< Ishaya 20 >

1 A shekarar da babban shugaban yaƙin da Sargon sarkin Assuriya ya aika, ya zo Ashdod ya kuma fāɗa mata ya kuma ci ta da yaƙi,
L'Année en laquelle Tartan, envoyé par Sargon Roi d'Assyrie, vint contre Asdod, et combattit contre Asdod, et la prit.
2 a wannan lokaci Ubangiji ya yi magana ta wurin Ishaya ɗan Amoz. Ya ce masa, “Tuɓe tsummokin da kake saye da su, da kuma takalman da ka sa a ƙafafu.” Ya kuwa yi haka, yana yawo tsirara kuma ba takalma a ƙafa.
En ce temps-là, l'Eternel parla par le ministère d'Esaïe fils d'Amots, en disant; va, et délie le sac de dessus tes reins, et déchausse tes souliers de tes pieds; ce qu'il fit, allant nu et déchaussé.
3 Sa’an nan Ubangiji ya ce, “Kamar dai yadda bawana Ishaya ya yi ta yawo tsirara kuma ba takalmi a ƙafa shekara uku, a matsayin alama da shaida a kan Masar da Kush,
Puis l'Eternel dit; comme mon serviteur Esaïe a marché nu et déchaussé, ce qui est un signe et un prodige contre l'Egypte et contre Chus pour trois années;
4 haka sarkin Assuriya zai kwashe kamammun Masarawa da Kushawa tsirara kuma ba takalma a ƙafa, yaro da babba, asirinsu a tsiraice, don a kunyata Masar.
Ainsi le Roi d'Assyrie emmènera d'Egypte et de Chus prisonniers et captifs les jeunes et les vieux, les nus et les déchaussés, ayant les hanches découvertes, ce qui sera l'opprobre de l'Egypte.
5 Waɗanda suka dogara ga Kush suka yi taƙama da Masar za su ji tsoro su kuma sha kunya.
Ils seront effrayés, et ils seront honteux à cause de Chus, auquel ils regardaient; et à cause de l'Egypte, [qui était] leur gloire.
6 A wannan rana mutanen da suke zama a bakin teku za su ce, ‘Dubi abin da ya faru da waɗanda muka dogara a kai, waɗanda muka gudu muka je don neman taimako da ceto daga sarkin Assuriya! Yaya za mu tsira?’”
Et celui qui habite en cette Ile-ci dira en ce jour-là; voilà en quel état est celui auquel nous regardions, celui auprès de qui nous nous sommes réfugiés pour avoir du secours, afin d'être délivrés de la rencontre du Roi d'Assyrie; et comment pourrons-nous échapper?

< Ishaya 20 >