< Ishaya 23 >

1 Abin da Allah ya faɗa game da Taya. Ku yi kuka mai zafi, ya jiragen ruwan Tarshish! Gama an hallaka Taya aka kuma bar su babu gida ko tasha. Daga ƙasar Saifurus magana ta zo musu.
論泰爾的默示: 他施的船隻都要哀號; 因為泰爾變為荒場, 甚至沒有房屋,沒有可進之路。 這消息是從基提地得來的。
2 Ku yi shiru, ku mutanen tsibiri da ku’yan kasuwan Sidon waɗanda masu ciniki a teku suka azurta.
沿海的居民, 就是素來靠航海西頓的商家得豐盛的, 你們當靜默無言。
3 A manyan ruwaye hatsin Shihor suka iso; girbin Nilu ne kuɗin shiga na Taya ta kuma zama kasuwar al’ummai.
在大水之上, 西曷的糧食、 尼羅河的莊稼是泰爾的進項; 她作列國的大碼頭。
4 Ki ji kunya, ya ke Sidon, da ke kuma, kagarar teku, gama teku ya yi magana ya ce, “Ban taɓa naƙuda ba balle in haifi’ya’ya; ban taɓa goyon’ya’ya maza ba balle in reno’ya’ya mata.”
西頓哪,你當慚愧; 因為大海說, 就是海中的保障說: 我沒有劬勞,也沒有生產, 沒有養育男子,也沒有撫養童女。
5 Sa’ad da magana ta kai Masar, za su razana da jin labari daga Taya.
這風聲傳到埃及; 埃及人為泰爾的風聲極其疼痛。
6 Ku haye zuwa Tarshish; ku yi kuka mai zafi, ku mutanen tsibiri.
泰爾人哪,你們當過到他施去; 沿海的居民哪,你們都當哀號。
7 Wannan ce birnin murnanku, birnin nan na tun dā wadda ƙafafunta suka kai ta zama a ƙasashe masu nesa?
這是你們歡樂的城, 從上古而有的嗎? 其中的居民往遠方寄居。
8 Wane ne ya ƙulla wannan a kan Taya ita da take ba da rawanin sarauta, wadda’yan kasuwanta sarakuna ne, wadda masu cinikinta sanannu ne a duniya?
泰爾本是賜冠冕的。 她的商家是王子; 她的買賣人是世上的尊貴人。 遭遇如此是誰定的呢?
9 Ubangiji Maɗaukaki ya ƙulla shi, don yă kawo ƙarshen girman kan dukan darajarta ya kuma ƙasƙantar da dukan waɗanda suke sanannu a duniya.
是萬軍之耶和華所定的! 為要污辱一切高傲的榮耀, 使地上一切的尊貴人被藐視。
10 Ki nome ƙasarki har zuwa wajen Nilu, Ya Diyar Tarshish, gama ba ki da tashan jirgin ruwa kuma.
他施的民哪, 可以流行你的地,好像尼羅河; 不再有腰帶拘緊你。
11 Ubangiji ya miƙa hannunsa a bisa teku ya kuma sa mulkokinsa suka yi rawar jiki. Ya ba da umarni game da Funisiya cewa a hallaka kagararta.
耶和華已經向海伸手, 震動列國。 至於迦南, 他已經吩咐拆毀其中的保障。
12 Ya ce, “Ba za ki ƙara yin murna ba, Ya ke Budurwa Diyar Sidon, yanzu da kike ragargajiya! “Tashi, ki ƙetare zuwa Saifurus; a can ɗin ma ba za ki huta ba.”
他又說:受欺壓西頓的居民哪, 你必不得再歡樂。 起來!過到基提去; 就是在那裏也不得安歇。 (
13 Dubi ƙasar Babiloniyawa, wannan mutanen da yanzu ba su da wani amfani! Assuriyawa sun mai da ita wurin zaman halittun hamada; sun gina hasumiyoyin kwanto, suka ragargaza kagararta ƙaf suka mai da ita kango.
看哪,迦勒底人之地向來沒有這民,這國是亞述人為住曠野的人所立的。現在他們建築戍樓,拆毀泰爾的宮殿,使她成為荒涼。)
14 Ku yi kuka mai zafi, ku jiragen ruwan Tarshish; an rurrushe kagararku!
他施的船隻都要哀號, 因為你們的保障變為荒場。
15 A wannan lokaci za a manta da Taya har shekaru saba’in, tsawon rayuwar sarki. Amma a ƙarshen waɗannan shekaru saba’in, zai zama wa Taya kamar yadda yake a waƙar karuwa cewa,
到那時,泰爾必被忘記七十年,照着一王的年日。七十年後,泰爾的景況必像妓女所唱的歌:
16 “Ɗauki garaya, ki ratsa birni, Ya ke karuwar da aka manta da ita; kaɗa garaya da kyau, ki rera waƙoƙi masu yawa, saboda a tuna da ke.”
你這被忘記的妓女啊, 拿琴周流城內, 巧彈多唱,使人再想念你。
17 A ƙarshen shekaru saba’in, Ubangiji zai magance Taya. Za tă koma ga aikinta na karuwanci za tă kuma yi kasuwancinta da dukan mulkokin duniya.
七十年後,耶和華必眷顧泰爾,她就仍得利息,與地上的萬國交易。
18 Duk da haka za a keɓe ribarta da kuɗin shigarta wa Ubangiji; ba za a yi ajiyarsu ko a ɓoye su. Ribarta za tă tafi ga waɗanda suke yi wa Ubangiji sujada, don su sami yalwataccen abinci da tufafi masu kyau.
她的貨財和利息要歸耶和華為聖,必不積攢存留;因為她的貨財必為住在耶和華面前的人所得,使他們吃飽,穿耐久的衣服。

< Ishaya 23 >