< Ishaya 17 >
1 Abin da Allah ya faɗa game da Damaskus. “Duba, Damaskus ba za tă ƙara zama birni ba amma za tă zama tsibin juji.
The prophecy concerning Damascus. Behold, Damascus shall be no more a city; It shall become a heap of ruins.
2 Za a watse a bar biranen Arower a bar wa tumaki da shanu, waɗanda za su kwanta, ba tare da wani wanda zai tsorata su ba.
The cities of Aroer shall be forsaken; They shall be pastures for flocks, Which shall lie down, and none shall make them afraid.
3 Birni mai katanga za tă ɓace daga Efraim, ikon sarauta kuma daga Damaskus; raguwar Aram za tă zama kamar darajar Isra’ila,” in ji Ubangiji Maɗaukaki.
The fortress shall cease from Ephraim, And the kingdom from Damascus, and the rest of Syria; It shall be with them as with the glory of the children of Israel, Saith Jehovah of hosts.
4 “A wannan rana ɗaukakar Yaƙub za tă ƙare; kitsen jikinsa zai lalace.
In that day shall the glory of Jacob sink away, And the fatness of his flesh become leanness.
5 Zai zama kamar sa’ad da mai girbi ya tara hatsin da yake tsaye ya kuma girbe hatsin da hannunsa kamar sa’ad da mutum ya yi kala kawunan hatsi a Kwarin Refayim.
And it shall be as when the harvest-man gathereth the corn, And reapeth the ears with his arm; Yea, as when one gleaneth ears in the valley of Rephaim.
6 Duk da haka waɗansu kala za su ragu, sai ka ce sa’ad da an karkaɗe itace zaitun, aka bar’ya’yan zaitun biyu ko uku a can ƙwanƙolin rassan, ko kuma aka bar huɗu ko biyar a rassa na gefe na itace mai’ya’ya,” in ji Ubangiji, Allah na Isra’ila.
There shall be left in it only a gleaning, as in the olive-harvest, Two or three berries on the top of the highest bough, Four or five on the fruitful branches, Saith Jehovah, the God of Israel.
7 A wannan rana mutane za su nemi Mahaliccinsu su kuma juye idanunsu ga Mai Tsarkin nan na Isra’ila.
In that day shall a man have regard to his Maker, And his eyes shall look to the Holy One of Israel.
8 Ba za su dubi bagade ba, waɗanda suke aikin hannuwansu, ba za su kuma kula da ginshiƙan Ashera ba da kuma bagadan turaren da yatsotsinsu suka yi.
He shall not look to the altars, the work of his hands, Nor have respect to that which his fingers have made, The images of Astarte and the Sun-pillars.
9 A wannan rana biranensu masu ƙarfi, waɗanda suka bari saboda Isra’ilawa, za su zama kamar wuraren da aka ƙyale suka zama kufai a jeji. Za su kuma zama kango.
In that day shall his fortified cities be like ruins in the forests, or on the mountain tops, Which the enemy left, in flight from the children of Israel; And the land shall be a desolation.
10 Kun manta da Allah Mai Cetonku; ba ku tuna da Dutse, kagararku ba. Saboda haka, ko da yake kun fita ku shuka tsire-tsire mafi kyau kuka kuma shuka inabin da aka sayo daga waje,
For thou hast forgotten the God of thy salvation, And hast not been mindful of the rock of thy strength; Therefore though thou plant beautiful plants, And set shoots from a foreign soil,
11 ko da yake a ranar kun shuka su, kuka sa su yi girma, da safe kuma sa’ad da kuka shuka su, kuka sa suka yi toho suka yi fure, duk da haka girbin ba zai zama kome ba a ranar cuta da zafin da ba ta da magani.
When thou hast planted them, though thou hedge them in, And in the morning bring thy plants to the blossom, Yet shall the harvest flee away, In the day of pain and desperate sorrow.
12 Kash, ga hayaniyar al’ummai masu yawa suna hayaniya kamar rurin teku! Kash, ga fushin mutane suna ruri kamar rugugi kamar manyan ruwaye!
Alas! a tumult of many nations! They rage with the raging of the sea. Alas! a roaring of kingdoms! They roar with the roaring of mighty waters.
13 Ko da yake mutane suna ruri kamar sukuwar raƙuman ruwa, sa’ad da ya tsawata musu za su gudu can da nisa, aka kore su kamar yayinda iska ya hura a kan tuddai, kamar tattake kuma a cikin guguwa.
Like the roaring of mighty waters do the nations roar; He rebuketh them, and they flee away, Driven like the chaff of the mountains before the wind, Like stubble before the whirlwind.
14 Da yamma, sai razana ba tsammani! Kafin safiya, duk sun ɓace! Wannan ne rabon waɗanda suka washe mu, rabon waɗanda suka yi mana ƙwace.
At the time of evening, behold, terror! Before morning, behold, they are no more! This is the portion of them that spoil us, And the lot of them that plunder us.