< Ishaya 19 >
1 Abin da Allah ya faɗa game da Masar, Duba, Ubangiji yana a kan girgije a sukwane yana kuwa zuwa Masar. Gumakan Masar sun firgita a gabansa, zukatan Masarawa sun karai.
2 “Zan tā da hargitsi tsakanin mutumin Masar da mutumin Masar, ɗan’uwa zai yi gāba da ɗan’uwa maƙwabci ya yi gāba da maƙwabci, birni ya yi gāba da birni, mulki ya yi gāba da mulki.
3 Masarawa za su karai, zan kuma sa shirye-shiryensu su zama banza; za su nemi shawarar gumaka da kuma ruhohin matattu, za su nemi shawarar mabiya da na masu duba.
4 Zan ba da Masarawa ga ikon azzalumi shugaba, mugun sarki kuma zai yi mulki a kansu,” in ji mai girma, Ubangiji Maɗaukaki.
5 Ruwayen kogi za su ƙafe, bakin kogi zai shanye yă kuma bushe.
6 Wuriyoyi za su yi wari; rafuffukan Masar za su yi ta raguwa har su ƙafe. Iwa da jema za su bushe,
7 haka ma tsire-tsire kusa da Nilu, a bakin kogi. Kowane abin da aka shuka a gefen Nilu zai bushe, iska ta kwashe su ƙaf.
8 Masu kamun kifi za su yi nishi su kuma yi makoki, dukan waɗanda suke jefan ƙugiyoyi a Nilu; waɗanda suke jefan abin kamun kifi a ruwa abin kamun kifin za su zama marasa amfani.
9 Waɗanda suke aiki da kaɗin auduga za su karai, masu yin lilin mai kyau za su fid da zuciya.
10 Masu aikin tufafi ransu zai ɓace, kuma dukan masu samun albashi za su damu.
11 Shugabannin Zowan ba kome ba ne, wawaye ke kawai; mashawarta masu hikima na Fir’auna suna ba da shawarwari marasa amfani. Yaya za ka ce wa Fir’auna, “Ni ɗaya ne cikin masu hikima, almajirin sarakuna na dā can”?
12 Ina masu hikima suke yanzu? Bari su nuna maka su kuma sanar da abin da Ubangiji Maɗaukaki ya shirya a kan Masar.
13 Shugabannin Zowan sun zama wawaye, an ruɗe shugabannin Memfis dutsen kan kusurwa na mutanenta su sa Masar ta kauce.
14 Ubangiji ya sa zuba musu ruhun jiri; suka sa Masar ta yi tangaɗi cikin kome da take yi, kamar yadda mutumin da ya bugu yake tangaɗi cikin amansa.
15 Babu abin da Masar za tă yi, kai ko wutsiya, reshen dabino ko iwa.
16 A wannan rana Masarawa za su zama kamar mata. Za su yi rawar jiki lokacin da Ubangiji Maɗaukaki ya ɗaga hannu a kansu.
17 Ƙasar Yahuda kuma za kawo fargaba ga Masarawa; kowanne da Yahuda ya ambace zai firgita, saboda abin da Ubangiji Maɗaukaki yake shiri a kansu.
18 A wannan rana birane biyar a Masar za su yi yaren Kan’ana su kuma miƙa kai cikin yarjejjeniya ga Ubangiji Maɗaukaki. Za a ce da ɗayansu Birnin Hallaka.
19 A wannan rana za a kasance da bagade ga Ubangiji a tsakiyar Masar, da kuma ginshiƙin dutse Ubangiji a iyakarta.
20 Zai zama alama da kuma shaida ga Ubangiji Maɗaukaki a ƙasar Masar. Sa’ad da suka yi kuka ga Ubangiji saboda masu zaluntarsu, zai aiko musu mai ceto da mai kāriya, zai kuma cece su.
21 Saboda haka Ubangiji zai sanar da kansa ga Masarawa, kuma a wannan rana za su yarda da Ubangiji. Za su yi masa sujada da hadayu da hadayun hatsi; za su yi alkawura ga Ubangiji su kuma kiyaye su.
22 Ubangiji zai bugi Masar da annoba; zai buge su ya kuma warkar da su. Za su juyo wurin Ubangiji, zai amsa roƙonsu ya kuma warkar da su.
23 A wannan rana za a kasance da babban hanya daga Masar zuwa Assuriya. Assuriyawa za su tafi Masar, Masarawa kuma za su tafi Assuriya. Masarawa da Assuriyawa za su yi sujada tare.
24 A wannan rana Isra’ila za tă zama na uku, tare da Masar da Assuriya, abin albarka ga duniya.
25 Ubangiji Maɗaukaki zai albarkace su, yana cewa, “Albarka ta tabbata ga Masar, mutanena, Assuriya aikin hannuna, da kuma Isra’ila gādona.”