hatsin da ba a iya ƙidayawa; da ba za a taɓa yanke sunansu balle a hallaka su daga gabana ba.”
et fuisset quasi arena semen tuum, et stirps uteri tui ut lapilli ejus; non interisset et non fuisset attritum nomen ejus a facie mea.
20 Ku bar Babilon, ku gudu daga Babiloniyawa! Ku yi shelar wannan da sowa ta farin ciki ku kuma furta shi. Ku aika shi zuwa iyakokin duniya; ku ce, “Ubangiji ya fanshi bawansa Yaƙub.”
Egredimini de Babylone, fugite a Chaldæis, in voce exsultationis annuntiate: auditum facite hoc, et efferte illud usque ad extrema terræ. Dicite: Redemit Dominus servum suum Jacob.
21 Ba su ji ƙishi ba sa’ad da ya bishe su a cikin hamada; ya sa ruwa ya malalo dominsu daga dutse; ya tsage dutse ruwa kuwa ya kwararo.
Non sitierunt in deserto, cum educeret eos: aquam de petra produxit eis, et scidit petram, et fluxerunt aquæ.
22 “Babu salama ga mugaye” in ji Ubangiji.
Non est pax impiis, dicit Dominus.

< Ishaya 48 >