< Ishaya 42 >

1 “Ga bawana, wanda na ɗaukaka, zaɓaɓɓen nan nawa wanda nake jin daɗi; Zan sa Ruhuna a cikinsa zai kuwa kawo adalci ga al’ummai.
הן עבדי אתמך בו בחירי רצתה נפשי נתתי רוחי עליו משפט לגוים יוציא
2 Ba zai yi ihu ko ya tā da murya, ko ya daga muryarsa a tituna ba.
לא יצעק ולא ישא ולא ישמיע בחוץ קולו
3 Iwan da ta tanƙware ba zai karye ba, ba zai kashe lagwani mai hayaƙi ba. Cikin aminci zai kawo adalci;
קנה רצוץ לא ישבור ופשתה כהה לא יכבנה לאמת יוציא משפט
4 ba zai kāsa ko ya karai ba sai ya kafa adalci a duniya. Cikin dokarsa tsibirai za su sa zuciya.”
לא יכהה ולא ירוץ עד ישים בארץ משפט ולתורתו איים ייחלו
5 Ga abin da Allah Ubangiji ya ce, shi da ya halicci sammai ya kuma miƙe su, wanda ya shimfiɗa duniya da dukan abin da ya fito cikinta, wanda ya ba wa mutanenta numfashi, da rai ga waɗanda suke tafiya a kanta.
כה אמר האל יהוה בורא השמים ונוטיהם רקע הארץ וצאצאיה נתן נשמה לעם עליה ורוח להלכים בה
6 “Ni Ubangiji, na kira ka cikin adalci; zan riƙe hannunka. Zan kiyaye ka in kuma sa ka zama alkawari ga mutane haske kuma ga Al’ummai,
אני יהוה קראתיך בצדק ואחזק בידך ואצרך ואתנך לברית עם--לאור גוים
7 don ka buɗe idanun makafi ka’yantar da kamammu daga kurkuku kuma kunce ɗaurarrun kurkuku masu zama cikin duhu.
לפקח עינים עורות להוציא ממסגר אסיר מבית כלא ישבי חשך
8 “Ni ne Ubangiji; sunana ke nan! Ba zan ba da ɗaukakata ga wani ba ko yabona ga gumaka.
אני יהוה הוא שמי וכבודי לאחר לא אתן ותהלתי לפסילים
9 Duba, abubuwan da sun tabbata, sababbin abubuwa kuwa nake furtawa; kafin ma su soma faruwa na sanar da su gare ku.”
הראשנות הנה באו וחדשות אני מגיד בטרם תצמחנה אשמיע אתכם
10 Ku rera sabuwar waƙa ga Ubangiji, ku yi yabonsa daga iyakar duniya, ku da kuka gangara zuwa teku, da kome da yake cikinsa, ku tsibirai, da waɗanda suke zama a cikinsu.
שירו ליהוה שיר חדש תהלתו מקצה הארץ יורדי הים ומלאו איים וישביהם
11 Bari hamada da garuruwanta su tā da muryoyinsu; bari wuraren zaman da Kedar ke zama su yi farin ciki. Bari mutanen Sela su rera don farin ciki; bari su yi sowa daga ƙwanƙolin duwatsu.
ישאו מדבר ועריו חצרים תשב קדר ירנו ישבי סלע מראש הרים יצוחו
12 Bari su ɗaukaka Ubangiji su kuma yi shelar yabonsa a tsibirai.
ישימו ליהוה כבוד ותהלתו באיים יגידו
13 Ubangiji zai fita ya yi yaƙi kamar mai ƙarfi, kamar jarumi zai yi himma; da ihu zai tā da kirarin yaƙi zai kuma yi nasara a kan abokan gābansa.
יהוה כגבור יצא כאיש מלחמות יעיר קנאה יריע אף יצריח--על איביו יתגבר
14 “Na daɗe ina shiru, na yi shiru na kuma ƙame kaina. Amma yanzu, kamar mace mai naƙuda, na yi ƙara, ina nishi ina kuma haki.
החשיתי מעולם--אחריש אתאפק כיולדה אפעה אשם ואשאף יחד
15 Zan lalatar da duwatsu da tuddai in busar da dukan itatuwansu; zan mai da koguna su zama tsibirai in kuma busar da tafkuna.
אחריב הרים וגבעות וכל עשבם אוביש ושמתי נהרות לאיים ואגמים אוביש
16 Zan yi wa makafi jagora a hanyoyin da ba su taɓa sani ba, a hanyoyin da ba a saba ba zan bishe su; zan mai da duhu ya zama haske a gabansu in kuma mai da ƙasa mai kururrumai ta zama sumul. Abubuwan da zan yi ke nan; ba zan yashe su ba.
והולכתי עורים בדרך לא ידעו--בנתיבות לא ידעו אדריכם אשים מחשך לפניהם לאור ומעקשים למישור--אלה הדברים עשיתם ולא עזבתים
17 Amma waɗanda suka dogara ga gumaka, waɗanda suke ce wa siffofi, ‘Ku ne allolinmu,’ za a mai da su baya da kunya.
נסגו אחור יבשו בשת הבטחים בפסל האמרים למסכה אתם אלהינו
18 “Ka ji, kai kurma; duba, kai makaho, ka kuma gani!
החרשים שמעו והעורים הביטו לראות
19 Wane ne makaho in ba bawana ba, da kuma kurma in ba ɗan aikan da na aika ba? Wane ne makaho kamar wanda ya miƙa kai gare ni, makaho kamar bawan Ubangiji?
מי עור כי אם עבדי וחרש כמלאכי אשלח מי עור כמשלם ועור כעבד יהוה
20 Kun ga abubuwa masu yawa, amma ba ku kula ba; kunnuwanku suna a buɗe, amma ba kwa jin wani abu.”
ראית (ראות) רבות ולא תשמר פקוח אזנים ולא ישמע
21 Yakan gamsar da Ubangiji saboda adalcinsa ya sa dokarsa ta zama mai girma da kuma mai ɗaukaka.
יהוה חפץ למען צדקו יגדיל תורה ויאדיר
22 Amma ga mutanen da aka washe aka kuma kwashe ganima, an yi wa dukansu tarko a cikin rammuka ko kuma an ɓoye su cikin kurkuku. Sun zama ganima, babu wani da zai kuɓutar da su; an mai da su ganima, ba wanda zai ce, “Mayar da su.”
והוא עם בזוז ושסוי הפח בחורים כלם ובבתי כלאים החבאו היו לבז ואין מציל משסה ואין אמר השב
23 Wane ne a cikinku zai saurari wannan ko ya kasa kunne sosai a cikin kwanaki masu zuwa?
מי בכם יאזין זאת יקשב וישמע לאחור
24 Wa ya ba da Yaƙub don yă zama ganima Isra’ila kuma ga masu kwasar ganima? Ba Ubangiji ba ne, wanda kuka yi wa zunubi? Gama ba su bi hanyoyinsa ba; ba su yi biyayya da dokarsa ba.
מי נתן למשוסה (למשסה) יעקב וישראל לבזזים הלוא יהוה זו חטאנו לו ולא אבו בדרכיו הלוך ולא שמעו בתורתו
25 Saboda haka ya zuba musu zafin fushinsa, yaƙi mai tsanani. Ya rufe su cikin harsunan wuta, duk da haka ba su gane ba; ya cinye su, amma ba su koyi kome ba.
וישפך עליו חמה אפו ועזוז מלחמה ותלהטהו מסביב ולא ידע ותבער בו ולא ישים על לב

< Ishaya 42 >