< Ishaya 31 >
1 Kaiton waɗanda suka gangara zuwa Masar don neman taimako, waɗanda suke dogara ga dawakai, waɗanda suke dogara ga yawan kekunan yaƙinsu da kuma a girman ƙarfin mahayan dawakansu, amma ba sa dogara ga Mai Tsarkin nan na Isra’ila, ko ya nemi taimako daga Ubangiji.
2 Shi ma yana da hikima kuma zai iya kawo masifa; ba ya janye kalmominsa. Zai yi gāba da gidan mugu, gāba da waɗanda suke taimakon masu aikata mugunta.
3 Amma Masarawa mutane ne ba Allah ba; dawakansu nama da jini ne ba ruhu ba. Sa’ad da Ubangiji ya miƙa hannunsa, shi da yake taimako zai yi tuntuɓe shi da aka taimaka zai fāɗi; dukansu biyu za su hallaka tare.
4 Ga abin da Ubangiji ya faɗa mini, “Kamar yadda zaki kan yi ruri babban zaki a kan abin da ya yi farauta, kuma ko da yake dukan ƙungiyar makiyaya sun taru wuri ɗaya a kansa, ba zai jijjigu ta wurin ihunsu ba ko ya damu da kiraye-kirayensu, ta haka Ubangiji Maɗaukaki zai sauko don yă yi yaƙi a kan Dutsen Sihiyona da kuma a kan ƙwanƙolinsa.
5 Kamar tsuntsaye masu shawagi a sama haka Ubangiji Maɗaukaki zai kiyaye Urushalima; zai kāre ta ya kuma fanshe ta, zai ‘ƙetare’ ta ya kuma kuɓutar da ita.”
6 Ku dawo gare shi ku da kuka yi masa babban tayarwa, ya Isra’ilawa.
7 Gama a wannan rana kowannenku zai ƙi gumakan azurfa da zinariya da hannuwanku masu zunubi suka yi.
8 “Za a karkashe Assuriyawa da takobin da ba na yin mutum ba; takobi, da ba na yin mutum ba, zai cinye. Za su gudu daga takobi za a kuma sa samarinsu aikin dole.
9 Kagararsu za tă fāɗi saboda razana; da ganin matsayin yaƙin, shugabannin yaƙinsu za su firgita,” in ji Ubangiji, wanda wutarsa tana a Sihiyona, wanda matoyarsa tana a Urushalima.