< Ishaya 4 >
1 A wannan rana mata guda bakwai za su cafke namiji guda su ce, “Ma ciyar da kanmu mu kuma yi wa kanmu sutura; ka dai bari mu ce kai ne mijinmu. Ka ɗauke mana kunyar da za mu sha.”
On that day seven women will take hold of one man and say, “Our own food we will eat, our own clothing we will wear. But let us take your name to remove our shame.”
2 A wannan rana Reshen Ubangiji zai zama kyakkyawa da kuma ɗaukaka, kuma amfanin ƙasar zai zama abin fariya da ɗaukakar waɗanda suka rayu a Isra’ila.
On that day the branch of Yahweh will be beautiful and glorious, and the fruit of the land will be tasty and delightful for those survivors in Israel.
3 Waɗanda suka rage a Sihiyona, waɗanda suka rage a Urushalima, za a ce da su masu tsarki, wato, dukan waɗanda aka rubuta a cikin masu rai a Urushalima.
It will happen that the one who is left in Zion and the one who remains in Jerusalem will be called holy, everyone who is written down as living in Jerusalem.
4 Ubangiji zai wanke duk wani ƙazantar matan Sihiyona; ya tsabtacce jinin da aka zubar daga Urushalima ta wurin ruhun hukunci da yake ƙuna kamar wuta.
This will happen when the Lord will have washed away the filth of the daughters of Zion, and will have cleansed the blood stains from Jerusalem's midst, by means of the spirit of judgment and the spirit of flaming fire.
5 Sa’an nan Ubangiji zai sa girgijen hayaƙi da rana da harshen wuta da dare a bisa dukan Dutsen Sihiyona da kuma bisa waɗanda suka tattaru a can; a bisa duka kuwa ɗaukakar za tă zama rumfa.
Then over the whole site of Mount Zion and over her place of assembly, Yahweh will create cloud and smoke by day, and the shining of a flaming fire by night; it will be a canopy over all the glory.
6 Za tă zama rumfa da inuwar da za tă tare zafin rana, da kuma mafaka da wurin ɓuya daga hadari da ruwan sama.
It will be a shelter for shade in the daytime from the heat, and a refuge and a cover from the storm and rain.