< Ishaya 3 >
1 Yanzu ka duba fa, Ubangiji, Ubangiji Maɗaukaki, yana shirin yă ɗauke kowane tanadi da taimako daga Urushalima da Yahuda dukan tanade-tanaden abinci da kuma dukan tanade-tanaden ruwa,
2 jarumi, da soja, alƙali da annabi masu duba da dattijo,
3 shugaban sojojin hamsin da mutum mai makami, mai ba da shawara, gwanin sarrafa abubuwa da mai gwanintan dabo.
4 “Zan sa’yan yara su zama shugabanninsu;’yan yara kurum za su yi mulkinsu.”
5 Mutane za su zalunci juna mutum da mutum, maƙwabci da maƙwabci. Yara za su rena tsofaffi, ƙasƙantacce zai rena mai daraja.
6 Mutum zai kama ɗaya daga cikin’yan’uwansa a gidan mahaifinsa ya ce, “Kana da abin sawa, ka zama shugabanmu; wannan kango kuma yă zama a ƙarƙashinka!”
7 Amma a ranan nan zai tā da murya ya ce, “Ba ni ba dai. Ba ni da abinci ko abin sawa a gidana; kada ka mai da ni shugaban mutane.”
8 Urushalima tana tangaɗi, Yahuda yana fāɗuwa; maganganunsu da ayyukansu suna gāba da Ubangiji, suna rena ɗaukakar kasancewarsa.
9 Fuskokinsu shaidu ne a kansu; suna nuna zunubinsu a fili kamar yadda Sodom ya yi; ba sa ma ɓoye shi. Kaitonsu! Sun jawo wa kansu masifa.
10 Ku faɗa wa masu adalci cewa kome zai zama musu da kyau, gama za su ji daɗin aikin da hannuwansu suka yi.
11 Kaiton masu mugunta! Masifa tana a kansu! Za a rama abin da hannuwansu suka yi.
12 Matasa suna zalunta mutanena, mata suna mulki a bisansu. Ya mutanena, jagorarinku suna ɓad da ku; suna karkatar da ku daga hanya.
13 Ubangiji ya ɗauki mazauninsa a cikin ɗakin shari’a; ya tashi don yă shari’anta mutane.
14 Ubangiji yana shari’a da dattawa da kuma shugabannin mutanensa, “Ku ne kuka lalace gonar inabina; ganimar talakawa suna a gidajenku.
15 Ina dalilin da kuke marmatsa mutanena kuna gurgurje fuskokin talakawa?” Ni Ubangiji Maɗaukaki na faɗa.
16 Ubangiji ya ce, “Matan Sihiyona suna da girman kai, suna tafiya da wuya a miƙe, da idanu masu yaudara, suna takawa ɗaya-ɗaya a hankali, da mundaye a ƙafafunsu, suna cas-cas.
17 Saboda haka Ubangiji zai kawo gyambuna a kawunan matan Sihiyona; Ubangiji zai sa a aske kawunansu, a bar su ƙwal.”
18 A wannan rana Ubangiji zai ƙwace abin da suke taƙama da shi, mundayensu, ɗankwalin kansu da abin wuyansu,
19 ’yan kunnensu, kwandagansu da lulluɓinsu,
20 kitsonsu, sarƙar da suke sa wa damatsansu da ɗamararsu, kwalabai turare da layu,
21 da ƙawanen da suka sa a yatsotsinsu da hancinsu,
22 tufafi masu kyau, da manyan rigunansu, da mayafansu, da jakar kuɗinsu
23 da madubi, da kuma tufafin lilin da adikai, da gyale.
24 A maimakon ƙanshi, wari ne za a ji; a maimakon abin ɗamara, igiya ce za a samu; a maimakon kyakkyawan gashi, sanƙo za su kasance da shi a kai; a maimakon tufafi masu kyau, za su sa tsummoki; a maimakon kyau, za su zama munana.
25 Mazanku za su mutu ta wurin takobi, jarumawanku za su mutu a yaƙi.
26 Ƙofofin Sihiyona za su yi makoki su kuma yi kuka; za tă zama wofi, za tă zauna a ƙasa.