< Ishaya 16 >
1 Ku aiko da raguna a matsayin haraji ga mai mulkin ƙasar, daga Sela a hamada, zuwa dutsen Diyar Sihiyona.
2 Kamar tsuntsaye masu firiya da aka kora daga sheƙa, haka matan Mowab suke a kogunan Arnon.
3 “Ku ba mu shawara, ku yanke shawara. Ku mai da inuwarku kamar dare, a tsakar rana. Ku ɓoye masu gudun hijira, kada ku bashe masu neman mafaka.
4 Ku bar Mowabawa masu gudun hijira su zauna tare da ku; ku zama mafakarsu daga mai neman hallaka su.” Mai danniya zai zo ga ƙarshe hallaka kuma za tă daina; masu lalatar da ƙasa za su kare
5 Da ƙauna za a kafa kursiyi; da aminci mutum zai zauna a kansa, wani daga gidan Dawuda, wani wanda ta shari’antawa yakan nuna gaskiya ya hanzarta yin adalci.
6 Mun ji fariyar Mowab, mun ji yawan fariyarta da girmankanta, fariyarta da reninta, amma taƙamarsu ta banza ce.
7 Saboda haka Mowabawa za su yi kuka mai zafi, za su yi kuka mai zafi tare saboda Mowab. Ku yi makoki ku kuma yi baƙin ciki saboda ƙosai da kuka riƙa ci a Kir Hareset.
8 Gonakin Heshbon sun bushe, inabin Sibma ma haka. Masu mulkin al’ummai sun tattake inabi mafi kyau, waɗanda suka taɓa yaɗuwa zuwa Yazer suka bazu ta wajen hamada. Tohonsu sun buɗu suka kai har teku.
9 Saboda haka na yi kuka, yadda Yazer take kuka, saboda inabin Sibma. Ya Heshbon, ya Eleyale, na cika ku da hawaye! Sowa ta murna a kanku saboda’ya’yan itatuwanku da suka nuna da kuma girbinku sun ɓace.
10 An ɗauke farin ciki da murna daga gonakin itatuwa masu’ya’ya; babu wanda yake rerawa ko yake sowa a cikin gonakin inabi; babu wanda yake matsin ruwan inabi a wuraren matsi, gama na kawo ƙarshen yin sowa.
11 Zuciyata tana makoki saboda Mowab kamar garaya, na yi baƙin ciki saboda Kir Hareset.
12 Sa’ad Mowab ta bayyana a masujadar bisa tudu, tana gajiyar da kanta ne kawai; sa’ad da ta tafi wurin tsafinta don tă yi addu’a, babu wani amfani.
13 Wannan ita ce maganar da Ubangiji ya riga ya yi game da Mowab.
14 Amma yanzu Ubangiji ya ce, “Cikin shekara uku, kamar yadda bawan da aka bautar da shi bisa ga yarjejjeniya zai lissafta, haka za a mai da daraja da kuma dukan yawan mutanen Mowab abin reni, daga ɗumbun mutanenta,’yan kaɗan ne kaɗai za su ragu, za su kuma zama marasa ƙarfi.”