< Ishaya 37 >

1 Sa’ad da Sarki Hezekiya ya ji haka, sai ya kyakkece rigunansa ya kuma sanya tsummoki ya tafi ya shiga haikalin Ubangiji.
ויהי כשמע המלך חזקיהו ויקרע את בגדיו ויתכס בשק ויבא בית יהוה
2 Ya aiki Eliyakim sarkin fada, Shebna magatakarda da kuma manyan firistoci, duka sanye da tsummoki, wurin Ishaya ɗan Amoz.
וישלח את אליקים אשר על הבית ואת שבנא הסופר ואת זקני הכהנים מתכסים בשקים--אל ישעיהו בן אמוץ הנביא
3 Suka faɗa masa cewa, “Ga abin da Hezekiya ya ce wannan rana ce ta baƙin ciki da tsawatawa da shan kunya, sai ka ce sa’ad da’ya’ya kan zo matakin haihuwa sa’an nan a rasa ƙarfin haihuwarsu.
ויאמרו אליו כה אמר חזקיהו יום צרה ותוכחה ונאצה היום הזה כי באו בנים עד משבר וכח אין ללדה
4 Mai yiwuwa Ubangiji Allahnka zai ji maganganun sarkin yaƙin da maigidansa, sarkin Assuriya, ya aika don yă zagi Allah mai rai, ya kuma tsawata masa saboda maganganun da Ubangiji Allahnka ya ji. Saboda haka ka yi addu’a saboda raguwar da suke da rai.”
אולי ישמע יהוה אלהיך את דברי רבשקה אשר שלחו מלך אשור אדניו לחרף אלהים חי והוכיח בדברים אשר שמע יהוה אלהיך ונשאת תפלה בעד השארית הנמצאה
5 Sa’ad da shugabannin Sarki Hezekiya suka zo wurin Ishaya,
ויבאו עבדי המלך חזקיהו--אל ישעיהו
6 sai Ishaya ya ce musu, “Ku faɗa wa maigidanku cewa, ‘Ga abin da Ubangiji ya faɗa. Kada ka ji tsoron abin da ka ji, maganganun nan da bayin sarkin Assuriya suka yi mini saɓo.
ויאמר אליהם ישעיהו כה תאמרון אל אדניכם כה אמר יהוה אל תירא מפני הדברים אשר שמעת אשר גדפו נערי מלך אשור אותי
7 Ka saurara! Zan sa ruhuna a cikinsa saboda sa’ad da ya ji wani labari, zai koma zuwa ƙasarsa, a can kuwa zan sa a kashe shi da takobi.’”
הנני נותן בו רוח ושמע שמועה ושב אל ארצו והפלתיו בחרב בארצו
8 Sa’ad da sarkin yaƙin ya ji cewa sarkin Assuriya ya bar Lakish, sai ya janye ya kuma sami sarki yana yaƙi da Libna.
וישב רבשקה וימצא את מלך אשור נלחם על לבנה כי שמע כי נסע מלכיש
9 To, fa, Sennakerib ya sami labari cewa Tirhaka, mutumin Kush sarkin Masar, yana fitowa don yă yi yaƙi da shi. Sa’ad da ya ji haka, sai ya aiki jakadu zuwa wurin Hezekiya da wannan magana.
וישמע על תרהקה מלך כוש לאמר יצא להלחם אתך וישמע וישלח מלאכים אל חזקיהו לאמר
10 “Ku faɗa wa Hezekiya sarkin Yahuda cewa kada ka bar allahn da ka dogara a kai ya ruɗe ka sa’ad da ya ce, ‘Ba za a ba da Urushalima ga sarkin Assuriya ba.’
כה תאמרון אל חזקיהו מלך יהודה לאמר אל ישאך אלהיך אשר אתה בוטח בו לאמר לא תנתן ירושלם ביד מלך אשור
11 Tabbatacce ka ji abin da sarakunan Assuriya suka aikata ga dukan ƙasashe, suna hallaka su tas. Kai kuwa za ka tsira ne?
הנה אתה שמעת אשר עשו מלכי אשור לכל הארצות--להחרימם ואתה תנצל
12 Allolin al’umman da kakannina suka hallaka sun cece su ne, allolin Gozan, Haran, Rezef da kuma na mutanen Eden waɗanda suke zama a Tel Assar?
