< Ishaya 34 >

1 Ku zo kusa, ku al’ummai, ku kuwa saurara ku kasa kunne, ku mutane! Bari duniya ta ji, da kuma dukan abin da yake cikinta, duniya, da dukan abin da yake fitowa daga gare ta!
קרבו גוים לשמע ולאמים הקשיבו תשמע הארץ ומלאה תבל וכל צאצאיה׃
2 Ubangiji yana fushi da dukan al’ummai; hasalarsa tana a kan mayaƙansu. Zai hallaka su tas, zai ba da su a karkashe.
כי קצף ליהוה על כל הגוים וחמה על כל צבאם החרימם נתנם לטבח׃
3 Za a jefar da waɗanda aka kashe gawawwakinsu za su yi wari; duwatsu za su jiƙu da jininsu.
וחלליהם ישלכו ופגריהם יעלה באשם ונמסו הרים מדמם׃
4 Za a tumɓuke dukan taurarin sammai za a kuma nannaɗe sararin sama kamar littafi; dukan rundunar sama za su fāffāɗi kamar ganyayen da suka yanƙwane daga kuringa, kamar’ya’yan ɓauren da suka bushe daga itacen ɓaure.
ונמקו כל צבא השמים ונגלו כספר השמים וכל צבאם יבול כנבל עלה מגפן וכנבלת מתאנה׃
5 Takobina ya sha zararsa a cikin sammai; duba, ya sauko cikin hukunci a kan Edom, mutanen da zan hallaka tas.
כי רותה בשמים חרבי הנה על אדום תרד ועל עם חרמי למשפט׃
6 Takobin Ubangiji ya jiƙu da jini, ya rufu da kitse, jinin raguna da na awaki, kitse daga ƙodar raguna. Gama Ubangiji ya yi hadayar Bozra da kuma babban kisa a Edom.
חרב ליהוה מלאה דם הדשנה מחלב מדם כרים ועתודים מחלב כליות אילים כי זבח ליהוה בבצרה וטבח גדול בארץ אדום׃
7 Babban bijimin jeji zai fāɗi tare da su, maruƙan bijimi da manyan bijimai. Ƙasarsu za tă cika da jini, ƙura kuma zai cika da kitse.
וירדו ראמים עמם ופרים עם אבירים ורותה ארצם מדם ועפרם מחלב ידשן׃
8 Gama Ubangiji yana da ranar ɗaukar fansa, shekarar ramuwa, don biya wa Sihiyona bukata.
כי יום נקם ליהוה שנת שלומים לריב ציון׃
9 Za a mai da rafuffukan Edom rami, ƙurarta za tă zama kibiritun farar wuta; ƙasarta za tă zama rami mai ƙuna!
ונהפכו נחליה לזפת ועפרה לגפרית והיתה ארצה לזפת בערה׃
10 Ba za a kashe ta ba dare da rana; hayaƙinta za tă yi ta tashi har abada. Daga tsara zuwa tsara za tă zama kango; babu wani da zai ƙara wucewa ta wurin.
לילה ויומם לא תכבה לעולם יעלה עשנה מדור לדור תחרב לנצח נצחים אין עבר בה׃
11 Mujiyar hamada da mujiya mai kuka za su mallake ta; babban mujiya da hankaka za su yi sheƙa a can. Allah zai miƙe a kan Edom magwajin bala’i da ma’aunin kango.
וירשוה קאת וקפוד וינשוף וערב ישכנו בה ונטה עליה קו תהו ואבני בהו׃
12 Sarakunanta ba za su kasance da wani abin da ake kira masarauta ba, dukan sarakunanta za su ɓace.
חריה ואין שם מלוכה יקראו וכל שריה יהיו אפס׃
13 Ƙayayuwa za su mamaye fadodinta ƙayayyuwa da sarƙaƙƙiya za su cika kagaranta. Za tă zama mazaunin diloli da gida don mujiyoyi.
ועלתה ארמנתיה סירים קמוש וחוח במבצריה והיתה נוה תנים חציר לבנות יענה׃
14 Halittun hamada za su sadu da kuraye, awakin jeji za su yi ta kiran juna; a can halittun dare su ma za su huta su kuma nemi wurin hutu wa kansu.
ופגשו ציים את איים ושעיר על רעהו יקרא אך שם הרגיעה לילית ומצאה לה מנוח׃
15 Mujiya za tă yi sheƙa a can ta zuba ƙwai; za tă ƙyanƙyashe su, ta kuma kula da’ya’yanta a inuwar fikafikanta; a can kuma shirwa za su taru, kowa da abokinsa.
שמה קננה קפוז ותמלט ובקעה ודגרה בצלה אך שם נקבצו דיות אשה רעותה׃
16 Duba a cikin littafin Ubangiji ka kuma karanta. Babu wani a cikin waɗannan da ya ɓace, babu ko ɗaya da ba ta da abokiya. Gama bakinsa ne ya ba da umarni, Ruhunsa kuma zai tara su wuri ɗaya.
דרשו מעל ספר יהוה וקראו אחת מהנה לא נעדרה אשה רעותה לא פקדו כי פי הוא צוה ורוחו הוא קבצן׃
17 Ya ba su rabonsu; hannunsa ya rarraba musu ta wurin awo. Za su mallake ta har abada su kuma zauna a can daga tsara zuwa tsara.
והוא הפיל להן גורל וידו חלקתה להם בקו עד עולם יירשוה לדור ודור ישכנו בה׃

< Ishaya 34 >