< Ishaya 33 >

1 Kaitonka, ya kai mai hallakarwa, kai da ba a hallakar da kai ba! Kaitonka, ya maciya amana, kai da ba a ci amanarka ba! Sa’ad da ka daina hallakarwa, za a hallaka ka; sa’ad da ka daina cin amana, za a ci amanarka.
הוי שודד ואתה לא שדוד ובוגד ולא בגדו בו כהתמך שודד תושד כנלתך לבגד יבגדו בך׃
2 Ya Ubangiji, ka yi mana jinƙai; muna marmarinka. Ka zama ƙarfinmu kowace safiya, cetonmu a lokacin damuwa.
יהוה חננו לך קוינו היה זרעם לבקרים אף ישועתנו בעת צרה׃
3 Da tsawar muryarka, mutane za su gudu; sa’ad da ka tashi, al’ummai za su watse.
מקול המון נדדו עמים מרוממתך נפצו גוים׃
4 Ganimarku, ya al’ummai ƙanana fāri sun girbe; kamar tarin fārin da mutane sun fāɗa wa.
ואסף שללכם אסף החסיל כמשק גבים שוקק בו׃
5 Ubangiji da girma yake, gama yana zaune a bisa; zai cika Sihiyona cikin gaskiya da adalci.
נשגב יהוה כי שכן מרום מלא ציון משפט וצדקה׃
6 Zai zama tabbataccen harsashi na koyaushe, ma’ajin ceto da hikima da sani a yalwace; tsoron Ubangiji shi ne mabuɗin wannan dukiya.
והיה אמונת עתיך חסן ישועת חכמת ודעת יראת יהוה היא אוצרו׃
7 Duba, jarumawansu suna kuka da ƙarfi a tituna; jakadun salama suna kuka mai zafi.
הן אראלם צעקו חצה מלאכי שלום מר יבכיון׃
8 An gudu an bar manyan hanyoyi, babu matafiye a kan hanyoyi. Aka keta yarjejjeniya, an rena shaidunsa ba a kuwa ganin girman kowa.
נשמו מסלות שבת עבר ארח הפר ברית מאס ערים לא חשב אנוש׃
9 Ƙasa tana kuka an kuma gudu an bar ta, Lebanon ta sha kunya ta kuma yanƙwane; Sharon ta zama kamar Araba, Bashan da Karmel sun kakkaɓe ganyayensu.
אבל אמללה ארץ החפיר לבנון קמל היה השרון כערבה ונער בשן וכרמל׃
10 “Yanzu zan tashi,” in ji Ubangiji. “Yanzu ne za a ɗaukaka ni; yanzu za a ɗaga ni sama.
עתה אקום יאמר יהוה עתה ארומם עתה אנשא׃
11 Kun yi cikin yayi, kuka haifi kara; numfashinku wuta ne da zai cinye ku.
תהרו חשש תלדו קש רוחכם אש תאכלכם׃
12 Za a ƙone mutane kamar da ƙuna farar ƙasa; kamar ƙayayyuwan da aka sare aka kuma sa musu wuta.”
והיו עמים משרפות שיד קוצים כסוחים באש יצתו׃
13 Ku da kuke da nesa, ku ji abin da na yi; ku da kuke kusa, ku san ikona!
שמעו רחוקים אשר עשיתי ודעו קרובים גברתי׃
14 Masu zunubi a Sihiyona sun firgita; rawar jiki ya kama marasa sanin Allah suna cewa, “Wane ne a cikinmu zai iya zama da wuta mai ci? Wane ne a cikinmu zai iya zama da madawwamiyar ƙonewa?”
פחדו בציון חטאים אחזה רעדה חנפים מי יגור לנו אש אוכלה מי יגור לנו מוקדי עולם׃
15 Shi da yake tafiya cikin adalci yana kuma magana abin da yake daidai, wanda yake ƙin riba daga cuta yana kuma kiyaye hannunsa daga karɓan cin hanci, wanda yake hana kunnuwansa daga ƙulla kisa ya kuma rufe idanunsa a kan tunanin aikata mugunta,
הלך צדקות ודבר מישרים מאס בבצע מעשקות נער כפיו מתמך בשחד אטם אזנו משמע דמים ועצם עיניו מראות ברע׃
16 shi ne mutumin da zai zauna a bisa, wanda mafakarsa za tă zama kagarar dutse. Za a tanada abincinsa, kuma ruwa ba zai kāsa masa ba.
הוא מרומים ישכן מצדות סלעים משגבו לחמו נתן מימיו נאמנים׃
17 Idanunku za su ga sarki a cikin kyansa ku kuma hangi ƙasar da take shimfiɗe can da nisa.
מלך ביפיו תחזינה עיניך תראינה ארץ מרחקים׃
18 Cikin tunaninku za ku yi tunani firgitar da ta faru tun dā kuna cewa, “Ina hafsan nan? Ina wannan wanda yake karɓar haraji? Ina hafsan da yake lura da hasumiyoyi?”
לבך יהגה אימה איה ספר איה שקל איה ספר את המגדלים׃
19 Ba za ku ƙara ganin waɗannan mutane masu girman kai kuma ba, waɗannan mutane masu magana da harshen da ba ku fahimta ba.
את עם נועז לא תראה עם עמקי שפה משמוע נלעג לשון אין בינה׃
20 Ku duba Sihiyona, birnin shagulgulanmu; idanunku za su ga Urushalima, mazauni mai lafiya, tentin da ba za a taɓa gusar ba; wanda ba a taɓa tumɓuke turakunsa ba, ko a tsinke igiyoyinta.
חזה ציון קרית מועדנו עיניך תראינה ירושלם נוה שאנן אהל בל יצען בל יסע יתדתיו לנצח וכל חבליו בל ינתקו׃
21 A can Ubangiji zai zama Mai Iko Duka namu. Zai zama kamar inda manyan koguna da rafuffuka suke. Matuƙan jirgin ruwa ba za su kai wurinsu ba, manyan jiragen ruwa ba za su yi zirga-zirga a kansu ba.
כי אם שם אדיר יהוה לנו מקום נהרים יארים רחבי ידים בל תלך בו אני שיט וצי אדיר לא יעברנו׃
22 Gama Ubangiji ne alƙalinmu, Ubangiji ne mai ba mu dokoki, Ubangiji ne sarkinmu; shi ne wanda zai cece mu.
כי יהוה שפטנו יהוה מחקקנו יהוה מלכנו הוא יושיענו׃
23 Maɗaurinku sun kunce ƙarfafan itacen jirgin ba su da kāriya, fikafikan jirgin ba su buɗu ba. Ta haka za a raba yalwar ganima har ma guragu za su kwashe ganimar.
נטשו חבליך בל יחזקו כן תרנם בל פרשו נס אז חלק עד שלל מרבה פסחים בזזו בז׃
24 Ba wani mazauna a Sihiyona da zai ce, “Ina ciwo”; za a kuma gafarta zunuban waɗanda suke zama a can.
ובל יאמר שכן חליתי העם הישב בה נשא עון׃

< Ishaya 33 >