ההצילו אותם אלהי הגוים אשר השחיתו אבותי את גוזן ואת חרן ורצף ובני עדן אשר בתלשר
13 Ina sarkin Hamat yake, sarkin Arfad fa, sarkin Sefarfayim, ko na Hena ko na Iffa?”
איה מלך חמת ומלך ארפד ומלך לעיר ספרוים הנע ועוה
14 Hezekiya ya karɓi wasiƙar daga jakadun ya karanta ta. Sa’an nan ya haura zuwa haikalin Ubangiji ya shimfiɗa ta a gaban Ubangiji.
ויקח חזקיהו את הספרים מיד המלאכים ויקראהו ויעל בית יהוה ויפרשהו חזקיהו לפני יהוה
15 Sai Hezekiya ya yi addu’a ga Ubangiji ya ce,
ויתפלל חזקיהו אל יהוה לאמר
16 “Ya Ubangiji Allah Maɗaukaki, Allah na Isra’ila, zaune a tsakanin kerubobi, kai kaɗai ne Allah a kan dukan masarautan duniya.
יהוה צבאות אלהי ישראל ישב הכרבים אתה הוא האלהים לבדך לכל ממלכות הארץ אתה עשית את השמים ואת הארץ
17 Ka kasa kunne, ya Ubangiji, ka kuma ji; ka buɗe idanunka, ya Ubangiji, ka kuma gani; ka saurara ga dukan maganganun da Sennakerib ya aika don yă zagi Allah mai rai.
הטה יהוה אזנך ושמע פקח יהוה עינך וראה ושמע את כל דברי סנחריב אשר שלח לחרף אלהים חי
18 “Gaskiya ce, ya Ubangiji, cewa sarakunan Assuriyawa sun mai da dukan waɗannan mutane da ƙasashensu kango.
אמנם יהוה החריבו מלכי אשור את כל הארצות--ואת ארצם
19 Sun jefar da gumakansu cikin wuta suka kuma hallaka su, gama su ba alloli ba ne itace ne kawai da dutse, da hannuwan mutane suka sarrafa.
ונתן את אלהיהם באש כי לא אלהים המה כי אם מעשה ידי אדם עץ ואבן--ויאבדום
20 Yanzu, ya Ubangiji Allahnmu, ka cece mu daga hannunsa, saboda masarautai a duniya su san cewa kai kaɗai ne, ya Ubangiji, Allah.”
ועתה יהוה אלהינו הושיענו מידו וידעו כל ממלכות הארץ כי אתה יהוה לבדך
21 Sa’an nan Ishaya ɗan Amoz ya aika da saƙo wa Hezekiya cewa, “Ga abin da Ubangiji, Allah na Isra’ila, ya faɗa. Saboda ka yi addu’a gare ni game da Sennakerib sarkin Assuriya,
וישלח ישעיהו בן אמוץ אל חזקיהו לאמר כה אמר יהוה אלהי ישראל אשר התפללת אלי אל סנחריב מלך אשור
22 ga abin da maganar Ubangiji ya faɗa a kansa, “Budurwa Diyar Sihiyona ta rena tana kuma maka ba’a. Diyar Urushalima tana kada kai yayinda kake gudu.
זה הדבר אשר דבר יהוה עליו בזה לך לעגה לך בתולת בת ציון--אחריך ראש הניעה בת ירושלם
23 Wane ne ka zargi ka kuma yi wa saɓo? A kan wa ka tā da muryarka ka kuma daga idanu cikin fariya? A kan Mai Tsarkin nan na Isra’ila!
את מי חרפת וגדפת ועל מי הרימותה קול ותשא מרום עיניך אל קדוש ישראל
24 Ta wurin jakadunka ka jibge zage-zage a kan Ubangiji. Ka kuma ce, ‘Da kekunan yaƙina masu yawa na hau ƙwanƙolin duwatsu, ƙwanƙolin mafi tsayi na Lebanon. Na sassare al’ul mafi tsayi fir mafi kyau. Na kai can wuri mafi nisa na kurminsa.
ביד עבדיך חרפת אדני ותאמר ברב רכבי אני עליתי מרום הרים ירכתי לבנון ואכרת קומת ארזיו מבחר ברשיו ואבוא מרום קצו יער כרמלו
25 Na haƙa rijiyoyi a baƙuwar ƙasa na kuma sha ruwa a can. Da tafin ƙafafuna na busar da dukan rafuffukan Masar.’
אני קרתי ושתיתי מים ואחרב בכף פעמי כל יארי מצור
26 “Ba ka ji ba cewa tun dā can na shirya ya zama haka? A kwanakin dā na kafa shi; yanzu na sa ya faru, cewa ka mai da birane masu mafaka zuwa tsibin ɓuraguzai.
