< Ishaya 29 >

1 Kaitonki, Ariyel, Ariyel birnin da Dawuda ya zauna! Ƙara shekara ga shekara a kuma bar shagulgulanki su yi ta kewayewa.
[Væ Ariel, Ariel civitas, quam expugnavit David! additus est annus ad annum: solemnitates evolutæ sunt.
2 Duk da haka zan yi wa Ariyel kwanto za tă kuma yi kuka da makoki, za tă zama mini kamar bagaden jini.
Et circumvallabo Ariel, et erit tristis et mœrens, et erit mihi quasi Ariel.
3 Zan kafa sansani kewaye da ke duka; zan kewaye ki da hasumiyoyi in tasar miki da ayyukan kwantona na yaƙi.
Et circumdabo quasi sphæram in circuitu tuo, et jaciam contra te aggerem, et munimenta ponam in obsidionem tuam.
4 Za a ƙasƙantar da ke, za ki ƙi yin magana daga ƙasa; maganarki za tă yi ƙasa-ƙasa daga ƙura. Muryarki za tă zama kamar fatalwa daga ƙasa; daga ƙura maganarki zai fito ƙasa-ƙasa.
Humiliaberis, de terra loqueris, et de humo audietur eloquium tuum; et erit quasi pythonis de terra vox tua, et de humo eloquium tuum mussitabit.
5 Amma abokan gābanki masu yawa za su zama kamar ƙura mai laushi, sojojinsu masu firgitarwa za su yi ta tashi kamar yayin da iska ta hura. Farat ɗaya, cikin ɗan lokaci,
Et erit sicut pulvis tenuis multitudo ventilantium te, et sicut favilla pertransiens multitudo eorum qui contra te prævaluerunt;
6 Ubangiji Maɗaukaki zai zo da tsawa da rawar ƙasa da ƙara mai girma, da hadarin iska da guguwa da harshe na wuta mai ci.
eritque repente confestim. A Domino exercituum visitabitur in tonitruo, et commotione terræ, et voce magna turbinis et tempestatis, et flammæ ignis devorantis.
7 Sa’an nan sojojin dukan al’umman da suka yi yaƙi da Ariyel, da suka fāɗa mata da kagararta suka kuma yi mata kwanto, za su zama kamar yadda yake da mafarki, wahayi da dare,
Et erit sicut somnium visionis nocturnæ multitudo omnium gentium quæ dimicaverunt contra Ariel, et omnes qui militaverunt, et obsederunt, et prævaluerunt adversus eam.
8 kamar sa’ad da mai yunwa yana mafarki cewa yana cin abinci, amma sai ya farka, yunwan tana nan; kamar sa’ad da mai ƙishirwa yana mafarki cewa yana shan ruwa, amma sai ya farka yana suma, da ƙishinsa. Haka zai zama da sojoji na dukan al’ummai da suka yi yaƙi da Dutsen Sihiyona.
Et sicut somniat esuriens, et comedit, cum autem fuerit expergefactus, vacua est anima ejus; et sicut somniat sitiens et bibit, et postquam fuerit expergefactus, lassus adhuc sitit, et anima ejus vacua est: sic erit multitudo omnium gentium quæ dimicaverunt contra montem Sion.
9 Ku firgita ku kuma yi mamaki, ku makance kanku ku kuma zama a makance; ku bugu, amma ba da ruwan inabi ba, ku yi tangaɗi, amma ba daga barasa ba.
Obstupescite et admiramini; fluctuate et vacillate; inebriamini, et non a vino; movemini, et non ab ebrietate.
10 Ubangiji ya kawo muku barci mai nauyi, Ya rufe idanunku (annabawa); ya rufe kawunanku (masu duba).
Quoniam miscuit vobis Dominus spiritum soporis; claudet oculos vestros: prophetas et principes vestros, qui vident visiones, operiet.
11 Gare ku duk wannan wahayi ba kome ba ne sai dai maganganun da aka rufe a cikin littafi. In kuma kun ba da littafin ga wani wanda zai iya karanta, kuka kuma ce masa, “Karanta wannan, muna roƙonka,” zai amsa ya ce, “Ba zan iya ba; an rufe shi.”
Et erit vobis visio omnium sicut verba libri signati, quem cum dederint scienti litteras, dicent: Lege istum: et respondebit: Non possum, signatus est enim.
12 Ko kuwa in kun ba da littafin ga wani wanda ba zai iya karantawa ba, kuka kuma ce, “Karanta wannan, muna roƙonka,” zai amsa ya ce, “Ban iya karatu ba.”
