< Ishaya 22 >

1 Abin da Allah ya faɗa game da Kwarin Wahayi. Mene ne ya dame ku a yanzu, da dukanku kuka hau kan rufin gidaje.
This is the burden against the Valley of Vision: What ails you now, that you have all gone up to the rooftops,
2 Ya kai gari cike da hayaniya, Ya ke birnin tashin hankali da alkarya mai murna? Mutanenki ba su mutu ta wurin takobi ba, ba kuwa za su mutu a yaƙi ba.
O city of commotion, O town of revelry? Your slain did not die by the sword, nor were they killed in battle.
3 Dukan shugabanninki sun gudu gaba ɗaya; an kama su ba tare da an yi amfani da baka ba. Dukanku da aka kama an kwashe ku ɗaurarru gaba ɗaya, kun gudu tun abokin gāba yana da nisa.
All your rulers have fled together, captured without a bow. All your fugitives were captured together, having fled to a distant place.
4 Saboda haka na ce, “Ƙyale ni kurum; bari in yi kuka mai zafi. Kada ka yi ƙoƙarin ta’azantar da ni a kan hallakar mutanena.”
Therefore I said, “Turn away from me, let me weep bitterly! Do not try to console me over the destruction of the daughter of my people.”
5 Ubangiji, Ubangiji Maɗaukaki, yana da ranar giggicewa da tattakewa da banrazana a cikin Kwarin Wahayi, ranar ragargazawar katanga da ta yin kuka ga duwatsu.
For the Lord GOD of Hosts has set a day of tumult and trampling and confusion in the Valley of Vision— of breaking down the walls and crying to the mountains.
6 Elam ya ɗauki kwari da baka, tare da mahayan kekunan yaƙinta da dawakai; Kir ta buɗe garkuwoyi.
Elam takes up a quiver, with chariots and horsemen, and Kir uncovers the shield.
7 Kwarurukanku mafi kyau sun cika da kekunan yaƙi, an kuma tsai da mahayan dawakai a ƙofofin birni.
Your choicest valleys are full of chariots, and horsemen are posted at the gates.
8 An rurrushe kāriyar Yahuda, a ranan nan kuwa kun yi la’akari da makamai a cikin Fadan Kurmi;
He has uncovered the defenses of Judah. On that day you looked to the weapons in the House of the Forest.
9 kuka ga cewa Birnin Dawuda tana da wuraren kāriya masu yawa da suka tsattsage; kuka tattara ruwa a Tafkin Ƙasa.
You saw that there were many breaches in the walls of the City of David. You collected water from the lower pool.
10 Kuka ƙirga gine-gine a Urushalima kuka kuma rurrushe gidaje don ku ƙarfafa katanga.
You counted the houses of Jerusalem and tore them down to strengthen the wall.
11 Kuka gina matarar ruwa tsakanin katanga biyu saboda ruwan Tsohon Tafki, amma ba ku yi la’akari da Wannan da ya yi su ba, ko ku kula da Wannan da ya shirya shi tuntuni.
You built a reservoir between the walls for the waters of the ancient pool, but you did not look to the One who made it, or consider Him who planned it long ago.
12 Ubangiji, Ubangiji Maɗaukaki ya kira ku a wannan rana don ku yi kuka ku yi ihu, don ku aske gashinku ku kuma sa tsummoki.
On that day the Lord GOD of Hosts called for weeping and wailing, for shaven heads and the wearing of sackcloth.
13 Amma duba, sai ga shi kuna farin ciki kuna kuma murna, kuna yankan shanu kuna kashe tumaki, kuna cin nama kuna kuma shan ruwan inabi! Kuna cewa, “Bari mu ci mu kuma sha, gama gobe za mu mutu!”
But look, there is joy and gladness, butchering of cattle and slaughtering of sheep, eating of meat and drinking of wine: “Let us eat and drink, for tomorrow we die!”
14 Ubangiji Maɗaukaki ya bayyana wannan a kunnena cewa, “Har ranar mutuwarka ba za a yi kafarar wannan zunubi ba,” in ji mai girma Ubangiji Maɗaukaki.
The LORD of Hosts has revealed in my hearing: “Until your dying day, this sin of yours will never be atoned for,”
15 Ga abin da Ubangiji, Ubangiji Maɗaukaki, ya faɗa, “Je, ka faɗa wa wannan mai hidima, Shebna, sarkin fada.
This is what the Lord GOD of Hosts says: “Go, say to Shebna, the steward in charge of the palace:
16 Mene ne kake yi a nan kuma wa ya ba ka izini ka haƙa kabari wa kanka a nan, kana fafe kabarinka a bisa kana sassaƙa wurin hutunka a dutse?
What are you doing here, and who authorized you to carve out a tomb for yourself here—to chisel your tomb in the height and cut your resting place in the rock?
17 “Ka yi hankali, Ubangiji yana shirin ya kama ka da ƙarfi ya kuma ɗauke ka, ya kai mai ƙarfi.
Look, O mighty man! The LORD is about to shake you violently. He will take hold of you,
18 Zai dunƙule ka kamar ƙwallo ya jefa ka a cikin ƙasa mai girma. A can za ka mutu a can kuma kekunan yaƙinka masu daraja za su kasance, abin kunya kake ga gidan maigidanka!
roll you into a ball, and sling you into a wide land. There you will die, and there your glorious chariots will remain—a disgrace to the house of your master.
19 Zan tumɓuke ka daga makaminka, za a kuma kore ka daga matsayinka.
I will remove you from office, and you will be ousted from your position.
20 “A wannan rana zan kira bawana, Eliyakim ɗan Hilkiya.
On that day I will summon My servant, Eliakim son of Hilkiah.
21 Zan rufe shi da rigarka in kuma yi masa ɗamara in miƙa masa ikonka. Zai zama mahaifi ga waɗanda suke zama a Urushalima da kuma gidan Yahuda.
I will clothe him with your robe and tie your sash around him. I will put your authority in his hand, and he will be a father to the dwellers of Jerusalem and to the house of Judah.
22 Zan sa mabuɗin gidan Dawuda a kafaɗarsa; abin da ya buɗe ba mai rufewa, kuma abin da ya rufe ba mai buɗewa.
I will place on his shoulder the key to the house of David. What he opens no one can shut, and what he shuts no one can open.
23 Zan kafa shi kamar turke a tsayayyen wuri; zai zama mazaunin daraja domin gidan mahaifinsa.
I will drive him like a peg into a firm place, and he will be a throne of glory for the house of his father.
24 Dukan ɗaukakar iyalinsa za tă rataya a kansa daga’ya’yansa da zuriyarsa har zuwa dukan ƙananan kayan aikinsa, wato, daga kwanoni har zuwa tuluna.
So they will hang on him the whole burden of his father’s house: the descendants and the offshoots—all the lesser vessels, from bowls to every kind of jar.
25 “A ranan nan, in ji Ubangiji Maɗaukaki, turken da aka kafa a tsayayyen wuri zai sumɓule; za a sare shi ya fāɗi, za a kuma datse nauyin da yake rataya a kansa.” Ni Ubangiji na faɗa.
In that day, declares the LORD of Hosts, the peg driven into a firm place will give way; it will be sheared off and fall, and the load upon it will be cut down.” Indeed, the LORD has spoken.

< Ishaya 22 >