< Ishaya 43 >

1 To, fa, ga abin da Ubangiji yana cewa, shi da ya halicce ka, ya Yaƙub, shi da ya siffanta ka, ya Isra’ila, “Kada ka ji tsoro, gama na fanshe ka; na kira ka da suna; kai nawa ne.
ועתה כה אמר יהוה בראך יעקב ויצרך ישראל אל תירא כי גאלתיך קראתי בשמך לי אתה׃
2 Sa’ad da kuka bi ta ruwaye, zan kasance tare da ku; sa’ad da kuka bi ta koguna, ba za su kwashe ku ba. Sa’ad da kuke tafiyata cikin wuta, ba za tă ƙone ku ba; harsunan wutar ba za su ƙone ku ba.
כי תעבר במים אתך אני ובנהרות לא ישטפוך כי תלך במו אש לא תכוה ולהבה לא תבער בך׃
3 Gama ni ne Ubangiji, Allahnku, Mai Tsarkin nan na Isra’ila, Mai Cetonku; na bayar da Masar don fansa, Kush da Seba a maimakonku.
כי אני יהוה אלהיך קדוש ישראל מושיעך נתתי כפרך מצרים כוש וסבא תחתיך׃
4 Da yake ku masu daraja da kuma girma ne a idona, saboda kuma ina ƙaunarku, zan ba da mutane a maimakonku, al’umma kuma domin ranku.
מאשר יקרת בעיני נכבדת ואני אהבתיך ואתן אדם תחתיך ולאמים תחת נפשך׃
5 Kada ku ji tsoro, gama ina tare da ku; zan kawo yaranku daga gabas in kuma tattara ku daga yamma.
אל תירא כי אתך אני ממזרח אביא זרעך וממערב אקבצך׃
6 Zan ce wa arewa, ‘Ku miƙa su!’ Ga kudu kuma, ‘Kada ku riƙe su.’ Kawo’ya’yana maza daga nesa’ya’yana mata kuma daga iyakar duniya,
אמר לצפון תני ולתימן אל תכלאי הביאי בני מרחוק ובנותי מקצה הארץ׃
7 kowa da ake kira da sunana, wanda aka halitta saboda ɗaukakata, wanda na siffanta na kuma yi.”
כל הנקרא בשמי ולכבודי בראתיו יצרתיו אף עשיתיו׃
8 Jagoranci waɗanda suke da idanu amma suke makafi, waɗanda suke da kunnuwa amma suke kurame.
הוציא עם עור ועינים יש וחרשים ואזנים למו׃
9 Dukan al’ummai su taru mutane kuma su tattaru. Wane ne a cikinsu ya yi faɗar wannan ya kuma yi mana shelar abubuwan da suka riga suka faru? Bari su kawo shaidunsu don su tabbatar cewa sun yi daidai, don waɗansu su ji su kuma ce, “Gaskiya ne.”
כל הגוים נקבצו יחדו ויאספו לאמים מי בהם יגיד זאת וראשנות ישמיענו יתנו עדיהם ויצדקו וישמעו ויאמרו אמת׃
10 “Ku ne shaiduna,” in ji Ubangiji, “bawana kuma wanda na zaɓa, saboda ka sani ka kuma gaskata ni ka kuma fahimci cewa ni ne shi. Kafin ni babu allahn da aka siffanta, ba kuwa za a yi wani a bayana ba.
אתם עדי נאם יהוה ועבדי אשר בחרתי למען תדעו ותאמינו לי ותבינו כי אני הוא לפני לא נוצר אל ואחרי לא יהיה׃
11 Ni kaɗai, ni ne Ubangiji, kuma in ban da ni babu wani mai ceto.
אנכי אנכי יהוה ואין מבלעדי מושיע׃
12 Na bayyana na ceci na kuma furta, Ni ne, ba wani baƙon allah a cikinku. Ku ne shaiduna,” in ji Ubangiji, “cewa ni ne Allah.
