< Ishaya 46 >

1 Bel ya rusuna, Nebo ya durƙusa ƙasa; ana ɗaukan gumakansu a kan dabbobi ne. Siffofin da ake yawo da su nawaya ne, kayan nauyi masu gajiyarwa.
כרע בל קרס נבו--היו עצביהם לחיה ולבהמה נשאתיכם עמוסות משא לעיפה
2 Sun durƙusa suka kuma rusuna tare; ba su iya kuɓutar da nauyin kaya su kansu sukan tafi bauta.
קרסו כרעו יחדו לא יכלו מלט משא ונפשם בשבי הלכה
3 “Ku kasa kunne gare ni, ya ku gidan Yaƙub, dukanku waɗanda kuka rage na gidan Isra’ila, ku da na lura da ku tun da aka yi cikinku, na kuma riƙe ku tun haihuwarku.
שמעו אלי בית יעקב וכל שארית בית ישראל--העמסים מני בטן הנשאים מני רחם
4 Har lokacin da kuka tsufa kuka yi furfura ni ne shi, ni ne shi wanda zai lura da ku. Na yi ku zan kuma riƙe ku; zan lura da ku in kuma kuɓutar da ku.
ועד זקנה אני הוא ועד שיבה אני אסבל אני עשיתי ואני אשא ואני אסבל ואמלט
5 “Da wa za ku kwatanta ni ko ku ɗauka daidai da ni? Da wa nake kama da har da za ku kwatanta ni?
למי תדמיוני ותשוו ותמשלוני ונדמה
6 Waɗansu sukan zubar da zinariya daga jaka su kuma auna azurfa a ma’auni; sukan yi haya maƙerin zinariya don yă ƙera allah, su kuma rusuna su yi masa sujada.
הזלים זהב מכיס וכסף בקנה ישקלו ישכרו צורף ויעשהו אל יסגדו אף ישתחוו
7 Sukan daga shi a kafaɗunsu su kuma ɗauke shi; sukan kafa shi a tsaye a wurinsa, a can kuwa zai tsaya. Daga wannan wuri ba zai iya gusawa ba. Ko da wani ya nemi taimakonsa, ba ya amsawa; ba zai iya cetonsa daga wahala ba.
ישאהו על כתף יסבלהו ויניחהו תחתיו ויעמד--ממקומו לא ימיש אף יצעק אליו ולא יענה מצרתו לא יושיענו
8 “Ku tuna da wannan, ku sa shi a zuciya, ku riƙe shi a zuciya, ku’yan tawaye.
זכרו זאת והתאששו השיבו פושעים על לב
9 Ku tuna da abubuwan da suka riga suka faru, waɗannan na tun dā; ni ne Allah, kuma babu wani; ni ne Allah kuma babu wani kamar ni.
זכרו ראשנות מעולם כי אנכי אל ואין עוד אלהים ואפס כמוני
10 Nakan sanar da ƙarshe tun daga farko, daga fil azal, abin da yake zuwa nan gaba. Na ce nufina zai tabbata, kuma zan aikata dukan abin da na gan dama.
מגיד מראשית אחרית ומקדם אשר לא נעשו אמר עצתי תקום וכל חפצי אעשה
11 Daga gabas na kira tsuntsun da yake farauta; daga can ƙasa mai nesa, wani mutumin da zai cika nufina. Abin da na riga na faɗa, shi zan sa ya faru; abin da na shirya, shi zan aikata.
קרא ממזרח עיט מארץ מרחק איש עצתו (עצתי) אף דברתי אף אביאנה--יצרתי אף אעשנה
12 Ku kasa kunne, ku masu taurinkai, ku da kuke nesa da adalci.
שמעו אלי אבירי לב--הרחוקים מצדקה
13 Ina kawo adalcina kusa, ba shi da nisa; kuma cetona ba zai jinkirta ba. Zan yi wa Sihiyona ceto, darajata ga Isra’ila.
קרבתי צדקתי לא תרחק ותשועתי לא תאחר ונתתי בציון תשועה לישראל תפארתי

< Ishaya 46 >