< Ishaya 38 >
1 A kwanakin nan sai Hezekiya ya kamu da ciwo ya kuma kusa ya mutu. Annabi Ishaya ɗan Amoz ya tafi wurinsa ya kuma ce, “Ga abin da Ubangiji ya ce ka shirya gidanka, domin za ka mutu; ba za ka warke ba.”
In those days Hezekiah was sick to the point of dying. So Isaiah son of Amoz, the prophet, came to him, and said to him, “Yahweh says, 'Set your house in order; for you will die, not live.'”
2 Hezekiya ya juye fuskarsa wajen bango ya kuma yi addu’a ga Ubangiji,
Then Hezekiah turned his face to the wall and prayed to Yahweh.
3 “Ka tuna, ya Ubangiji, yadda na yi tafiya a gabanka da aminci da dukan zuciya na kuma yi abin da yake nagari a idanunka.” Sai Hezekiya ya yi kuka mai zafi.
He said, “Please, Yahweh, call to mind how I have faithfully walked before you with my whole heart, and how I have done what was good in your sight.” Then Hezekiah wept loudly.
4 Sai maganar Ubangiji ta zo wa Ishaya cewa,
Then the word of Yahweh came to Isaiah, saying,
5 “Ka tafi ka faɗa wa Hezekiya, ‘Ga abin da Ubangiji Allah na kakanka Dawuda, ya ce na ji addu’arka na kuma ga hawayenka; zan ƙara maka shekaru goma sha biyar ga rayuwarka.
“Go and say to Hezekiah, the leader of my people, 'This is what Yahweh, the God of David your ancestor, says: I have heard your prayer, and I have seen your tears. See, I am about to add fifteen years to your life.
6 Zan kuwa cece ka da wannan birni daga hannun sarkin Assuriya. Zan kiyaye wannan birni.
Then I will rescue you and this city from the hand of the king of Assyria, and I will defend this city.
7 “‘Ga alamar Ubangiji gare ka cewa Ubangiji zai aikata kamar yadda ya yi alkawari.
This will be the sign to you from Yahweh, that I will do what I have promised.
8 Zan sa inuwar da rana ta yi a kan matakalar Ahaz ta koma baya da taki goma.’” Saboda haka inuwar ta koma da baya daga fuskar rana har taki goma.
Look, I will cause the shadow on the stairs of Ahaz to go back ten steps.'” So the shadow went back ten steps of the stairs on which it had advanced.
9 Rubutun Hezekiya sarkin Yahuda bayan ciwonsa da kuma warkarwarsa.
This was the written prayer of Hezekiah king of Judah, when he had been sick and then recovered:
10 Na ce, “Cikin tsakiyar rayuwata dole in bi ta ƙofofin mutuwa a kuma raba ni da sauran shekaruna?” (Sheol )
“I said that halfway through my life I will go through the gates of Sheol; I am sent there for the rest of my years. (Sheol )
11 Na ce, “Ba zan ƙara ganin Ubangiji ba, Ubangiji a ƙasa ta masu rai; ba zan ƙara ga wani mutum, ko in kasance tare da waɗanda suke zama a wannan duniya ba.
I said that I will no longer see Yahweh, Yahweh in the land of the living; I will no longer look on mankind or the inhabitants of the world.
12 Kamar tentin makiyayi an rushe gidana aka kuma ƙwace ta daga gare ni. Kamar mai saƙa, na nannaɗe rayuwata, ya kuma yanke ni daga sandar saƙa; dare da rana ka kawo ni ga ƙarshe.
My life is removed and carried away from me like a shepherd's tent; I have rolled up my life like a weaver; you are cutting me off from the loom; between day and night you are ending my life.
13 Na yi jira da haƙuri har safiya, amma kamar zaki ya kakkarya ƙasusuwana duka; dare da rana ka kawo ni ga ƙarshe.
I cried out until the morning; like a lion he breaks all my bones. Between day and night you are ending my life.
14 Na yi kuka kamar mashirare ko zalɓe, na yi kuka kamar kurciya mai makoki. Idanuna suka rasa ƙarfi yayinda na duba sammai. Na damu; Ya Ubangiji, ka taimake ni!”
Like a swallow I chirp; I coo like a dove; my eyes grow tired with looking upward. Lord, I am oppressed; help me.
15 Amma me zan ce? Ya riga ya yi mini magana, shi kansa ne kuma ya aikata. Zan yi tafiya da tawali’u dukan kwanakina saboda wahalar raina.
What shall I say? He has both spoken to me, and has done it; I will walk slowly all my years because I am overcome with grief.
16 Ubangiji, ta waɗannan abubuwa ne mutane suke rayuwa; ruhuna kuma yana samun rai a cikinsu shi ma. Ka maido mini da lafiya ka kuma sa na rayu.
Lord, the sufferings you send are good for me; may my life be given back to me; you have restored my life and health.
17 Tabbatacce wannan kuwa saboda ribata ne cewa in sha irin wahalan nan. Cikin ƙaunarka ka kiyaye ni daga ramin hallaka; ka sa dukan zunubaina a bayanka.
It was for my benefit that I experienced such grief. You have rescued me from the pit of destruction; for you have thrown all my sins behind your back.
18 Gama kabari ba zai yabe ka ba, matattu ba za su rera yabonka ba; waɗanda suka gangara zuwa rami ba za su sa zuciya ga amincinka ba. (Sheol )
For Sheol does not thank you; death does not praise you; those who go down into the pit do not hope in your trustworthiness. (Sheol )
19 Masu rai, masu rai, su suke yabonka, kamar yadda nake yi a yau; iyaye za su faɗa wa’ya’yansu game da amincinka.
The living person, the living person, he is the one who gives you thanks, as I do this day; a father makes known to children your trustworthiness.
20 Ubangiji zai cece ni, za mu kuma rera da kayan kiɗi masu tsirkiya dukan kwanakinmu a cikin haikalin Ubangiji.
Yahweh is about to save me, and we will celebrate with music all the days of our lives in the house of Yahweh.”
21 Ishaya ya riga ya ce, “Ku shirya curin da aka yi da’ya’yan ɓaure ku kuma shafa a marurun, zai kuwa warke.”
Now Isaiah had said, “Let them take a lump of figs and put it on the boil, and he will recover.”
22 Hezekiya ya riga ya yi tambaya ya ce, “Me zai zama alama ta cewa zan haura zuwa haikalin Ubangiji?”
Hezekiah also had said, “What will be the sign that I should go up to the house of Yahweh?”