< Ishaya 28 >
1 Kaito ga wannan rawani, girman kai na mashayan Efraim, ga fure mai yanƙwanewa, darajar kyansa, da aka sa a kan kwari mai ba da amfani, ga birnin nan, wadda take girman kan waɗanda aka ƙasƙantar da ruwan inabinsu!
2 Duba, Ubangiji yana da wanda yake da iko da kuma ƙarfi. Kamar dutsen ƙanƙara da kuma iska mai ɓarna, kamar kwararowar ruwa da rigyawa mai kirmewa, zai jefa shi har ƙasa da ƙarfi.
3 Za a tattaka wannan rawani, girman kai na mashayan Efraim da ƙafa.
4 Wannan fure mai yanƙwanewa, darajarar kyansa, da aka sa a kan kwari mai ba da amfani, zai zama kamar’ya’yan ɓaure, nunan fari, da zarar wani ya gani ya kuma tsinka, zai haɗiye shi.
5 A wannan rana Ubangiji Maɗaukaki zai zama rawani mai daraja kyakkyawan rawani wa mutanensa da suka ragu.
6 Zai zama ruhun adalci gare shi wanda yake zaune a kujerar shari’a, wurin samun ƙarfi ga waɗanda suka kori abokan gāban da suka fāɗa musu da yaƙi a ƙofofi.
7 Da waɗannan kuma masu tangaɗi saboda sun sha ruwan inabi suke jiri don sun sha barasa Firistoci da annabawa suna tangaɗi saboda sun sha barasa sun kuma yi tatur da ruwan inabi; suna jiri saboda sun sha barasa, suna tangaɗi sa’ad da suke ganin wahayi, suna tuntuɓe sa’ad da suke ba da shawara.
8 Duk amai ya rufe teburori kuma babu wani wurin da ba a ɓata ba.
9 “Wane ne yake so ya koyar? Ga wa yake bayyana saƙonsa? Ga yaran da aka yaye, ga waɗanda ba a daɗe da yayewa ba ne?
10 Gama haka yake. Yi ka kuma yi, yi ka kuma yi, mulki a kan mulki, mulki a kan mulki; nan kaɗan, can kaɗan.”
11 To da kyau, da leɓunan baƙi da ku harsunan da ba sani ba Allah zai yi magana da wannan mutane,
12 waɗanda zai ce, “Wannan shi ne wurin hutu, bari waɗanda suka gaji su huta”; da kuma, “Wannan shi ne wurin wartsakewa” amma sun ƙi su saurara.
13 Saboda haka fa, maganar Ubangiji gare su za tă zama, Yi ka kuma yi, yi ka kuma yi, mulki akan mulki, mulki a kan mulki; nan kaɗan, can kaɗan, domin su tafi su kuma fāɗi da baya, su ji rauni a kuma kama su da tarko, a kai su zaman bauta.
14 Saboda haka ku saurari maganar Ubangiji, ku masu ba’a ku da kuke mulkin wannan mutane a Urushalima.
15 Kuna fariya cewa, “Mun yi alkawari da mutuwa, mun kuma yi yarjejjeniya da kabari. Sa’ad da zafi ya ratsa, ba zai taɓa mu ba, gama mun mai da ƙarya mafakarmu ruɗu kuma wurin ɓuyanmu.” (Sheol )
16 Saboda haka ga abin da Ubangiji Mai Iko Duka ya ce, “Duba, na kafa dutse a Sihiyona, dutsen da aka gwada, dutsen kusurwa mai daraja don tabbataccen tushe; wanda ya dogara gare shi ba zai taɓa shan kunya ba.
17 Zan mai da gaskiya igiyar gwaji adalci kuma ɗan katakon gwajin ginin; ƙanƙara za tă share mafakarku, ƙarya, da ruwa kuma za su mamaye maɓuyanku.
18 Za a soke alkawarinku da mutuwa; yarjejjeniyarku da kabari ba zai zaunu ba. Sa’ad da zafi mai ɓarna ya ratsa, zai hallaka ku. (Sheol )
19 A duk sa’ad da ya zo; ko da safiya, ko dare ko kuma da rana, zai yi ta ratsawa yana kwasanku.” Za ku zama kamar mutumin da ya zama abin karin magana,
20 wanda ya yi ƙoƙari yă kwanta a gajeren gado, yă kuma rufa da ɗan siririn bargo.
21 Ubangiji zai tashi kamar yadda ya yi a Dutsen Feratsim, zai tā da kansa kamar a Kwarin Gibeyon don yă aikata aikinsa, aikinsa da ba a saba gani ba, yă kuma yi aikinsa, baƙon aikinsa.
22 Yanzu ku daina ba’arku, in ba haka ba sarƙoƙinku za su ƙara nauyi; Ubangiji, Ubangiji Maɗaukaki, ya faɗa mini game da hallakar da aka ƙaddara a kan dukan ƙasar.
23 Ku saurara ku kuma ji muryata; ku kasa kunne ku kuma ji abin da na faɗa.
24 Sa’ad da manomi ya yi noma don shuki, yakan ci gaba da noma ne? Yakan ci gaba da sara yana yin kunyoyi a ƙasa ne?
25 Sa’ad da ya shirya wuri da kyau, ba yakan shuka kanumfari ya kuma yayyafa ɗaɗɗoya ba? Ba yakan shuka alkama a kunyoyinsa sha’ir a kunyoyinsa, tamba kuma a filinsa ba?
26 Allahnsa ya umarce shi ya kuma koya masa hanyar da take daidai.
27 Ba a bugan kanumfari da ƙaton sanda ko a yi ta jujjuye ƙafar keke a kan ɗaɗɗoya; akan buga kanumfari da siririn sanda ɗaɗɗoya kuma da tsumagiya.
28 Dole a niƙa hatsi don a yi burodi; saboda haka mutum ba zai yi ta bugun alkama, har yă ɓata tsabar ba. Ya san yadda zai sussuke alkamarsa, ba tare da ya ɓata tsabarta ba.
29 Dukan wannan hikimar takan zo daga Ubangiji Maɗaukaki ne, shi da yake mashawarci mai banmamaki, mafifici kuma cikin hikima.