הלוא שמעת למרחוק אותה עשיתי מימי קדם ויצרתיה עתה הבאתיה--ותהי להשאות גלים נצים ערים בצרות
27 Mutanensu, suka rasa ƙarfi, sun firgita suka kuma sha kunya. Suka zama kamar tsire-tsire a gona, kamar tsire-tsiren ta suka tohu, kamar ciyawar da ya tsiro a kan rufi, wadda zafi ya yi wa ƙuna kafin tă yi girma.
וישביהן קצרי יד חתו ובשו היו עשב שדה וירק דשא חציר גגות ושדמה לפני קמה
28 “Amma na san inda kake zama da sa’ad da kakan fita ka kuma koma da yadda ka harzuƙa gāba da ni.
ושבתך וצאתך ובואך ידעתי ואת התרגזך אלי
29 Saboda ka harzuƙa gāba da ni kuma saboda girmankanka ya kai kunnuwana, zan sa ƙugiya a hancinka linzamina a bakinka, zan kuma sa ka koma ta hanyar da ka zo.
יען התרגזך אלי ושאננך עלה באזני--ושמתי חחי באפך ומתגי בשפתיך והשיבתיך בדרך אשר באת בה
30 “Wannan zai zama alama gare ka, ya Hezekiya, “Wannan shekara za ka ci abin da ya yi girma da kansa, shekara ta biyu kuma abin da ya tsiro daga wancan. Amma a shekara ta uku za ka yi shuki ka kuma girba, za ka dasa gonakin inabi ka kuma ci’ya’yansu.
וזה לך האות--אכול השנה ספיח ובשנה השנית שחיס ובשנה השלישית זרעו וקצרו ונטעו כרמים--ואכול (ואכלו) פרים
31 Sauran da suka rage na gidan Yahuda kuwa za su yi saiwa a ƙarƙashi su kuma ba da’ya’ya a bisa.
ויספה פליטת בית יהודה הנשארה--שרש למטה ועשה פרי למעלה
32 Gama daga Urushalima raguwa za tă fito, kuma daga Dutsen Sihiyona ƙungiyar waɗanda suka tsira. Himmar Ubangiji Maɗaukaki zai cika wannan.
כי מירושלם תצא שארית ופליטה מהר ציון קנאת יהוה צבאות תעשה זאת
33 “Saboda haka ga abin da Ubangiji yana cewa game da sarkin Assuriya, “Ba zai shiga wannan birni ba ya harbe kibiya a nan. Ba zai zo gabansa da garkuwa ba ko ya gina mahaurai kewaye a kansa ba.
לכן כה אמר יהוה אל מלך אשור לא יבוא אל העיר הזאת ולא יורה שם חץ ולא יקדמנה מגן ולא ישפך עליה סללה
34 Ta hanyar da ya zo da ita zai koma; ba zai shiga wannan birni ba,” in ji Ubangiji.
בדרך אשר בא בה ישוב ואל העיר הזאת לא יבוא נאם יהוה
35 “Zan kāre wannan birni in kuma cece shi, saboda girmana da kuma saboda sunan Dawuda bawana!”
וגנותי על העיר הזאת להושיעה--למעני ולמען דוד עבדי
36 Sai mala’ikan Ubangiji ya fita ya kuma karkashe mutane dubu ɗari da dubu tamanin da dubu biyar a sansanin Assuriya. Sa’ad da mutane suka farka kashegari, sai ga gawawwaki duk a kwance!
ויצא מלאך יהוה ויכה במחנה אשור מאה ושמנים וחמשה אלף וישכימו בבקר והנה כלם פגרים מתים
37 Saboda haka Sennakerib sarkin Assuriya ya janye. Ya koma zuwa Ninebe ya zauna a can.
ויסע וילך וישב סנחריב מלך אשור וישב בנינוה
38 Wata rana, yayinda yake yin sujada a haikalin allahnsa Nisrok,’ya’yansa maza Adrammelek da Sharezer suka kashe shi da takobi, suka kuma gudu zuwa ƙasar Ararat. Esar-Haddon ɗansa kuwa ya gāje shi a matsayin sarki.
ויהי הוא משתחוה בית נסרך אלהיו ואדרמלך ושראצר בניו הכהו בחרב והמה נמלטו ארץ אררט וימלך אסר חדן בנו תחתיו

< Ishaya 37 >