< Ishaya 44 >
1 “Amma yanzu ka saurara, ya Yaƙub, bawana, Isra’ila, wanda zaɓa.
2 Ga abin da Ubangiji yana cewa, shi wanda ya yi ka, wanda ya siffanta ka a cikin mahaifa, wanda kuma zai taimake ka. Kada ka ji tsoro, ya Yaƙub, bawana, Yeshurun, wanda na zaɓa.
3 Gama zan zuba ruwa a ƙeƙasasshiyar ƙasa, rafuffuka kuma a busasshiyar ƙasa; zan ba da Ruhuna ga’ya’yanka, albarkata kuma ga zuriyarka.
4 Za su tsiro kamar ciyawa a wuriyar ruwa, kamar kurmi kusa da rafuffuka masu gudu.
5 Wani zai ce, ‘Ni na Ubangiji ne’; wani kuma zai kira kansa da sunan Yaƙub; har yanzu wani zai rubuta a hannunsa, ‘Na Ubangiji,’ ya kuma ɗauki sunan Isra’ila.
6 “Ga abin da Ubangiji yana cewa, Sarki da kuma Mai Fansar Isra’ila, Ubangiji Maɗaukaki. Ni ne farko ni ne kuma ƙarshe; in ban da ni babu wani Allah.
7 Wane ne kuwa kama da ni? Ya faɗa a ji. Bari yă yi shela ya kuma nuna shi a gabana mene ne ya faru tun da na kafa mutanena na dā, mene ne kuma bai riga ya faru ba, I, bari yă faɗa abin da zai zo.
8 Kada ku firgita kada kuma ku ji tsoro. Ban furta wannan na kuma yi faɗar haka tuntuni ba? Ku ne shaiduna. Akwai wani Allah in ban da ni? A’a, babu wani Dutse; ban san da wani ba.”
9 Duk masu yin gumaka ba kome ba ne, da kuma abubuwan da suke ɗauka da daraja banza ne. Waɗanda za su yi magana a madadinsu makafi ne; jahilai ne, marasa kunya.
10 Waɗanda suke siffanta allah su kuma yi zubin gunki, waɗanda ba za su yi musu ribar kome ba?
11 Shi da irinsa za su sha kunya; masu sassaƙa ba kome ba mutane ne kurum. Bari su tattaru su ɗauki matsayinsu; za su firgita su kuma sha mummunan kunya.
12 Maƙeri yakan ɗauki kayan aiki ya yi aiki da shi a cikin garwashi; ya ƙera gunki da guduma, ya gyara shi da hannuwansa masu ƙarfi. Yakan ji yunwa ya kuma rasa ƙarfi; yakan sha ruwa ya kuma ji gajiya.
13 Kafinta yakan gwada katako yă kuma zāna siffar da alli; yă goge shi da kayan aiki yă kuma zāna shi da alƙalami. Yă siffanta shi a kamannin mutum, mutum cikin dukan darajarsa, don yă ajiye shi a cikin masujada.
14 Yakan ka da itacen saifires, ko kuwa ya ɗauki saifires ko oak. Yă bar shi yă yi girma a cikin itatuwan kurmi, ko yă shuka itacen fir, ruwan sama kuma yă sa yă yi girma.
15 Abin hura wutar mutum ne; yakan ɗebi waɗansu yă hura wuta don yă ji ɗumi, ya hura wuta yă gasa burodi. Amma yakan ƙera zinariya yă kuma yi masa sujada; yakan yi gunki sa’an nan yă rusuna masa.
16 Rabin katakon yakan ƙone a wuta; a kansa yakan dafa abincinsa, yă gasa namansa yă kuma ci sai ya ƙoshi. Yakan ji ɗumi yă kuma ce, “Aha! Na ji ɗumi; na gan wutar.”
17 Da sauran itacen yakan yi allah, gunkinsa; yă rusuna masa yă kuma yi sujada. Yakan yi masa addu’a yă ce, “Ka cece ni; kai ne allahna.”
18 Ba su san kome ba, ba su fahimci kome ba; an rufe idanunsu don kada su gani, tunaninsu kuma a rufe don kada su fahimta.
19 Ba wanda yakan dakata ya yi tunani, ba wanda yake da sani ko fahimi ya ce, “Da rabinsa na yi amfani da shi don hura wuta; na ma gasa burodi a kan garwashinsa, na gasa nama na kuma ci. Ya kamata in yi abin ƙyama daga abin da ya rage? Ya kamata in rusuna wa guntun katako?”
20 Yana cin toka, zuciyar da ta ruɗe tana ɓad da shi; ba zai iya cece kansa ba, ko ya ce, “Wannan abin da yake hannun dama na ba ƙarya ba ne?”
21 “Tuna da waɗannan abubuwa, ya Yaƙub, gama kai bawana ne, ya Isra’ila. Na yi ka, kai bawana ne; Ya Isra’ila, ba zan manta da kai ba.
22 Na shafe laifofinka kamar girgije, zunubanka kamar hazon safe. Ka komo wurina, gama na kuɓutar da kai.”
23 Ku rera don farin ciki, ya sammai, gama Ubangiji ya aikata wannan; ku yi sowa, ya duniya a ƙarƙashi. Ku ɓarke da waƙoƙi, ku duwatsu, ku jeji da dukan itatuwanku, gama Ubangiji ya kuɓutar da Yaƙub, ya nuna ɗaukakarsa a cikin Isra’ila.
24 “Ga abin da Ubangiji yana cewa, Mai Fansarka, wanda ya yi ka a cikin mahaifa. “Ni ne Ubangiji, wanda ya yi dukan abubuwa, wanda ya shimfiɗa sammai ya kuma kafa harsashen duniya da kansa,
25 wanda ya sassāke alamun annabawan ƙarya ya masu duba suka zama wawaye, wanda ya tumɓuke koyon masu hikima ya mai da shi banza,
26 wanda ya tabbatar da maganganun bayinsa ya kuma cika annabce-annabcen’yan aikansa, “wanda ya ce game da Urushalima, ‘Za a zauna a cikinta,’ game da garuruwan Yahuda, ‘Za a gina su,’
27 wanda ya ce wa zurfin ruwaye, ‘Ku bushe, zan kuma busar da rafuffukanku,’
28 wanda ya yi zancen Sairus ya ce, ‘Shi ne makiyayina zan kuma cika dukan abin da na gan dama; zai yi zancen Urushalima cewa, “Bari a sāke gina ta,” game da haikali kuma cewa, “Bari a kafa harsashinsa.”’