אנכי הגדתי והושעתי והשמעתי ואין בכם זר ואתם עדי נאם יהוה ואני אל׃
13 I, kuma tun fil azal ni ne shi. Babu wani da zai amshi daga hannuna. Sa’ad da na aikata, wa zai iya sauyawa?”
גם מיום אני הוא ואין מידי מציל אפעל ומי ישיבנה׃
14 Ga abin da Ubangiji yana cewa, Mai Fansarku, Mai Tsarkin nan na Isra’ila, “Saboda ku zan aika Babilon in kawo dukan Babiloniyawa kamar masu gudun hijira, a cikin jiragen ruwa waɗanda suke taƙama da su.
כה אמר יהוה גאלכם קדוש ישראל למענכם שלחתי בבלה והורדתי בריחים כלם וכשדים באניות רנתם׃
15 Ni ne Ubangiji, Mai Tsarkin nan, Mahaliccin Isra’ila, Sarkinku.”
אני יהוה קדושכם בורא ישראל מלככם׃
16 Ga abin da Ubangiji yana cewa, shi da ya yi hanya ta cikin teku, hanya ta cikin manyan ruwaye,
כה אמר יהוה הנותן בים דרך ובמים עזים נתיבה׃
17 wanda ya ja kekunan yaƙi da dawakai, mayaƙa da kuma ƙarin mayaƙa tare ya kwantar da su a can, ba kuwa za su ƙara tashi ba, ya kashe hayaƙi daga lagwani,
המוציא רכב וסוס חיל ועזוז יחדו ישכבו בל יקומו דעכו כפשתה כבו׃
18 “Ku manta da abubuwan da suka riga suka faru; kada ku yi tunanin abin da ya riga ya wuce.
אל תזכרו ראשנות וקדמניות אל תתבננו׃
19 Duba, ina yi abu sabo! Yanzu yana faruwa; ba ku gan shi ba? Ina yin hanya a cikin hamada rafuffuka kuma a cikin ƙeƙasasshiyar ƙasa.
הנני עשה חדשה עתה תצמח הלוא תדעוה אף אשים במדבר דרך בישמון נהרות׃
20 Namun jeji suna girmama ni, diloli da mujiyoyi ma haka, domin na tanada musu ruwa a hamada da rafuffuka a ƙeƙasasshiyar ƙasa, don a ba da abin sha ga mutanena, zaɓaɓɓuna,
תכבדני חית השדה תנים ובנות יענה כי נתתי במדבר מים נהרות בישימן להשקות עמי בחירי׃
21 mutanen da na yi saboda kaina don su furta yabona.
עם זו יצרתי לי תהלתי יספרו׃
22 “Duk da haka ba ku kira bisa sunana ba, ya Yaƙub, ba ku gajiyar da kanku saboda ni ba, ya Isra’ila.
ולא אתי קראת יעקב כי יגעת בי ישראל׃
23 Ba ku kawo mini tumaki don hadaya ta ƙonewa ba, balle ku girmama ni da hadayunku. Ban nawaita muku da hadaya ta gari ba balle in gajiyar da ku da bukatar turare.
לא הביאת לי שה עלתיך וזבחיך לא כבדתני לא העבדתיך במנחה ולא הוגעתיך בלבונה׃
24 Ba ku saya wani turaren kalamus domina ba ko ku gamshe ni da kitsen hadayunku. Amma kun nawaita ni da zunubanku kuka kuma gajiyar da ni da laifofinku.
לא קנית לי בכסף קנה וחלב זבחיך לא הרויתני אך העבדתני בחטאותיך הוגעתני בעונתיך׃
25 “Ni kaɗai ne na shafe laifofinku, saboda sunana, ban kuma ƙara tunawa da zunubanku ba.
אנכי אנכי הוא מחה פשעיך למעני וחטאתיך לא אזכר׃
26 Ku tunashe ni abin da ya riga ya wuce, bari mu yi muhawwara wannan batu tare; ku kawo hujjarku na nuna rashin laifinku.
הזכירני נשפטה יחד ספר אתה למען תצדק׃
27 Mahaifinku na farko ya yi zunubi; masu magana a madadinku suka yi mini tayarwa.
אביך הראשון חטא ומליציך פשעו בי׃
28 Saboda haka zan kunyata manyan baƙi na haikalinku, zan tura Yaƙub ga hallaka Isra’ila kuwa yă zama abin dariya.
ואחלל שרי קדש ואתנה לחרם יעקב וישראל לגדופים׃

< Ishaya 43 >