< Ishaya 47 >
1 “Ki gangara, ki zauna a ƙura, Budurwa Diyar Babilon; ki zauna a ƙasa ba tare da rawani ba, Diyar Babiloniyawa. Ba za a ƙara kira ke marar ƙarfi’yar gata ba.
“Go down and sit in the dust, O Virgin Daughter of Babylon. Sit on the ground without a throne, O Daughter of Chaldea! For you will no longer be called tender or delicate.
2 Ɗauki dutsen niƙa ki niƙa gari; ki kware lulluɓinki. Ki ɗaga fatarinki ki bar ƙafafunki tsirara, ki kuma yi ta ratsa cikin rafuffuka.
Take millstones and grind flour; remove your veil; strip off your skirt, bare your thigh, and wade through the streams.
3 Tsirararki zai bayyana za a kuma buɗe kunyarki. Zan ɗauki fansa; ba zan bar wani ba.”
Your nakedness will be uncovered and your shame will be exposed. I will take vengeance; I will spare no one.”
4 Mai Fansarmu, Ubangiji Maɗaukaki shi ne sunansa, shi ne Mai Tsarkin nan na Isra’ila.
Our Redeemer—the LORD of Hosts is His name— is the Holy One of Israel.
5 “Zauna shiru, tafi cikin duhu, Diyar Babiloniya; ba za a ƙara kira ke sarauniyar masarautai.
“Sit in silence and go into darkness, O Daughter of Chaldea. For you will no longer be called the queen of kingdoms.
6 Na yi fushi da mutanena na ƙazantar da gādona; na ba su ga hannunki, ba ki kuwa nuna musu jinƙai ba. Har ma da tsofaffi kin jibga musu kaya masu nauyi sosai.
I was angry with My people; I profaned My heritage, and I placed them under your control. You showed them no mercy; even on the elderly you laid a most heavy yoke.
7 Kika ce, ‘Zan ci gaba har abada, madawwamiyar sarauniya!’ Amma ba ki lura da waɗannan abubuwa ko ki yi la’akari a kan abin da zai faru ba.
You said, ‘I will be queen forever.’ You did not take these things to heart or consider their outcome.
8 “To, yanzu fa, ki kasa kunne, ke mai ƙaunar nishaɗi, mai zama da rai kwance kina kuma ce wa kanki, ‘Ni ce, kuma babu wani in ban da ni. Ba zan taɓa zama gwauruwa ko in sha wahalar rashin’ya’ya ba.’
So now hear this, O lover of luxury who sits securely, who says to herself, ‘I am, and there is none besides me. I will never be a widow or know the loss of children.’
9 Duk waɗannan za su sha kanki cikin farat ɗaya, a rana guda, rashin’ya’ya da gwauranci. Za su zo a kanki da cikakken minzani, duk da yawan masu dubanki da kuma dukan sihirinki.
These two things will overtake you in a moment, in a single day: loss of children, and widowhood. They will come upon you in full measure, in spite of your many sorceries and the potency of your spells.
10 Kin dogara a muguntarki kika kuma ce, ‘Babu wanda ya gan ni.’ Hikimarki da saninki sun ɓad da ke sa’ad da kika ce wa kanki, ‘Ni ce, kuma babu wani in ban da ni.’
You were secure in your wickedness; you said, ‘No one sees me.’ Your wisdom and knowledge led you astray; you told yourself, ‘I am, and there is none besides me.’
11 Bala’i zai fāɗo a kanki, kuma ba za ki san yadda za ki rinjaye shi yă janye ba. Masifa za tă fāɗo a kanki da ba za ki iya tsai da ita da kuɗin fansa ba; lalacewar da ba ki taɓa mafarkinta ba za tă auko miki nan da nan.
But disaster will come upon you; you will not know how to charm it away. A calamity will befall you that you will be unable to ward off. Devastation will happen to you suddenly and unexpectedly.
12 “Ki dai ci gaba, da sihirinki da kuma makarunki masu yawa, waɗanda kika yi ta wahala tun kina jaririya. Mai yiwuwa ki yi nasara, mai yiwuwa ki jawo fargaba.
So take your stand with your spells and with your many sorceries, with which you have wearied yourself from your youth. Perhaps you will succeed; perhaps you will inspire terror!
13 Dukan shawarwarin da kika samu sun dai gajiyar da ke ne kawai! Bari masananki na taurari su zo gaba, waɗannan masu zāna taswirar sammai suna kuma faɗa miki dukan abin da zai faru da ke wata-wata, bari su cece ki daga abin da zai faru da ke.
You are wearied by your many counselors; let them come forward now and save you— your astrologers who observe the stars, who monthly predict your fate.
14 Tabbas suna kama da bunnu; wuta za tă cinye su ƙaf. Ba za su ma iya ceton kansu daga ikon wutar ba. Ba wutar da wani zai ji ɗumi; ba wutar da za a zauna kusa da ita.
Surely they are like stubble; the fire will burn them up. They cannot deliver themselves from the power of the flame. There will be no coals to warm them or fire to sit beside.
15 Abin da za su iya yi miki ke nan kawai, waɗannan da kika yi ta fama da su kika kuma yi ciniki da su tun kina jaririya. Kowannensu zai tafi cikin kuskurensa; babu ko ɗayan da zai cece ki.
This is what they are to you— those with whom you have labored and traded from youth— each one strays in his own direction; not one of them can save you.