< Ishaya 18 >

1 Kaiton ƙasar da ake jin ƙarar fikafikai a bakin kogunan Kush,
唉!古實河外翅膀刷刷響聲之地,
2 wadda ta aiko da jakadu ta teku cikin jiragen ruwan da aka yi da kyauro a bisa ruwa. Ku tafi, ku’yan saƙo masu sauri, zuwa ga dogayen mutane masu sulɓin jiki, zuwa ga mutanen da ake jin tsoro a ko’ina, al’umma mai ƙarfin iko tana jawabin da ba a saba ji ba, mai ƙasar da koguna suka raba.
差遣使者在水面上, 坐蒲草船過海。 先知說:你們快行的使者, 要到高大光滑的民那裏去。 自從開國以來,那民極其可畏, 是分地界踐踏人的; 他們的地有江河分開。
3 Ku dukan mutanen duniya, ku da kuke zama a duniya, sa’ad da aka ɗaga tutar a kan duwatsu, za ku gan shi, sa’ad da kuma aka busa ƙaho, za ku ji shi.
世上一切的居民和地上所住的人哪, 山上豎立大旗的時候你們要看; 吹角的時候你們要聽。
4 Ga abin da Ubangiji ya faɗa mini, “Zan yi shiru in kuma duba a hankali daga mazaunina, kamar ƙuna mai zafi a hasken rana, kamar girgijen raba a lokacin girbi.”
耶和華對我這樣說: 我要安靜,在我的居所觀看, 如同日光中的清熱, 又如露水的雲霧在收割的熱天。
5 Gama kafin girbi, sa’ad da furanni suka karkaɗe furanni kuma suka zama’ya’yan inabin da suka nuna, zai faffalle rassan kuringar inabi da wuƙa, ya yanke ya kuma kwashe rassan da suka bazu.
收割之先,花開已謝, 花也成了將熟的葡萄; 他必用鐮刀削去嫩枝, 又砍掉蔓延的枝條,
6 Duk za a bar su wa tsuntsayen dutse su ci da kuma namun jeji; tsuntsaye kuma za su ci rani a kansu, namun jeji kuma za su yi damina a kansu.
都要撇給山間的鷙鳥和地上的野獸。 夏天,鷙鳥要宿在其上; 冬天,野獸都臥在其中。
7 A wannan lokaci za a kawo kyautai wa Ubangiji Maɗaukaki daga dogayen mutane masu sulɓin jiki, daga mutanen da ake jin tsoro a ko’ina, al’umma mai ƙarfin iko na jawabin da ba a saba ji ba, mai ƙasar da koguna suka raba. Za a kawo kyautai zuwa Dutsen Sihiyona, wurin da Sunan Ubangiji Maɗaukaki yake.
到那時,這高大光滑的民, 就是從開國以來極其可畏、 分地界踐踏人的, 他們的地有江河分開; 他們必將禮物奉給萬軍之耶和華, 就是奉到錫安山- 耶和華安置他名的地方。

< Ishaya 18 >