< Ishaya 32 >
1 Duba, sarki zai yi mulki cikin adalci masu mulki kuma su yi mulki da adalci.
For, behold, a righteous king shall reign, and princes shall govern with judgment.
2 Kowane mutum zai zama kamar wurin fakewa daga iska mafaka kuma daga hadari, kamar rafuffukan ruwa a hamada da kuma inuwar babban dutse a ƙeƙasasshiyar ƙasa.
And a man shall hide his words, and be hidden, as from rushing water, and shall appear in Sion as a rushing river, glorious in a thirsty land.
3 Sa’an nan idanun waɗanda suka gani ba za su ƙara rufewa ba, kunnuwan waɗanda suka ji kuma za su saurara.
And they shall no more trust in men, but they shall incline their ears to hear.
4 Zuciya marasa haƙuri za su sani su kuma fahimta, harshen masu ana’ana kuma zai sāke su yi magana sosai.
And the heart of the weak ones shall attend to hear, and the stammering tongues shall soon learn to speak peace.
5 Ba za a ƙara ce da wawa mai girma ba ko kuwa a ɗaukaka mazambaci.
And they shall no more at all tell a fool to rule, and your servants shall no more at all say, Be silent.
6 Gama wawa maganar wauta yakan yi, zuciyarsa ta cika da mugunta, yana aikata abubuwan rashin sanin Allah yana baza kurakurai game da Ubangiji; yana barin mayunwata da yunwa ya kuma hana masu ƙishirwa ruwan sha.
For the fool shall speak foolish words, and his heart shall meditate vanities, and to perform lawless deeds and to speak error against the Lord, to scatter hungry souls, and he will cause the thirsty souls to be empty.
7 Matakan mazambaci mugaye ne, yana ƙulla mugayen shirye-shirye don yă hallaka talakawa da ƙarairayi, ko sa’ad da roƙon mai bukata da gaskiya ne.
For the counsel of the wicked will devise iniquity, to destroy the poor with unjust words, and ruin the cause of the poor in judgment.
8 Amma mutumin kirki kan yi shirye-shirye masu kirki, kuma yakan tsaya a kan ayyukan kirki.
But the godly have devised wise [measures], and this counsel shall stand.
9 Ku matan da kuke zaman jin daɗi, ku tashi ku saurare ni; ku’yan matan da kuke tsammani kuna da kāriya, ku ji abin da zan faɗa!
Rise up, you rich women, and hear my voice; you confident daughters, listen to my words.
10 Cikin ɗan lokaci ƙasa da shekara guda ku da kuke tsammani kuna da kāriya za ku yi rawar jiki; girbin’ya’yan inabi zai kāsa, girbin’ya’yan itatuwa kuma ba zai zo ba.
Remember for a full year in pain, yet with hope: the vintage has been cut off; it has ceased, it shall by no means come again.
11 Ku yi rawar jiki, ku mata masu jin daɗi, ku sha wahala, ku’yan matan da kuke tsammani kuna da kāriya! Ku tuɓe rigunanku, ku ɗaura tsummoki a kwankwasonku.
Be amazed, be pained, you confident ones: strip you, bare yourselves, gird your loins;
12 Ku bugi ƙirjinku don gonaki masu kyau don’ya’yan inabi
and beat your breasts, because of the pleasant field, and the fruit of the vine.
13 da kuma don ƙasar mutanena, da ƙasar da ƙayayyuwa da sarƙaƙƙiya ne suka yi girma, I, ku yi kuka saboda dukan gidajen da dā ake biki da kuma domin wannan birnin da dā ake murna a ciki.
[As for] the land of my people, the thorn and grass shall come upon [it], and joy shall be removed from every house.
14 Za a ƙyale kagarar, a gudu a bar birnin da dā ake hayaniya; mafaka da hasumiyar tsaro za su zama kango har abada, jin daɗin jakuna, makiyaya don garkuna,
[As for] the rich city, the houses are deserted; they shall abandon the wealth of the city, [and] the pleasant houses: and the villages shall be caves for ever, the joy of wild asses, shepherds' pastures;
15 sai an zubo Ruhu a kanmu daga sama, hamada kuma ta zama ƙasar mai taƙi, gona mai taƙi kuma ta zama kamar kurmi.
until the Spirit shall come upon you from on high, and Chermel shall be desert, and Chermel shall be counted for a forest.
16 Aikin gaskiya zai zauna a hamada adalci kuma zai zauna a ƙasa mai taƙi.
Then judgment shall abide in the wilderness, and righteousness shall dwell in Carmel.
17 Aikin adalci zai zama salama; tasirin adalci zai zama natsuwa da tabbaci har abada.
And the works of righteousness shall be peace; and righteousness shall ensure rest, and [the righteous] shall be confident for ever.
18 Mutanena za su zauna lafiya a wuraren salama, a gidaje masu kāriya, a wuraren hutun da babu fitina.
And his people shall inhabit a city of peace, and dwell in [it] in confidence, and they shall rest with wealth.
19 Ko da yake ƙanƙara za tă fāɗo a jeji, a kuma rurrushe birni gaba ɗaya,
And if the hail should come down, it shall not come upon you; and they that dwell in the forests shall be in confidence, as those in the plain country.
20 zai zama muku da albarka, ku da kuke shuki iri kusa da kowane rafi, kuna kuma barin lafiyayyiyar makiyaya domin shanu da jakunanku.
Blessed are they that sow by every water, where the ox and ass tread.