Et dabitur liber nescienti litteras, diceturque ei: Lege; et respondebit: Nescio litteras.
13 Ubangiji ya ce, “Waɗannan mutane sun zo kusa da ni da bakinsu suka kuma girmama ni da leɓunansu, amma zukatansu suna nesa daga gare ni. Sujadar da suke mini cike take da dokokin da mutane suka koyar.
Et dixit Dominus: Eo quod appropinquat populus iste ore suo, et labiis suis glorificat me, cor autem ejus longe est a me, et timuerunt me mandato hominum et doctrinis,
14 Saboda haka zan firgita waɗannan mutane sau ɗaya da abubuwan banmamaki a kan abubuwan banmamaki; hikimar masu hikima za tă lalace, azancin masu azanci zai ɓace.”
ideo ecce ego addam ut admirationem faciam populo huic miraculo grandi et stupendo; peribit enim sapientia a sapientibus ejus, et intellectus prudentium ejus abscondetur.
15 Kaiton waɗanda suke zuwa manyan zurfafa don su ɓoye shirye-shiryensu daga Ubangiji, waɗanda suke aikinsu cikin duhu su yi tunani, “Wa yake ganinmu? Wa zai sani?”
Væ qui profundi estis corde, ut a Domino abscondatis consilium; quorum sunt in tenebris opera, et dicunt: Quis videt nos? et quis novit nos?
16 Kuna birkitar abubuwa, sai ka ce an mayar da mai ginin tukwane ya zama yumɓu! Abin da aka yi zai ce wa wanda ya yi shi, “Ba shi ne ya yi ni ba”? Tukunya za tă iya ce wa mai ginin tukwane, “Ba ka san kome ba”?
Perversa est hæc vestra cogitatio; quasi si lutum contra figulum cogitet, et dicat opus factori suo: Non fecisti me; et figmentum dicat fictori suo: Non intelligis.
17 Cikin ɗan lokaci, za a mai da Lebanon gona mai taƙi kuma gona mai taƙi za tă zama kamar kurmi?
Nonne adhuc in modico et in brevi convertetur Libanus in carmel, et carmel in saltum reputabitur?
18 A wannan rana kurame za su ji maganganun littafi, daga duruduru da duhu kuma idanun makafi za su gani.
Et audient in die illa surdi verba libri, et de tenebris et caligine oculi cæcorum videbunt.
19 Masu tawali’u za su sāke yin farin ciki a cikin Ubangiji; mabukata za su yi farin ciki cikin Mai Tsarkin nan na Isra’ila.
Et addent mites in Domino lætitiam, et pauperes homines in Sancto Israël exsultabunt;
20 Masu zalunci za su ƙare, masu ba’a za su ɓace, kuma dukan waɗanda suke da ido don mugunta za su hallaka,
quoniam defecit qui prævalebat, consummatus est illusor, et succisi sunt omnes qui vigilabant super iniquitatem,
21 waɗanda ta magana kawai sukan mai da mutum mai laifi, waɗanda suke kafa tarko wa mai ba da kāriya a ɗakin shari’a da shaidar ƙarya kuma su hana marar laifi samun shari’ar adalci.
qui peccare faciebant homines in verbo, et arguentem in porta supplantabant, et declinaverunt frustra a justo.
22 Saboda haka ga abin da Ubangiji wanda ya fanshi Ibrahim, ya ce wa gidan Yaƙub, “Ba za a ƙara kunyata Yaƙub ba; fuskokinsu kuma ba za su ƙara yanƙwanewa ba.
Propter hoc, hæc dicit Dominus ad domum Jacob, qui redemit Abraham: Non modo confundetur Jacob, nec modo vultus ejus erubescet;
23 Sa’ad da suka ga’ya’yansu a tsakiyarsu, aikin hannuwansu, za su kiyaye sunana da tsarki; za su san tsarkin Mai Tsarkin nan na Yaƙub, za su kuma ji tsoron Allah na Isra’ila.
sed cum viderit filios suos, opera manuum mearum in medio sui sanctificantes nomen meum, et sanctificabunt Sanctum Jacob, et Deum Israël prædicabunt;
24 Su da suke marasa azanci a ruhu za su sami fahimtar; waɗanda suke gunaguni za su yarda da koyarwa.”
et scient errantes spiritu intellectum, et mussitatores discent legem.]

< Ishaya 29 >